Manzon Allah (S) ya ce; "ku sani Sadaka tana kawar wa mai yin ta azabar kabari, kuma shi Mumini yana cikin inuwar Sadakarsa a ranar alkiyama".

 FALALAR SADAKA



       _Ma'asumah Nigeria news update 

             //Mnnu/Ng0038 



                  25/03/2023


Sadaka tana cikin Muhimman alheri da Bawa ke amfanuwa da su a Duniya da Lahira, ita Sadaka amfaninta ribi biyu ne, duk wanda ya yi Sadaka da wani abu, to tun a Duniya Allah Zai yi masa sakamako na wannan Sadaka ta hanyar kare masa wata masifa ko bala'i da zai same shi, ko kuma yin Sadakar ya janyo masa wani amfani a rayuwarsa. Kuma ladar sa ta yin sadaka tana taskace a wurin Allah Ta'ala. 


Manzon Allah (S) ya ce; "ku sani Sadaka tana kawar wa mai yin ta azabar kabari, kuma shi Mumini yana cikin inuwar Sadakarsa a ranar alkiyama". 


Abu Abdullahi (As)  ya ce;  "Sadaka a bayyane, tana kare mutum daga nau'i Saba'in na bala'i. Sadaka a boye, tana bishe fushin Ubangiji ". 


A wani wuri kuma ya na cewa; "Sadaka da rana ta na narka laifuka kamar yadda gishiri ke narkewa a cikin ruwa, ita kuma Sadaka da dare tana bishe fishin Ubangiji"(Thawabul A'amal. 175). 


_Journalist Fatima✍️

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post