Lallai Wannan Al'amari (Addinin Allah) Babu Makawa Zai Tabbata.

 


Ma'asumah Nigeria News Update


— Shaikh Ya'aqoub Yahaya Katsina.


A cikin jawabin su Shaikh Ya'aqoub Yahaya Katsina ga ƴan uwa na Da'irar Kudan a ranar da su kai masa ziyara 15/02/2022* ya sake tabbatar da cewa lallai wannan al'amari addinin Allah zai tabbata da taimakon Allah(T) inda yake cewa; “Bin wannan tafarki ɗin da wannan hanyar da wannan karantarwar, to lazim ne na tabbatar addini, kamar yadda idan kace a kawo 'Tuwo' to kana nufin har da 'Miya' sabida Miya lazimin Tuwo ne, hakanan idan kace a kawo Tawada kayi rubutu to kana nufin harda Alƙalami, sabida alƙalami lazimin Tawada ne. To haka bin wannan tafarki ɗin shi lazim ne na tabbatar addini. Wannan ƴar ƙanƙanuwar jama'a ɗin da za'a samu waɗanda su cancanta Allah Yayi amfani dasu, to dasu Allah zai yi amfani ya tabbatar da addini.


“Wannan tabbatar addinin lazimi ne madamar ana kan wannan tafarki ɗin, ba makawa ne kawai, kamar ashana da takarda idan ka kyarsa ashana ka kanga akan takarda, idan kaga wannan takardar bata kama ba sai dai idan jiƙe take da ruwa, amma idan har a bushe take to zata kama. Manzon Allah (s) yana cewa “Allah zai taimaki al’ummar nan da raunanan mu ne (waɗanda basu iya kare kansu) da addu'o'insu, da sallolinsu, da tsarkin zuciyarsu. Waɗannan abubuwan guda uku dasu Allah zai taimaki al’umma, idan mutum ya tsare waɗannan abubuwan guda uku to Allah Yayi alƙawarin zai kawo taimakonsa. Kuma Allah tabbatar da hakan kafin yanzu.


Yaci gaba da cewa; “Waɗannan raunanan da ake ganin ba'a bakin komi suke ba, a kaita azabtarwa to dasu Allah Yayi amfani ya taimaki addini, addini ya kafu. Shehu Usmanu Ɗanfodiyo shima abinda ya faru kenan. Shima anan ganin wasu ƴan tsirarun mutane ne, fulani ne sun addabi mutane ayita ƙoƙarin ayi maganinsu, dasu ne Allah Yayi amfani wajan tabbatar da addini. Wannan ma abinda zai faru kenan Insha Allahu.


“Imam Khumaini(Q.s) ma abinda ya faru kenan. Ta ita yiwuwu mutum ya dubi faɗin ƙasa yayi tambaya yace yanzu duk mutanen nan zasu bada goyon baya al'amarin nan ya tabbata? To abin ba anan yake ba, ba'a yawa ne ba, “Kammin Fi'atin Ƙalilatin ne, galabat Fi'atan Kasiratan Bi'iznillah” tsiraru ake buƙata, kai hatta ma faɗin ƙasa ma ba shine ma'auni ba, abinda ke ma'auni shine Muminai waɗanda zasu bautawa Allah Ta'ala yadda yake son a bauta masa.


“Idan aka samu wani gari ko wani ƙauye wanda a ƙalla tamanin bisa ɗari (80%) sun karɓi da'awa (Harka) kuma zasu iya bata kariya, su ciyar da ita gaba, su sadaukar Allah Ta'ala yana iya amfani dasu, zai yiwu daga nan abin yayi naso yaje makwafta daga nan kuma ya faɗaɗa yake ko ina, a tarihin musulunci hakanan ne, wasu ƴan tsirarun mutane ne Allah Yayi musu jarabawa suci jarabawa daga nan Allah Ya kwashe su ya kaisu Madina daga Madina musulumci ya yaɗu yanzu ya mamaye duk duniya. Duk duniya yanzu musulunci yana nan ko ina.


“To idan aka samu Allah Yayi mana irin wannan tagomashi ɗin, a samu wani gari ko wani yanki ko wani wuri idan ya zamo an samu karɓuwar da'awar koda tamanin suka karɓa su shirya su sadaukar to Allah Ta'ala zai yi amfani dasu (idan sun cancanta) ya haskawa saura. Haka ya da Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo lokacin da aka kareshi daga Ɗagyal ya koma Gudu daga Gudu ne Allah Ya farar da abin ƙarshe ya dawo Sifawa ya tafi Sokoto daga kuma abubuwa suka yaɗu ko ina”.


A wani ɓangaren kuma yake cewa; “Shi kafuwar addini lazimin aikin ne, tabbatuwar addini lazimin aikin ne, madamar za ayi bara'a da wula'a su tabbata, kuma ayi aiki na Tablighi, ayi aiki na irshadi, matukar akwai malami kuma akwai almajirai ai magana ta ƙare. Ba magana ce ta ƙungiya ba, a'a murshidi da masu karɓar irshadi. Ka karanta tarihi ka gani, duk tarihin Annabawa murshidi ne da masu karɓar irshadi to dasu ne Allah yake tabbatar da addini, don haka lokaci ne, kuma shi kansa jiran wannan lokacin shima ibada ne. Sabida haka ana bukatar hakuri”.


“Sabida ba wani abune wanda ba zai yiwu ba, idan kace Mustahili ne (abinda ba zai yiwu ba) to sauri kake. kana gani za'ayi baka, ko kuma idan ka mutu sai a fasa. To Lallai abun ba haka bane, koda ka mutu (kana kan hanyar) zaka samu ladan assasawa sai wasu su ƙarasa. To zai yiwu kawai, madamar kan wannan tafarkin ake to zai yiwu, babu abinda zai hana shi yiwuwa. Allah Ta'ala Ya taimake mu”.


— Wani yanki na jawabin Shaikh Ya'aqoub Yahaya Katsina ga ƴan uwa na Da'irar Kudan da su kai masa ziyara a ranar 15/02/2022.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post