HUKUNCIN MATAR DA TAYI TSARKI (da sauran rana) KAFIN YINI YA QARE DA WANDA WATAN RAMADANA YA ZAGO MASA ALHALI YANA DA RAMUWA A KANSA !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


KANA DA ZABI WAJEN RAMA AZUMI A JERE KO KUMA A RARRABE 


Da yawa daga cikin mutane basu san hukuncin matar da tayi tsarki cikin watan azumi da sauran rana ba, saboda haka su kanyi abinda su kaga dama ne bisa rashin sani. Saboda haka akwai buqatar mutum yasan wannan hukunci domin ya sanar da iyalinsa kafin hakan ya faru a kansu. 


Sannan kuma ana samun mutane wadanda watan Ramadan ke zagowa ya same su da sauran ramakon azumin Ramadana da ya gabata. Wasu hakan na faruwa ne a kansu bisa ganganci, wasu kuma bisa lalura. Saboda haka idan hakan ta faru gare su ga hukuncin da ya hau kansu. 


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


علل الشرائع ابْنُ إِدْرِيسَ عَنْ أَبِيهِ عَنِ ابْنِ عِيسَى عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحَكَمِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَبِي بَصِيرٍ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ:- ضا، فقه الرضا عليه السلام‏ إِذَا طَهُرَتِ الْمَرْأَةُ مِنْ حَيْضِهَا وَ قَدْ بَقِيَ عَلَيْهَا بَقِيَّةُ يَوْمٍ صَامَتْ ذَلِكَ الْيَوْمَ تَأْدِيباً وَ عَلَيْهَا قَضَاءُ ذَلِكَ الْيَوْمِ وَ إِنْ حَاضَتْ وَ قَدْ بَقِيَ عَلَيْهَا بَقِيَّةُ يَوْمٍ أَفْطَرَتْ وَ عَلَيْهَا الْقَضَاءُ وَ إِذَا مَرِضَ الرَّجُلُ وَ فَاتَهُ صَوْمُ شَهْرِ رَمَضَانَ كُلِّهِ وَ لَمْ يَصُمْهُ إِلَى أَنْ يَدْخُلَ عَلَيْهِ شَهْرُ رَمَضَانَ مِنْ قَابِلٍ فَعَلَيْهِ أَنْ يَصُومَ هَذَا الَّذِي قَدْ دَخَلَ عَلَيْهِ وَيَتَصَدَّقَ عَنِ الْأَوَّلِ لِكُلِّ يَوْمٍ بِمُدِّ طَعَامٍ وَ لَيْسَ عَلَيْهِ الْقَضَاءُ إِلَّا أَنْ يَكُونَ قَدْ صَحَّ فِيمَا بَيْنَ شَهْرَيْنِ رَمَضَانَيْنِ فَإِذَا كَانَ كَذَلِكَ وَ لَمْ يَصُمْ فَعَلَيْهِ أَنْ يَتَصَدَّقَ عَنِ الْأَوَّلِ لِكُلِّ يَوْمٍ مُدّاً مِنْ طَعَامٍ وَ يَصُومَ الثَّانِيَ فَإِذَا صَامَ الثَّانِيَ قَضَى الْأَوَّلَ بَعْدَهُ فَإِنْ فَاتَهُ شَهْرَانِ رَمَضَانَانِ حَتَّى دَخَلَ الشَّهْرُ الثَّالِثُ وَ هُوَ مَرِيضٌ فَعَلَيْهِ أَنْ يَصُومَ الَّذِي دَخَلَهُ وَ يَتَصَدَّقَ عَنِ الْأَوَّلِ لِكُلِّ يَوْمٍ بِمُدٍّ مِنْ طَعَامٍ وَ يَقْضِيَ الثَّانِيَ فَإِنْ أَرَدْتَ سَفَراً وَ أَرَدْتَ أَنْ تُقَدِّمَ مِنْ صَوْمِ السَّنَةِ شَيْئاً فَصُمْ ثَلَاثَةَ أَيَّامٍ لِلشَّهْرِ الَّذِي تُرِيدُ الْخُرُوجَ فِيهِ وَ إِنْ أَرَدْتَ قَضَاءَ شَهْرِ رَمَضَانَ فَأَنْتَ بِالْخِيَارِ إِنْ شِئْتَ قَضَيْتَهَا مُتَتَابِعاً وَ إِنْ شِئْتَ مُتَفَرِّقاً وَ قَدْ رُوِيَ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع أَنَّهُ قَالَ يَصُومُ ثَلَاثَةَ أَيَّامٍ ثُمَّ يُفْطِرُ وَ إِذَا مَاتَ الرَّجُلُ وَ عَلَيْهِ مِنْ صَوْمِ شَهْرِ رَمَضَانَ فَعَلَى وَلِيِّهِ أَنْ يَقْضِيَ عَنْهُ‏."


Ya zo cikin Ilalus-Shara'i'i  na Ibn Idrisa, daga babansa daga Ibn Isah, daga Aliyu Bn Hakam, daga Muhammad Bn Yahya, daga baban Baseer, daga Abu Abdullah (A. S) yace : 


Kuma ya zo cikin Fiqhu na Imam Ridha (A. S)  cewa :


" IDAN MACE TAYI TSARKI DAGA HAIDHARTA ALHALI AKWAI ABINDA YA RAGE GARE TA DAGA YININ, TO, ZA TA AZUMCI WANNAN RANA SABODA  LADABI, KUMA AKWAI RAMAKON WANNAN RANA A KANTA. 


IDAN KUMA HAIDHA TAZO MATA ALHALI AKWAI SAURAN YINI A KANTA, ZA TA SHA, KUMA AKWAI RAMAKO A KANTA. 


IDAN KUMA MUTUM YAYI RASHIN LAFIYA HAR AZUMIN WATAN RAMADANA YA KUBUCE MASA GABA-'DAYA, KUMA BAI SAMU YA YI SHI BA HAR AZUMIN WATA NA GABA YAZO MASA, TO, ZAI AZUMCI WANNAN (sabon watan) DA YAZO, KUMA YAYI SADAQA AKAN NA FARKO (wanda bai samu ya azumce shi ba), MUDUN ABINCI A KOWACCE RANA, KUMA BABU RAMAKO A KANSA,   SAI DAI IN DAMA YA KASANCE YA WARKE A TSAKANIN WADANNAN WATANNI BIYU NA RAMADANA. TO, IDAN HAKAN YA KASANCE KAMAR HAKA, KUMA BAI AZUMCE SHI BA, TO, ABINDA KE KANSA SHINE ZAI YI SADAQA GA NA FARKON, KOWACCE RANA YA BADA MUDU NA ABINCI, KUMA YA AZUMCI NA BIYUN. IDAN YA GAMA AZUMTAR NA BIYUN KUMA SAI YA RAMA NA FARKON DAGA BAYA. 


IDAN KUMA WATANNI BIYU NE NA RAMADANA SUKA KUBUCE MASA HAR WATA NA UKU YA SHIGO ALHALI YANA HALIN RASHIN LAFIYA, TO, ABINDA KE KANSA SHINE YA AZUMCI WANDA YA SHIGO, KUMA YAYI SADAQA AKAN NA FARKO, KOWACCE RANA YA BAYAR DA MUDU NA ABINCI, SAI KUMA YA BIYA NA BIYUN. 


IDAN KUMA YAYI NUFIN YIN TAFIYA SANNAN KUMA YAYI NUFIN GABATAR DA WANI ABU NA AZUMIN SHEKARA, TO, YA AZUMCI KWANAKI UKU NA WATAN DA YAYI NUFIN FITA A CIKINSA. 


IDAN KUMA  KAYI NUFIN RAMA (azumin) WATAN RAMADANA, TO, KANA DA ZABI (choice), IDAN KASO ZA KA IYA RAMA SHI A JERE (ba tare da ka huta ba), IDAN KUMA KASO ZA KA IYA RAMA SHI A RARRABE. "


Haqiqa an riwaito daga Abu Abdullah (A. S) cewa ya ce :


" ZAI AZUMCI KWANAKI UKU (a jere) SANNAN YA SHA. KUMA IDAN MUTUM YA RASU ALHALI AKWAI RAMAKON AZUMIN RAMADANA A KANSA, TO, WASIYYINSA NE ZAI RAMA MASA. "


علل الشرائع ج 2 ص 70.



بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏93، ص: 334


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


25th March, 2023/ 3rd Ramadan, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post