Gargadi na Musamman Da Kasar Saudiyya ga Masu Daukar Hoto a lokacin Gudanar da Ibadah.

 


Hukumar kasar saudiya mai kula da aikin Haji da Umrah  ta yi kira ga masu ziyarar ibada zuwa wurare masu alfarma da su martaba darajar wuraren.

Sannan kuma su bi dokoki wajen ɗaurar hotunan.

Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su ɓige da ɗaukar hotuna, a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su ƙasa mai tsarkin.


Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don ɗaukar hoto a wuraren da jama'a da dama suka taru, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama'a a wuraren.

Haka kuma Kasar Saudiyyar  ta gargaɗi masu ɗaukar hotunan da su guji haɗawa da wasu mutanen a cikin hoton nasu Wadanda Basusan Sunayi ba, su tabbatar Sun nemi izinin Su kafin Su dauka, ko kuma su Daukin Hoton su kadai batate da Jama'a ba.


A cikin Wannan lokacin ne dai mutane sun ɓullo da salon ɗaukar hotuna a lokacin ziyarar ibada zuwa ƙasa mai tsarkin tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta kamar facebook, whatsapp da Tweeter dss.

Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa zai iya zama 'Riya', abin da kuma a cewar malaman zai iya ɓata wa mutanen ibadar tasu, hakan yasa kasar tayi gargadi ga masu daukar hotunan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post