GA KYAUTAR ADDUA GA IYAYE MASU YARA.



Idan ki ka tashi da asuba kafin ki yi wa kowa magana sai ki dafa kan yaro koda yana barci sai ki karanta.

(Ihdina ssiradal mustakim ) 41 ki kwana 7 ban da fashi to koda yaro ya fara rashin ji Wallahi zai daina, wannan mujarrabi ne kada a yi sakaci da ku yi wa yaran ku za ku ga natsuwa ta mamaki a tare da su. 


Idan yaranmu suna cikin barci a tofa musu inna anzannahu kafa daya a gabansu da kirjinsu kafa dai daya bazasu tafa kusantar wani da miji ba inba mijinsu ba haka maza ma.


Uwa takaranta Suratul Fatiha daga farko zuwa karshe kafa arba'in da daya 41 tsakanin magariba da Isha. Allah zai shiryarmata yaranta  su zama masu hankali masu ladabi da biyayya da tausayin iyaye.


 Idan yaranmu zasu kwanta suyi barci sai a tofa musu Bismillah a midigarsu kafa bakwai Yana Buda kwakwalwa Don Allah kiturawa kowa kada ki manta da mutum ko da daya, Rabbi gifirli minkulli zambin wa'atubu ilallahi.


Sadakar ayi salati ga Manzon tsira hadia ga lafiyar #Zakzaky da Umma bayin Allah.


Daga Shafin Shaikh Salihu Garba.


Alz. Ya Kwafo don Amfanarbmu baki daya.


               Mnnu//Ng0027


Ma'asumah Nigerian News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post