FALALAR ISTIGFARI

 



_Ma'asumah Nigeria News Update 

//Mnnu/Ng0038


Istigfari da nufin tuba ko neman afuwar Allah bisa Zunubai da kurakurai wadanda mutum ya aikata cikin sani da wadanda bai sani ba, ko kuma don kaskantar da kai ga Allah da nuna gazawa, abu ne mai tasiri da amfanin gaske ga Musulmi. 


Manzon Allah (S)  ya ce; "Istigfari a gareku garkuwa ne mai kare shiga azaba".  A wani wurin yana cewa " Farin ciki ya tabbata ga wanda ya Samu Istigfari a karkashin  duk wani Zunubi (da ya aikata) a littafinsa ranar alkiyama". 


Imam Ali (As) ya ce; "Tuba (ga Allah)  yana tsarkake zuciya, kuma yana wanke mutum daga Zunubi" (Gurarul Hikam). 


A wasu ruwayoyin an nuna cewa Manzon Allah (S) a kullum yana Istigfari sau 100.


Malaman tarbiyya sun ce mafi karancin abin da mutum zai yi shine

 Istigfari 100 a kullum. 


_Journalist Fatima✍️

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post