AYI HATTARA YARAN ZAMANI:- Jinsin Mutane Uku da Ba za Su Shiga Aljannah ba!!!

 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


AYI HATTARA YARAN ZAMANI 


Na ambaci yaran zamani ne saboda suna daga cikin jinsin wadannan mutane uku wadanda ba za su shiga Aljannah ba sakamakon rashin biyayyarsu ga mahaifansu.


Idan ka tara yaran wannan zamani ka kasa su gida goma sai ka tarar  daqyar ka sami kaso biyu  masu biyayya ga mahaifansu cikin kowanne irin yanayi alhali ba wai mahaifan nasu nayi musu umarni wajen sabawa Ubangiji bane.


Ba wai cikin wadanda muke kira Amawa kadai wannan matsala take ba,  a'a, har cikin masu da'awar sune ke kan karantarwa Ahlul-Bait  (A. S) , wato masu kiran kansu da 'yan'uwa ko 'yan Shi'ah. 


Ya zo cikin riwaya daga Imam Ali (A.S) yana cewa :


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ


ู‚ุงู„ ุงู„ุฅู…ุงู… ุนู„ูŠ ุจู† ุฃุจูŠ ุทุงู„ุจ(ุน):


 " ุซَู„ุงุซَุฉٌ ู„ุง ูŠَุฏْุฎُู„ُูˆู†َ ุงู„ْุฌَู†َّุฉَ: ุณَูّุงูƒُ ุฏَู…ٍ ุญَุฑุงู…ٍ، ูˆَ ุนุงู‚ُّ ูˆุงู„ِุฏَูŠْู‡ِ، ูˆู…َุดَّุงุกٌ ุจِู†َู…ูŠู…َุฉٍ."


" (jinsin mutane) UKU BA ZA SU SHIGA ALJANNAH BA : MAI ZUBAR DA JINANE BISA HARAM, DA  MAI SABAWA MAHAIFA, DA KUMA MAI YAWO DA ANNAMIMANCI (mai haddasa fitina tsakanin wani da wani). "


ุงู„ู…ุตุฏุฑ : ุนูŠูˆู† ุงู„ุญูƒู… ูˆุงู„ู…ูˆุงุนุธ


Wadannan sune jinsin mutane uku da aka kawo cikin wannan hadisi wadanda aka ce ba za su shiga Aljannah ba. 


Sai kowa yayi nazari akan kowanne daga cikinsu, amma ni dai na danyi bayani kadan kan yara masu sabawa mahaifansu, domin ita ce tafi yawa na daga abinda ake aikatawa wadanda suke yiwa mutum shamaki da Aljannah. 


YAA ALLAH KA SHIRYAR MANA DA 'YA'YAYENMU WADANDA KE NEMAN SHIRIYA 


๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍๐ŸผAdo Isah Guda.


          (08137925034)


5th March, 2023/  13th Sha'aban, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post