ALLAH BA YA 'DAUKAKA BAWANSA JAHILI !!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


HAQURI BA YA JAWOWA MUTUM KOMAI SAI 'DAUKAKA 


Shi jahilci ciwo ne mai matuqar illa ga mutum da kuma al'umma baki daya. Shi a qashin kansa jahili kan cutu sakamakon jahilcin da yake da shi, sannan kuma ayyukansa kan cutar da al'umma sakamakon koyi da wasu za suyi da ayyukansa a rashin sani. 


Ya zo cikin hadisi daga Manzon Allah (tsira da aminci su tabbata a gare shi) yake cewa; 


" SHUGABA JA'IRI, DA MALAMI KANGARARRE, DA KUMA MAI QOQARI (a addini amma ) JAHILI  ."


Saboda haka kuwa jahili ba zai taba samun daukaka wajen mutane ba ballantana wajen Allah (S. W. A). 


Shi kuwa haquri daukaka ma'abocinsa yake yi, domin ta hanyarsa ne ake samun nasarar komai na rayuwa. Saboda haka babu wani mutum da zai kasance mai haquri face Allah ya daukaka shi. 


Ya zo cikin Usulul-Khafiy daga iddati daga Barqee, daga Aliyu Bn Hafsi al-Qurashiy al-Kuufeey zuwa kan 

Abu Abdullah (aminci ya tabbata a gare shi) yace; 


 الكافي عَنِ الْعِدَّةِ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ حَفْصٍ الْقُرَشِيِّ الْكُوفِيِّ رَفَعَهُ إِلَى أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ:


Manzon Allah (tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi da iyalan gidansa)  yace, 


" ALLAH BAI TABA 'DAUKAKA (mutum) DA JAHILCI BA, KUMA BAI TABA QASQANTAR (da mutum) TA HANYAR HAQURI BA  ."


 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏: " مَا أَعَزَّ اللَّهُ بِجَهْلٍ قَطُّ وَ لَا أَذَلَّ بِحِلْمٍ قَطُّ ."


Saboda haka mu qara haquri cikin komai namu,  kada zaqi ko suka ko zargi ko aibantawa ko kuma cutarwa ya zame mana jarrabawa mafi girma wacce za ta hana mu juriya har ya zama munyi hasarar duniya da lahirarmu.


Haquri siffa ce ta Annabawa (A. S), duk wanda yayi haquri zai sami daukaka daga Allah kamar yadda ya daukaka Annabawansa (A. S). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


      (08137925034)


16th January, 2021/  3rd Jimada-Saaniy, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post