AL'UMMA TANA ZAUNE TANA GANI. __Sheikh Ibrahim Zakzaky (H)




 "Yanayin da muka samu kanmu a ciki Muna musulmi amma wani Abu ya shiga tsakaninmu da aikata sakon, sau dayawa in mutum ya dauki alkur'ani zaiji Allaha ta,ala yace, ya ku wadanda kukayi Imani kuyi kaza! idan ya duba wannan al'umma tamu sai yaga ba abin da take yi ba kenan, sai ya duba a cikin alkur'ani yaga yadda allah ta'ala yace Kubar kaza, in ya duba sai yaga wannan abu a cikin Al'umma, bama kawai ana aikatawa ba harma an ce qa'ida ne ma ayi. Harma in mutum zai aikata wannan ana iya bashi lacici ya yi.


Kuma Al'umma tana zaune tana gani,  wannan ba sai na baku misalai ba ku ma kuna iya gani, ga sunan a kewaye suke da mu. To me ya janyo haka? 

Muna nufin kenan munsamu kanmu a wannan zamanin wanda ba zai yiwu ayi aiki da fatawan sakon ba? Wato lokacin aikata sakon ya wuce kenan? Mu wanda bamu aikatawa din lokacin aikatashi ya wuce ne? a'a lokacin aikatashi bai wuce ba, ana ma bukatanmu da mu aikata.


__Sheikh Zakzaky (H) cikin Ja.wabin, _ ABIN DA YA HAU KAN MUSULMI.   (JEGA)


_Sheikh Zakzaky's Gallery


30-1-2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post