Na ajiye aiki da BBC Hausa don bude sabon babi a rayuwata- Abdulbaki Jari




Matashin 'Danjarida da ke aiki da sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Jari ya bayyana babban dalilin da ya sa ya ajiye aikinsa da kamfanin na yada labarai na kasar Birtaniya bayan ya shafe fiye da shekaru hudu yana aiki da su.


A safiyar Larabar nan ne 'Danjaridar ya wallafa wani sako zuwa ga masoyansa a shafinsa na Facebook inda ya ce ya yi hakan ne domin ya samu damar bude wani sabon babi a tarihin rayuwarsa.


Sai dai DCL Hausa ta ga jama'a da dama na ta aika masa sakonnin fatan alkhayri tare da fatan nasara a inda zai tsinci kansa.


A makon jiya ne dai wasu kafofin yada labaran Nijeriya suka fitar da wani rahoton da ke cewa wasu ma’aikata 9 na sashen Hausa BBC din sun ajiye aikinsu sakamakon samun gurbin aiki da suka yi a wani gidan rediyo na kasar Turkiyya, duk da dai har ya zuwa yanzu BBC Hausa ba ta yi magana ba kan ajiye aikin ma'aikatan nata ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post