A Kaf Nijeriya Muna Da Adadin Bankuna 5,437, A Jihohin Mu 18 Na Arewa Muna Da 1,188 Ne Kacal, Jihar Legas Ita Kadai Tana Da Bankuna 1,624 Sama Da Yawan Na Arewa Baki Daya !!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


....Hakan yasa 'yan Arewa suke ta shan wahala wurin sabbin kudi.


Daga Comr Abba Sani Pantami 


A kaf Najeriya muna da adadin Bankuna 5,437, a jihohin mu 18 na Arewa muna da 1,188 ne kacal, jihar Legas ita kadai tana da Bankuna 1,624.


Abuja tana da Bankuna 390, sauran jihohin yankunan kudancin Najeriya suna da Bankuna 2,235.


Idan kuka duba yawan Bankunan da jihar Legas kadai take dasu yafi na dukkannin jihohin Arewa baki daya, wannan dalilin yasa zaku ga al-ummar Arewa ce kadai take shan wahala musamman a yanzu da ake ta fama da matsalar chanjin sabbin kudi.


Idan muka duba zamu ga mu yankin Arewa mun ninka kudancin Najeriya yawan adadin mutane da jihohi da yawan kananan hukumomi amma sun fimu yawan Bankuna da sauran abubuwan more rayuwa da ka iya kawo saukin rayuwa ga al-umma.


Wannan dalilin yasa yanzu haka a kudancin Najeriya ko layi babu a bankunan su duk wahalar da muke sha akan chanjin sabbin kudi su duk basu san da ita ba duk akan 'yan Arewa ya kare.


Allah ya ceci yankin mu na Arewa, Allah ka bamu shugabanni masu kinshin mu da zasu yi silar kawo mana karshen matsalolin da muke ta fama da su.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post