Labari da dumi dumin sa CBN ya kawo sabon shirin musanyar tsohon kuɗi don sauƙaƙawa mutanen karkara
dban bankin Nigeria CBN ya sanar da kawo wani sabon tsarin musayar Kuɗin Naira da aka canja (N1000, N500, N200) zuwa sabo, domin sauƙaƙawa mutanen karkara.


Cikin wata sanarwa da daraktan shafin bibiyar banki, Haruna B. Mustapha, ya sanyawa hannu, yace ba za'a bawa mutum ɗaya sabon kuɗi sama da N10,000 ba a hannu sai dai a karbi tsohon a tura masa zuwa asusun banki idan sun wuce haka. 


Sannan kuma idan mutum bashi da asusu to za karbi bayanansa a take a buɗe masa sannan a saka masa kuɗinsa a ciki, kana kuma akwai takardun N100, N50, N20, N10, N5 wadda idan mutum bai samu waɗanda aka canza ba, za a sauya masa da waɗannan.


Har ila yau, yace wakilan da zasu samar suna da damar karɓar tsohon kuɗi su baka sabo kuma kyauta ne, saidai abinda ake cira idan mutum zai cire kuɗinsa koda da kansa ne. 


Bugu da ƙari, daga baya wakilan da suka saka akan aikin zasu dinga mayarwa da banki tsohon kuɗin. Kamar yadda suka ce, wannan shiri ne da za'a aiwatar a dukkan kananan hukumomi na jihohin Najeriya.


A ranar 31 ga watan da muke ciki na Janairu ne wa'adin da CBN ya bayar na daina karɓar kudaden da aka canjawa fasali zai cika, sai dai har kawo yanzu al'ummar Nigeria na kukan cewa akwai ƙarancin sabbin kuɗaɗen a injin cirar kudi na ATM, harma da cikin bankuna, wasu ma na cewa basu taba ganin sabon Kuɗin a zahiri ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post