Hotuna inda aka binne Shahidan Yakin Badar (Yanzu Ba'a zuwa Wajen An Dauki wani Hoton Daga Sama....


 

[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Wani hoton An Dauko Daga sama, filin Badar yana nuni da filin da aka binne Sahabbai goma sha hudu da suka yi shahada a Ya*kin Badar. Yanzu Ba a  Bari a isa Wurin.


Musulmi sun yi nasara da taimakon Allah (ﷻ). Annabi (SAW) da sahabbansa sun yi jarumtaka har sai da Kuraishawa suka yi babban rashi, suka gudu daga fagen fama. Sun yi hasarar mutane 70 daga cikin fitattun mazajensu, sannan Guda 70 musulmi suka kama su a matsayin fursuna.


Musulmi goma sha hudu ne suka yi shahada a wannan yakin. Wanda ya fara shahada shi ne Umayr bin al-Humam (رضي الله عنه)


Daya daga cikin mafi karancin shekaru a yakin Badar shi ne wani yaro da ake kira Umayr bin Abi Waqqas (رضي الله عنه). Ya fito yaqi  yana dan shekara goma sha shida ya ji tsoron Manzon Allah ba zai bar shi ya shiga Yakin ba.


Sai ya yi kokarin kada a gan shi, sai babban yayansa, Sa’ad bin Abi Waqqas (رضي الله عنه) ya tambaye shi ina zashi? Sai Yace “Ina jin tsoron Manzon Allah ya mayar da ni lokacin da nake son tafiya. Watakila Allah ya ba ni sha*hada.” Ya amsa, Lallai haka lamarin ya kasance. Annabi (SAW) ya so ya mayar da shi gida saboda yana karami amma Umayr ya fara kuka. Hawayensa sun sanyaya zuciyar Manzon Allah wanda ya ba shi damar tafiya Yakin Tare da mummunai.


An ka*she Umayr, shi ne mafi kankantar sha*hidi a cikin Yakin Badar.


Bayan yakin Badar, musulmi sun zama al'umma daya mai karfi. Yakin Badar babban misali ne daga tarihinmu wanda yake karantar da nasara baya dogaro da adadi ko tattara makamai da garkuwa, Nasara daga Allah (ﷻ) take. Allah (ﷻ) yana cewa a cikin Suratul Baqara:


Sau nawa wasu tsiraru suke cin galaba a kansu da izinin Allah. Kuma Allah Yanã tãre da mãsu haƙuri.


Alqur'ani (2:249)


Annabi (SAW) ya sanar da sahabbansa cewa Allah (ﷻ) ya riga ya Dubi wadanda suka halarci ya*kin Badar ya ce: “Ku yi yadda kuke so, na gafarta muku.” An karbo daga Rifa’ah Az-Zuraqi daya daga cikin wadanda suka halarci yakin Badar cewa Jibrilu (عليه السلام) ya zo wajen Annabi (SAW) ya ce: “Yaya kuke kallon jaruman Badar. a tsakaninku?” Manzon Allah (SAW) ya ce, “A matsayinsu na mafifitan musulmi,” ko kuma ya fadi wani abu makamancin haka. A kan haka, Jibrilu (عليه السلام) ya ce: “Haka mala’ikun da suka halarci yaqin Badar”.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Gaskiya ni ban fahimci natijar da akeso afitar ba a cikin wanan rubutun

    ReplyDelete
Previous Post Next Post