Ba Za A Yi Takarar Ba, An Kasa Cika Mana Alƙawari, Kuma Na Yi Watsi Da Jam'iyyar ADP Nan Take, Cewar Alan Waƙa


 


Mawaki Aminu Alan Waƙa ya fice daga jam'iyyar ADP ta Sha'aban Ibrahim Sharaɗa, sannan ya yi wurgi da takarar majalisar tarayya da yake yi a ƙaramar hukumar Nassarawa.


A cikin saƙon bidiyon da ya fitar, Ala ya nuna yayi danasanin fitowa ya bayyana kansa a matsayin ɗan takarar, domin ya ce babu wata takardar shaidar cewa yana takara da ya gani.


Ya kuma zargi ƙungiyar 13×13 da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta, wanda babban jigon ADP ne a Kano da yi musu an giza mai kantu ruwa kan shiga jami'yyar bisa sharaɗi.


Sai dai ya ce, daga baya ƙungiyar ta ƙasa yin kataɓis domin sanar da su matsayarsu, kurum an barsu da magana da wadanda ba su da hurumi.


Ala ya ce, tuni ya aike wa jami'yyar takardar sallama.


Mene ne ra'ayinku a kai

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post