Aiki Da Tunani Shine Mutum...!!!


@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 


- MENENE TUNANI..??? 

         Bismillahir-rahmanir-rahiim..✍️ 

Tunani kamar yanda masana suka bayyana Shine halarto da wani sabon, Al'amari wanda da bashi izuwa masaqar tunani ta zuciya, don baiwa zuciya aikin tasarrufi acikin jujjuyawar wannan al'amarin harya zuwa daidaiton zuciya akan amincin aiki.

Zuciya na iya kunsar kowadanne irin lamura don ba masaqar ta damar tantancesu akan yiwuwar aiwatar da su ko akasin haka, San nan kuma masana sun tabbatar da cewa TUNANI AIKI NE, dalilan su kuwa akan hakan shine, duk zuciyar da ta dauki wani al'amari tanason yin tunani akansa dole yazamana daga karshe ta haifar dashi izuwa aiki na zahiri.

Shin ko kasan yadda kake tunani haka ma al'amuranka suke wanzuwa? Idan a tunaninka ka dauka cewa kasala na damunka to sai zuciyarka ta sadar da wannan saqo cikin lungu da saqo na gabban jikinka, don haka sai ka samu kanka cikin kasala, Idan kuma ka cika zuciyarka da sha'awar aikata abubuwa da yawa sai ka zama mai kuzari wajen aikata wadannan abubuwa, MISALI;- Idan kasa aranka zaka zama mai yawan bautawa Allah, to fa duk lokacin aikata wani aiki Idan yayi sai dukkanin gabban jikinka su sadu da wannan saqo, nan take sai kaji kana son aikata wannan aiki, kuma wani abin mamaki aduk lokacin daka mika wuya ga Allah zaka sami Qarfin gwiwar aikata abubuwa fiye da yadda kake tsammani. 

Jiki kan samun karsashi Idan har mutum ya zama mai matuqar kulawa da kansa wajen bashi dukkan haqqoqinsa wadanda suka hada da con abinci mai gina jiki, da motsa jiki, da gujewa aikin da yafi qarfinsa(Don hakan kan illata jiki), da samun hutu ta hanyar barci da kuma kebe kai don samun hutu/Nutsuwa.

Idan ka zama mai kiyaye wadannan abubuwa, na tabbatar jikinka zai kasance cikin koshin lpy da nutsuwa, wanda hakan zai samar maka da jin karsashi da qarfi a jikinka, Saboda haka ka maisa hankali don ganin ka kawar da abubuwan da suke damunka.  

Domin samun karsashi da qarfin jikinka, saboda haka ka maida hankali don ganin ka kawar da abubuwan da suke damunka, Idan kuma ka bari damuwa da tsoro da fargaba suka cika zuciyarka,to lallai zaka kasance ka rasa karsashin da kake dashi, har wadansu cututtuka su addabe ka, Shi wannan jiki da kake gani yana neman taimakon ka, na gina kyawawan tunani don ka zama mai karsashi da samun qarfin jikinka, wanda hakan zai dore har lokacin da shekarunka zasuja. 
 
A bin fahimta a wannan rayuwar shine mutum yana iya canzawa Sakamakon canzawar tunaninsa, yadda mutum yake aiwatar da tunaninsa haka zai zama, yana da kyau a ce ya cika zuciyarsa da tunani masu amfani, ya kuma Qirqiri tunani wadanda za su kwantar da hankali da sa Shi qaunar jama'a, da tafiyar da abubuwa masu muhimmanci da son addini, Idan ka bi wannan hanya,to zaka zama kullum ka bambanta da sauran jama'a,kuma zaka canza nagartarka ta fito fili.

Yana da kyau mutum ya sake gina kansa,da tubalin da yake Mai Qarko ne, idan ya zama wanda ya fara gina kansa dashi na toka ne,kada ya zama mai tinani akan cewa bazai iya canza kansaba, Dukkammu mun yarda da cewa, Abokai nagari kan iya canza halayyar mutum, haka Kuma idan mutun yaso yakan iya gurbata kansa ta hanyar abokantaka da mutanen banza, mun yarda tunanin mutum na da tasiri ga yadda yake gudanar da al'amuransa na yau da kullum, Idan ka zama tunaninka ya gurbata, ban da tunanin muggan abubuwa, babu abinda zaka zama sai Mai aikata muggan ayyuka,  Amma idan tunaninka ya zama mai amfani, Akan abubuwa masu amfani da tasiri, Sai ka zama mai aikata aiki nagari.

Tunanin dan'Adam Shi ne Qashin bayan canzawar rayuwarsa, Za mu tabbatar da hakan ne ta hanyar abinda muke yi a rana, watau dai muna yinsa ne daidai da tunaninmu a wannan rana.

Ataqaice dai mutum yana zama'abinda yake so ya zama ne ta hanyar abinda yake tunani azuciyarsa, Idan kayi tunanin alheri sai Allah ya taimake ka tunaninka ya zama gaskiya. Yana da kyau ka canza halinda kake ciki Idan ya kasance mummuna ne, Haka kuma ba zai yiwu ba sai ka zama ka canza tunaninka ya zuwa ga abubuwa masu kyau.
Yã Dan'uwa, yana da kyau ka canza halinda kake ciki Idan ya kasance mummuna ne, Haka kuma ba zai yiwu ba sai ka zama ka canza tunaninka ya zuwa ga abubuwa masu kyau. 

- TA YAYA ZAKA YI HAKAN??? 

Yana da kyau Mutum ya canza tunaninsa dg munana zuwa'alheri, Idan mutum ya kasance mai mummunan zato tare da yin mummunan tunani, Zaka iske shi ba kasafai yakan sami alheri ba, Amma mu sani cewa yawancin mafarkenmu sukan tafi ne daidai da tunanin da muka kwanta da shi a wannan rana, Idan har mutum ya kwanta da tsoro a ransa, abu ne mai wuya a wannan dare bai yi mummunan mafarkiba, 

Yana da muhimmanci mutum ya
nesanci fidda kauna da kuma mummunan tunaninda zai wargaza masa rayuwa, da yawa irin wannan'tunani na debe kauna wanda shi yake haifar da rashin katabus yana illata mutanenmu harma zaka ga mutum mai jin karfi ya zamo raggo, da yawa sai kaga mutum yana zaune yace ya rasa aiki, Amma sai wani yazo daga wani gun ya nemi arziki kuma ya samu.

Shi tunanin mutum shine shi, In kana jin zaka iya komai kuma zaka ci nasara sai Allah Ya taimakeka. Dama dai mu musulmai musulunci ya hana mu debe kauna da fidda rai daga taimakon Allah, A Ko da yaushe musulmi mai jajircewa ne da kokari tare da neman taimakon Allah, don haka kada ka yarda da tunani irin na debe kauna, kullum ka zama mai yiwa Allah kyakkyawan zato da dagewa wajen fita daga'kowane mawuyacin hali ka samu kanka da kuma yi kokarin kara ci gaba da samun ni’imomin Ubangiji.

Amma tunani abubuwa masu kyawu sukan sa rayuwa ta zama cikin jin dadi, Kuma Idan mutum ya kwanta barci zuciyarsa na cike da tunanin alheri, to abune mai wuya a wannan dare bai yi mafarkin wani abu na alheri ba. 

Ya 'yan'uwana,Wannan ita ce hanyar kaiwa ga alheri da yalwa da farin ciki da kuma canza rayuwa da Qulla igiyar tunanin alheri aranka. Abu ne Mafi muhimmanci ga Mutumin da ya gane abubuwan da suke da amfani a gareshi,Mu sani tunanin alheri da fatansa kan sanya Allah ya a gaza wa mutum a duk harkokinsa,wannan kuwa yana buqatar a hada da Addu'a.
  

ALLAH YA KARA LAFIYA DA KARIYA A JAGORANA SHEIKH ZAKZAKY(H) DA MAI DAKINSA DA SAURAN ALMAJIRANSA🙏🙏

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post