AMFANIN LALLE DA IRIN MUHIMMANCIN SA AWAJAN DAN ADAM.
1: Ana dafa ganyen lalle ko garinsa da ruwa mace tashiga Na
mintuna 10/15 hatta karamar yarinya "Yar shekara 1 xa'a iya
sata a ciki yana maganin infection da cututtuka Na mata.

2: lalle yana maganin ciwon hakori da warin baki da kuma
tsatsar dake jikin hakora...idan aka dafa lalle da ruwa sai
aringa kuskure baki dashi. Sannan a samu garin lalle da
kanunfari da gawayi adakasu tare aringa goge baki dashi yana
kara karfin hakora sosai

3: lalle yana maganin ciwon kafa musamman irin kakannimmu
da iyaye jijiya ta rike gwiwa za'a kwaba lalle a kunsashi a
gwiwa sai a rufe da Leda ko babdeji abarshi Na tsawon awa
biyu ko daya sannan a cire, bayan ancire sai 'a samu
albabulnat adafashi a ruwan zafi sai a samu towel aringa
dannawa a kafar sai ahada ruwan kal da zaitun asa garin lalle
ahada sai a ringa shafawa a kafar yana maganin sosai domin
mungwadashi.

4:lalle yana maganin cin ruwa Na kafa idan aka lalle da ruwan
kal ko afram sai asa a kafar.

5:lalle yana maganin ciwon huhu idan aka samu ganyen
danyen lalle guda uku 3 sai a dafashi sannan asaka sugar ko
Zuma asha yana maganin ciwon huhu.

6:lalle yana maganin warin kashi da xakaji mutun yana wari da
tsami idan akaje wanka sai aringa dafa lalle yana kara wanke
jiki dashi yana maganin warin kashi sosai.

7:lalle yana maganin jiri(ajijiya) da mutun yakeyi idan aka dafa
lalle asaka Zuma maikyau asha.

8:lalle yana kara karfin farce da maganin tsagewar hannu ( Dan
uba) idan aka yawaita lalle a hannu ko kafa.

9:Ana Shankar lalle a hanci yana buda kwakwalwa..

10:Ana samun ganyen lalle guda uku ko biyu a jika a Kofi a
idan yajuku sai asa sugar asha amma ba'a karasha sai bayan
kwana biyu yana maganin ciwon koda.

11:Ana dafa lalle da Zuma mai kyau aringa sha yana maganin
hawan jini da bugun zuciya wallahi angwada angani.

12:Ana shafawa kuna lalle idan mutun ya kone ko yaji rauni sai
a samu kal tuffa a goga agun sannan a barbada garin lalle akai
kunar xai kame sosai.

13:Ana samun ganyen lalle guda 20 sai a samu ruwa cikin
kwanon San ruwa daya sugar gram 10 ko 20 ajika a ruwan a
ringa sha tsawon kwana 40 yana maganin kuturta insha Allah.

14: yin lalle a kafa yana budewa mace kofofin jini, musamman
macen da jinin al'ada yake mata wasa wata biyu ko uku
sannan yadawo to wallahi yin lalle a kafa tana magancewa
basaikin he Neman maganiba kugwada.

15: lalle yana maganin kurajan jiki daji ( Cancer) idan aka hada
lalle da man shanu aringa shafawa a jiji.

16:lalle yana maganin ciwon Mara ko cikin lokacin da mace
take jinin al'ada idan tasamu garin lallen saita kada aruwa
tasha.

17: asamu ganyen lalle guda 3 da furan lalle da Zuma ajika su
akofi da ruwan zafi asha yana maganin mura.

18:a hada garin lalle da kal aringa shafawa akai yana maganin
ciwon kai.

19: idan mutun yana habo jini yana ta zuba yaki tsayawa sai a
kwaba lalle a Dora akan hancin insha Allah jinin zai tsaya.

20: matar auren da tafiya budewa zata samu lalle ta kwaba da
ruwan dumi ta saka agabanta Na tsawan awa biyu sannan ta
cire tawanke da ruwan dumi yana matse mace sosai.

21:lalle yana maganin rauni Na ciwon sugar idan mai ciwon
sugar yaji rauni yakan Dade bai warkeba to idan aka kwaba
lalle akasa agun zai warke insha Allah.

22:a dafa lalle tare da ruwan kal sai aringa shafawa a baya
yana maganin ciwon baya ko kiringayin irin yanda shafawa
idan kai yana ciwo.

23:ana shawa jariri lalle idan anhaifeshi kafin aimasa wanka
ashfa masa lalle Na tsawon mintuna biyar ko uku yana
maganin cututtuka..

24:Shafa man lalle a karaya yana hade karaya akwai man lalle.

25:ana hada lalle da man wardi ko man lalle ashafawa me
cutar barin jiki.

26:ana hada lalle daman kahhh poor ba kafurba sai anja kahhh
poor yana maganin sanjin kashi.

27:ganye lalle guda biyu da ruwa Rabin Kofi da sugar tea
spoon asha yana maganin shawara.

28:lalle yana Magani karyewar gashi asamu garin lalle kwatan
Kofi da garin habbatussauda cokali 3 da cokali 3 Na ruwan
dumi ko a tafasa ashafa akai Na awa 3 ko 4 sannan a
wanke.....idan kuma gashi bashi da karfi sosai sai a sai asa
lalle Rabin Kofi da cokali biyu Na wardi sai ruwa kramin Kofi
sai ashafa Na awa 1 ko biyu sannan a wanke.

29 Ana hada lalle da Zuma ashafa agashi yana gyara gashi
sosai.

30:Ana hada
Lalle
Zuma
Manja
Hulba
Da kwai
Ashafa ajiki sannan ayi steaming da ruwan zafi (aturara jiki)
yana yaran jiki sosai.

31: ana shafawa gawa lalle yana gyarata.....

Wannan faida Dan Allah idan ka karanta to kawatsama duniya domin anfanuwar Alummar musulmi....

 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post