Yadda DR. Sheik Abduljabbar Kabara Ya Kammala Bawa Alkli Sarki Yola Gamsassun Hujjoji Game Da Auran Nana Safyya A Koton Kofar Kudu!!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Malam Yacigaba Da Bayanin Tufka Da Warwarar Da Take Cikin Hadisan Anas Na Karya Da Aka Nasaftawa Annabi SAW


Dr. Yace Karo A Tsakanin Wadannan Munanan Ruwayoyi Misali Hadisin Bn Abi Shaiba Na Cikin Muslim Wanda Shima Bn Abi Shaiba Yake Nuna A Nan Take Annabi (SAW) Yakamota A Yakin Ya Kwanta Da Ita, Kuma Kamar Yadda Na Fada Ta Kan Gawawwaki Aka Wuce Da Ita Kuma Gawawwakin Yan Uwanta Da Mijinta Da Babanta, Da Hadisin Muslim Na Zubairu Bn Harbin Da Yakarba Daga Anas 1365 Wanda Shi Kuma Yake Cewa Kan Hanyar Dawowa Yayi Kwanciyar Aure Da Ita,


Malam Yace Mai Makon Su Yiwa Annabi Adalci Na Cewar Amaryar Nan Guda Dayace Kuma Aka Samu Irin Wannan Karo A Ruwayoyin,


Amma Sai Suka Ce Duka Sun Inganta.


Amma Gashi A Cikin Ibn Hisham Mujalladi Na 4 Shafi Na 415 Sunan Babin


“BABIN TARIYAR ANNABI DA SAFIYYA DA GADIN ABU AYYUBA GA KUBBAR ANNABI”


Sai Yace Annabi Yayi


Angwanci Ko Dai A Khaibara Ko A Saddurrauha’I,


Duba San Rai Guri Daya,

Ta Yaya Za’ai Haka Ta Yiwu?

Sun San Ba’ayiba.


Irin Yadda Yayi Haka Ibn Kasir Yayi A


“BIDAYA WAN NIHAYA” Mujalladi Na 4 Shafi Na 211 Shima Yace Duk Biyun Anyi.


Ibn Qayyim A Cikin “ZADUL MA’AD” Juzu’I Na 2 Shafi Na 708 Sai Ya Canja Tsarin Maganar Saboda Ya Fuskanci Hankali Bazai Karbe Taba


Sai Yace Annabi (SAW) Ya Ribace Ta Sai Ya Umarci Bilal Ya Tafi Da Ita

Sannan Yayi Mata Tallan Musulunci.


___________________________________Anan Sai Malam Ya Dawo Kan Tuhumominsu Da Suka Gabatar Wa Kotu A Cajinsu.


___________________________________Malam Yace Daga Cikin Tuhuma Ta 3 Suka Ce Nayi Wa Ma’aiki Kazafi Da Kage

Cewa Ya Kwace Nana Safiyya.

To Ni Ba KWACE Nace Ba

Cewa Nayi KWACEWA

(Ya Bayar Ya Kwace)

Wanda Shi KWACEWA Daban Kwace Daban.

Wanda Lafazin Hakan Yazo Karara A Cewa Annabi (SAW) Ya Bashi

(Nana Safiyya) Bayan Tsegumin Kyanta Sai Yace Ya Kwato Ta Yace Yaje Ya Dauki Wata, 

Wannan Sunansa Kwacewa Ba Kwace Ba.

Shi Kwace Abinda Baka Baiwa Mutum Ba Ka karba,

Shi Kuwa Kwacewa Ka Bawa Mutum Kyauta Sanna Kace A Dawo Maka Da Ita Shine “Kwacewa” Kuma Wai Bayan Yaganta Kyakyawa

Wal Iyazu Billah.


Yana Daga Cikin Mummunan Bayanan Da Sukayi Akan Yadda Ma’aiki Ya Mallaketa Ta Wannan Mummunar Hanyar Kuma Da Kansu Sukazo Bayanin Dalilin Da Yasa Ma’aikin Allah Ya Bayar Da Ita Ya Kwaceta, Wanda Na Tabbatar Da Karyane Ba A Yiba Irin Bayanansu Zai Sa Musulmi Ya Zubar Da Hawaye Ga Misali A


Littafin “AL MUFHIM” Mujalladi Na 4 Shafi Na 109 Su Kace Ga Dalilin Kwacewa Bayan Bayarwa.

Wai Saboda Tana Daga Cikin Gidan Annabta Sannan Kyanta

(Wal iyazu billah)


Wai Kyau Yana Sa Jin Dadin Jima’i Shi Kuma Yawan Jima’ai Yana Sa A Haifi Yaya Masu Kyau. 


Malam Yace Don Haka Ni Banga Wani Dalili Ba Face Karawa Kwaba Ruwa Da Cin Mutuncin Annabi Da Hadisin Karya Idan Muka Duba,


“ATTAUDIH” Sharhin Bukhari Juzu’I Na 5 Shafi Na 329

Shima Maganar Kyanta Yayi Inda Suka Yi Ta Bayanin Ni’imar Da Take Cikin Jima’I Da Masu Kyau


Wannan Shine Abinda Suka Nasabtawa Annabi (S.A.W.)


Ni Kuma Nace Annabi Bazai Zama Haka Ba.


Shaida Na Daya Ya Fadi Cewa Suhaili Ya Fadi Dalilin Da Yasa Annabi (SAW) Ya Kwace Nana Safiyya A Lokacin In An Kula

Nace Masa Maganar Ibn Hajar Ce Amma Kuma Ya Kaucewa Ibn Hajar Din Saboda A Karatuttukana Na Bada Hujjoji Masu Karfi Da Suke Tabbatar Da Ibn Hajar Na Da Hannu Dumu Dumu A Kan Taba Mutuncin Annabi (SAW)


Wannan Yana Cikin Sharhinsa Na "Fathul Bari" Wannan Ne Yasa Nace Maganar Ibn Hajar Ce

Ba Ta Suhaili Ba Ce, Aduba

Mujalladi Na 7 Shafi Na 582 “FATHUL BARI”

Shi Cewa Yayi Suhaili Yace…..

Amma Tun Daga Sanda Yace “Kultu” Ya Zama Maganar Ibn Hajar Ce Ba Ta Suhaili Ba.


Sai Askalani Ya Cigaba Da Cewa Da Aka Ce Da Ma’aiki Yar Sarkinsu Ce Sai Yaga Bai Kamata Ace An Baiwa Dihya Ba Saboda Akwai Irinsa Da Yawa A Cikin Sahabbai Amma Ita Irin Masu Kyanta Kadanne.


Malam Yace Saboda Haka Shaida Ha’intar Kotu Yayi. 


Wannan Yana Daga Cikin Abinda Zai Mai Dashi Fyade Daraja Ta Daya,


Yazo Daga Ibn Umar Cikin Dai Fathul Bari Juzu’I Na Daya Shafi Na 461 Hasisi Na 16146

An Tambayi Ibn Umar Yaya Mutumin Da Ya Maida Yancin Kuyanga Sadakinta,

Sai Yace Kamar Mutumin Da Ya Bada Taguwa Hadayane Sannan Ya Dawo Yana Hawanta,


Kuma Duk Sahabbai Sun Hadu Akan Yin Hakan Haramun Ne Banda Abu Huraira Da Anas.


To Da Annabi Yayi Wannan Babu Yadda Za’ayi Ibn Umar Zai Fadi Haka Bayan Dashi Akayi Yakin Khaibar,


Sanna Ya Kawo Ibn Ma’ud Shima Ra’ayinsa Kenan A Hadisi Na 16147 


Sannan Ibn Sirina Shima Yana Fadar Irin Ta Ibn Umar


Sannan Ya Kawo Maganar Ada’u عطاء

To Duk Wadannan Suna Kara Munin Wannan Abu Idan Da Anyi Zai Zama Darja Ta Daya.


Inda Ace Gaskiya Ake Nema Tun Anan Hadisin Nan Yatabbata Karya Ce.

Saboda Ga Yadda Sahabbai Suke Kallon Wanda Yamaida Yanci Sadaki Haramunne.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post