Hirar Da nayi A Gidan Radio Maloney F.M A Garin Keffi Ta Jihar Nasarawa Kwana Ukku Da yin Mukabala Da Shek Abduljabbar Kabara (H)


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


A Ranar Talata 13-7-2021 da misalin qarfe 11:00-12:00 na rana anyi hira dani a wani gidan radio mai suna Maloney Fm a garin keffi na jihar Nassarawa akan muqabalar da aka gabatar a jihar kano tsakanin wasu malamai da Malam Abduljabbar (H) a wannan hira nayi bayani dalla- dalla game da fahimta ta da wannan al'amura, a jawabaina nace akwai dalilan da yasa ake yiwa Shehin malamin wannan taron gamayyar don karyashi wasu sabubban kuma tasgarone daga shi har nake cewa shi ba ma'asumi bane, wannan kalami bai yiwa da yawa na yan uwa dadi ba qarshe ma wasu sunyi amfani da wannan dama suka saka mini da zagi da zargi ,akwai hirar a wajen Najjarullah wanda ya saurari wannan hira zai fahimci cewa a dangane da fikri da hadisan qarya da malamin yake korewa ina tare dashi tunda na ja wasu hadisan a gidan rediyon,to abin mamaki a yanzu shine ire-iren wadannan mutane da suke zaginmu har yanzu naji sunyi shiru basa iya cewa komai akan wannan lamari kai wasu da yawansu sun firgita sun daina posting hotunansa a yanzu saboda tsoron kamu da dauri a kurkuku, wannan yasa nake kiran yan uwa cewa su gayyaci hankali sosai su bambamce tsakanin maqiyi da mai sabawa a fahimta, idan har malam yana sabawa da wasu a fahimta to dole sai an saba dashi shima, to irin harshen da za'a tattauna da wanda ya saba a fahimta dole ya sha bamban da harshen da za'a fuskanci magauci, wannan shine matakin farko na Nasiha ta ga yan uwa kafin Allah ya dawo dani mu shiga gwagwarmayar neman haqqimmu gabagadi ba tare da tsoro ko gudun mutuwa ba, zamu bi duk wani mataki na zaman lafiya wajen cigaba da yada aqidarmu ta matafitar Ahlul Bait (A.s) muna masu bibiyar bangarorin da mukayi tarayya a fahimta tare da cigaba da kiran mahukunta zuwa watsi da hukuncin da Alqali sarki yola yayi akan haramtacciyar shari'ar da aka dauki sama da shekara guda anayi wadda ta qare da wannan zalunci .

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post