Wafatin Nana Fadima Salamullahi Alaiha A Mahangar Shi'a Da Sunnah !!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Aliyu Samba


Kasancewar wannan maudu'i mai matukar tsauri musamman yanzu da aka siyasantar da addini zuwa maslahar wasu mutane, amma abu ne mai kyau musulmi ya wadatu da sani akan muhimman al'amuran da suka wakana kafin da lokacin wafatin Mawlatiy Zahra salamullahi alaiha. Saboda saɓanin da ake dashi tsakanin Makarantu biyu na Musulunci, ina nufin sunnah da shia, zan kawo hujjoji daga dukkan bangarori, a karshe kuma sai mu bar wa mai karatu cikakkiyar dama ya zabi fahimtar da tafi gamsar dashi. 


Yan shi'a sun tafi akan cewa Wafatin Nana Faɗima ya biyo bayan wasu nau'ikan cin zarafi da ta fuskanta a bayan wafatin Manzon Allah SAWA. 


Suna kafa hujja da Hadisin da aka ruwaito daga Nana A'isha Bint Abubakar Bn Abi Ƙuhafa cewa, Sayyida Faɗima SA ta nemi Khalifa Abubakar bn Abi Ƙuhafa ya bata abubuwa guda 3, sune Gadon ta, Fadak, da kuma Khumusi. Sai Khalifa yace da ita Annabi SAWA yace ba a'a gadon mu, abinda muka bari sadaka ne. Wannan yasa Khalifa Abubakar ya hana Sayyida Faɗima duka abunuwa ukun da ta buƙata.


Wannan al'amari ya sanya Sayyida Faɗima fushi da Khalifa Abubakar, sanadin haka ta kaurace masa, bata sake yi masa magana ba har tayi wafati watanni shida bayan wafatin Mahaifin Ta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam.


Lokacin da Sayyida Faɗima SA tayi shahada, Imam Ali AS ya binne ta da daddare, bai gayyaci Khalifa Abubakar ba don yi mata jana'iza, Imam Ali ne ya mata sallar Jana'iza.


Hadisin Nana A'isha da na ambata a sama ba wai iya a littafan shia yazo ba, ya zo har cikin Littafan Ahlussunnah da ake kira ''Sahihul Bukhari'' da ''Sahihu Muslim''. Ga matanin hadisin nan a kasa;


حَدَّثَنِي مُحَمَّدُ بْنُ رَافِعٍ، أَخْبَرَنَا حُجَيْنٌ، حَدَّثَنَا لَيْثٌ، عَنْ عُقَيْلٍ، عَنِ ابْنِ شِهَابٍ، عَنْ عُرْوَةَ بْنِ الزُّبَيْرِ، عَنْ عَائِشَةَ، أَنَّهَا أَخْبَرَتْهُ، أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ رَسُولِ اللَّهِ(ص)َ أَرْسَلَتْ إِلَى أَبِي بَكْرٍ الصِّدِّيقِ تَسْأَلُهُ مِيرَاثَهَا مِنْ رَسُولِ اللَّهِ(ص)َ مِمَّا أَفَاءَ اللَّهُ عَلَيْهِ بِالْمَدِينَةِ، وَفَدَكٍ، وَمَا بَقِيَ مِنْ خُمْسِ خَيْبَرَ، فَقَالَ أَبُو بَكْرٍ : إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ(صَ) قَالَ: "لَا نُورَثُ، مَا تَرَكْنَا صَدَقَةٌ".... فَأَبَى أَبُو بَكْرٍ أَنْ يَدْفَعَ إِلَى فَاطِمَةَ شَيْئًا، فَوَجَدَتْ فَاطِمَةُ عَلَى أَبِي بَكْرٍ فِي ذَلِكَ، قَالَ: فَهَجَرَتْهُ، فَلَمْ تُكَلِّمْهُ حَتَّى تُوُفِّيَتْ وَعَاشَتْ بَعْدَ رَسُولِ اللَّهِ(صَ) سِتَّةَ أَشْهُرٍ، فَلَمَّا تُوُفِّيَتْ دَفَنَهَا زَوْجُهَا عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ لَيْلًا، وَلَمْ يُؤْذِنْ بِهَا أَبَا بَكْرٍ، وَصَلَّى عَلَيْهَا عَلِيٌّ...

 

Bukhari hadisi mai lamba 3092, 3094, 3711, 4033, 4035, 4240, 5358, 6725, 6728, 6730, 7305 ).


- صحيح مسلم كتاب : الجهاد والسير | باب : قول النبي : "لا نورث، ما تركنا فهو صدقة"، الجزء رقم : 5، الصفحة رقم :153، الحديث : 1759 ( 52 )، 1757, 1758, 1759.


Bayan su akwai wasu littattafan Ahlussunnah kamar haka:


 سنن أبي داود

 ( 2963, 2968, 2976 ).


 سنن الترمذي

 ( 1608, 1609, 1610 ).


سنن النسائي

 ( 4141 )


موطأ مالك

 ( 2840 ).


 مسند أحمد 

(9, 25, 55, 58, 60, 78, 79, 425, 1781, 1782, 25125, 26260 ).


Nana Faɗima ta dogara da Alqur'ani a matsayin hujjar ta kan neman gadon mahaifin ta, wanda a har zuwa yau mabiya shi'a da wasu daga ahlussunnah suna ganin cewa lallai fahimtar Nana Faɗima itace gaskiya kuma itace daidai, Nima fahimta ta kenan. Allahu A'alamu. 


Yan shia suna kawo cewa kafin wafatin ta salamullahi alaiha, bayan hana ta gado, Fadak da kuma Khumusi da Khalifa Abubakar yayi, sun kawo cewa yayi umarni a je a bincike gidan ta ko akwai dukiyar Allah da Nana Faɗima ta ajiye a gidan a fito da ita. 


Babban malamin Ahlussunnah sheikhul Islam Ibn Taimiyya ya tabbatar da haka a cikin littafin sa Minhajussunnah, Yake cewa: 


ﻭَﻏَﺎﻳَﺔُ ﻣَﺎ ﻳُﻘَﺎﻝُ : ﺇِﻧَّﻪُ ﻛﺒﺲ ﺍﻟْﺒَﻴْﺖَ ﻟِﻴَﻨْﻈُﺮَ ﻫَﻞْ ﻓِﻴﻪِ ﺷَﻲْﺀٌ ﻣِﻦْ ﻣَﺎﻝِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳُﻘَﺴِّﻤُﻪُ، ﻭَﺃَﻥْ ﻳُﻌْﻄِﻴَﻪُ ﻟِﻤُﺴْﺘَﺤِﻘِّﻪِ، ﺛُﻢَّ ﺭَﺃَﻯ ﺃَﻧَّﻪُ ﻟَﻮْ ﺗَﺮَﻛَﻪُ ﻟَﻬُﻢْ ﻟَﺠَﺎﺯَ؛ ﻓَﺈِﻧَّﻪُ ﻳَﺠُﻮﺯُ ﺃَﻥْ ﻳُﻌْﻄِﻴَﻬُﻢْ ﻣِﻦْ ﻣَﺎﻝِ ﺍﻟْﻔَﻲْﺀِ .


- ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ ﻓﻲ ﻧﻘﺾ ﻛﻼﻡ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ﺍﻟﻘﺪﺭﻳﺔ : ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ : ﺝ 8 ، ﺹ 291


A wannan yunƙuri da akai na bincike a gidan Nana Faɗinsa SA, an ruwaito cewa Khalifa Umar Bin Khattab ya bigi Sayyida Zahra salamullahi alaiha a ciki wanda shine yayi sanadiyar ɓari da tayi na cikin Muhsin, Sannan kuma aka ruwaito cewa Khalifa Umar cikin fushi yayi umarnin a ƙone gidan da duk wanda ke cikin sa, ciki har da Imam Hassan da Imam Hussaini SA. 


Wani Malamin Ahlussunnah mai suna Shahristani ya kawo cikin littafin sa kamar haka:


ﺍﻥ ﻋﻤﺮ ﺿﺮﺏ ﺑﻄﻦ ﻓﺎﻃﻤﺔ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺒﻴﻌﺔ ﺣﺘﻰ ﺍﻟﻘﺖ ﺍﻟﺠﻨﻴﻦ ﻣﻦ ﺑﻄﻨﻬﺎ ﻭﻛﺎﻥ ﻳﺼﻴﺢ ﺍﺣﺮﻗﻮﺍ ﺩﺍﺭﻫﺎ ﺑﻤﻦ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﺍﺭ ﻏﻴﺮ ﻋﻠﻰ ﻭﻓﺎﻃﻤﺔ ﻭﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ...


- ﺍﻟﻤﻠﻞ ﻭﺍﻟﻨﺤﻞ : ﺍﻟﺸﻬﺮﺳﺘﺎﻧﻲ، ﺝ ١، ﺹ ٥٧ . ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻮﻓﺎﺓ : ٥٤٨ . ﺗﺤﻘﻴﻖ : ﻣﺤﻤﺪ ﺳﻴﺪ ﻛﻴﻼﻧﻲ . ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻤﻌﺮﻓﺔ، ﺑﻴﺮﻭﺕ - ﻟﺒﻨﺎﻥ .


Yan shia suna kan cewa Khalifa Abubakar da Khalifa Umar ba su tsaya akan tauye hakkin Fatimah (as) akan Khumusi, gadon babanta(saw) da Fadak ba kadai, sai da Umar ya jagoranci kona gidanta(as).


 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post