CUTA DA MAGANI:-Matsalar Rashin Haihuwa

 



MENENE INFERTILITY?INFERTILITY: 

Wata matsala ce da Mata ke fuskanta ta shafe sama da watanni 12 ba tareda ta samu ciki ba ko alamunsa.


ALAMOMIN INFERTILITY:


- Yawaitar Jin zafin yayin Saduwar aure.

- Hauhawar Jinin haila Mara misali, Mai tsaho, ko ciwon yayin al'adar.

- Fitar Jinin al'ada Mai duhu (Dark) or Shar.

- Wasan al'ada.

- Canzawar Kwayoyin Sinadarin al'ada.

- Qiba Mara musaltuwa.

- Yawaitar ciwon Mara.

- Yawaitar ciwon baya.

- Yawaitar tashin Zuciya ko amai Amman Baga masu ciki ba.


ABUBUWAN DAKAN KAWO MATSALAR RASHIN HAIHUWA (INFERTILITY):

- Genetic disorder (Cutar Gado)

- Age (Shekaru) akalla shekara 35 (Mata) 40 Kuma (Maza)

- Ciwon Sugar.

- Eating disorders (Cutar yunwa) kamar anorexia nervosa and bulimia.

- Shan giya

- Shan Taba

- Rashin motsa jiki.

- Yawan shakar guba (toxins) Kamar pesticides.

- Yawan motsa jiki mara qa'ida.

- Yawaitar shigar "ray" jikin mutum mussaman yayin aikin (cancer) ko aiki a radiation room.

- Kaciyar Mata (Female Genital Mutilation)

E.T.C


BINCIKEN DA AKEYI IDAN ANJE ASIBITI:

Binciken ya kasu Kashi-Kashi akwai na mata (Infertility) akwai Kuma na maza (Impotency)


¶ BINCIKEN MATA (INFERTILITY):


1. Abdominopelvic Ultrasound Scan da high vaginal swab (USS & HVS).


Anan za bukaci kiyi wannan binciken alokacin da ake zargin sanyin Mara ne ya janyo Miki wannan matsala.


Sannan wannan bincike zai iya nuna Koda akwai wani Abu acikin mahaifar kamar matsalar Fibroid, Ovarian cyst, endometrial tumors, uterine synechia da sauransu Wanda suma duk zasu iya janyo Rashin haihuwa.


2. Hysterosalpingography


Wannan binciken zai nuna Koda akwai toshewar hannun mahaifa (tubal blockage) ko taruwar ruwa acikin hannun mahaifar (hydrosalpinx).


Anfi yin wannan bincike a matan da sukai fama da ciwon sanyi.


3. Hormonal analysis.


Wannan test din zai nuna 

Koda sinadaran "Thyroid gland watoh T3 &T4 da TSH sunyi yawa ko kadan a jiki, haka zalika zaikara nuna sinadarin prolactin ko yayi yawa ko kadan shima (yakanyi yawa a hyperprolactinaemia)". Sannan zai kara nuna yawan sinadaran LH, FSH, PROGESTERONE da sauransu ajiki.


4. Endometrial biopsy


Wannan binciken zai nuna Koda akwai kansa (Ciwon Daji) acikin mahaifa.


6. Laparoscopy.


Wannan binciken zai nuna ko da akwai wata matsala a ciki ko mahaifa. wannan binciken kusan shine binciken kwakwaf Wanda zainuna komai.


¶ BINCIKEN MAZA (IMPOTENCY):


1. Physical Examination:


Wannan binciken zai taimaka wajen gani da ido ko akwai raguwar dan maraina ko sandarewar jijiyo, ko fesowar kuraje dadai sauran su.


2. Semen Analysis (SA):


Wannan binciken zai taimaka wajen gano cututtukan da suka shafi maniyyi.


3. Blood tests E.g (ED, BGT, CBC, low T, Hemoglobin A1c w/eAG, Prostate-specific).


Wannan gwaji ne na jini da'ake Don gano ko akwai gwayoyin Cututtuka, matsalar, Rashin miqewar al'aura, ciwon sugar, sanin adadin gwayoyin jini, Wanda matsalar hakan Kan janyo rashin haihuwa ga maza.


4. Urine tests (urinalysis).


Wannan gwaji ne da akeyi na fitsari don gano kwayoyin cututtuka dake kawo matsalar sanyi Wanda hakan Kan Hana haihuwa.


5. Ultrasound Scan (USS)


Likita zai buqaci wannan binciken alokacin da ya ke zargin sanyin Mara, ko toshewar hanyar maniyyi, fitsari ne ya janyo Maka wannan matsala.


6. Psychological exam.


Wannan gwaji ne akeyi na auna tunani ko kwakwalwa, Idan ana tunanin kanada matsalar tabin hankili ko rangwaminsa.


DAGA QARSHE: Bawa yasa aransa haihuwa Allah ke bayarwa aduk lokacin daya so ga Wanda Kuma yaso, sannan tashi neman maganin cuta ibadane, Idan mukai duba da Allah bai saukar da cuta ba face Saida ya fara Samar da maganinta.


SHAWARA: Duk Wacce/Wanda yake fama da wannan matsalar to asharwarce ya ziyarci asibiti mafi kusa Don gano inda matsalar take tareda bada mafita,

Haqiqa Shan magani barkatai agida ko akan hanya, ko burus da al'amarin bashi ne mafita ba.


ALLAH UBANGIJI YA BAMU LAFIYA, YALWATUWAR ARZIQI MAI AMFANI, DA KUMA ZAMAN LAFIYA AMIN YA RABBI.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group din mu na Telegram Anan


👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/


DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post