CIKIN FUSHI:- Shari'ar Sheikh Abdul-Jabbar Wacce Riba Miyagun Malaman Musulunci Suka Ci..?? - Daga Alkalamin Ado Isah Guda



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BURIN KOWANNE MUMINI SHINE YA MUTUM KAN HANYAR ALLAH


Ita shahada zabin Allah ce kuma daukaka ga wanda ya same ta, shi yasa bisa zabi na Allah ya karbi rayukan A'imma (A. S) a matsayin shahidai. 


Fiyayyen halitta Manzo Muhammad Bn Abdullahi (S. A. W. W) bayan cutar dashi da akayi kan gaskiya sai kuma qarshen rayuwarsa da zama shahada sakamon guba (poison) da aka dura masa, wanda hakan ya zama qarin karama wacce Allah ke karrama bayinSa salihai da ita. 


Ranar 18th ga Zul-Hijjah 1443 shekarar da ta wuce ta zama babbar rana ta zalunci wacce azzalumar gwamnatin Kano wacce tayi amfani da miyagun mutane masu amsa sunan malaman muslimci ta daure (prison) Sheikh Abdul-Jabbar bisa wata manufa tasu boyayyiya ta hanyar bayyana qarya da cewa wai ya ci mutuncin Annabin rahma (A. A. W. W, alhali ba Annabin rahman ne cikin zukatansu ba.


Ba zai taba yiwuwa ace an kafa hukumar muslimci mai iko qarqashin gwamnatin kafirci ba, ballantana ace wai an samar da wata kotu ta muslimci mai aiki da dokar muslimci. Idan hukuma ko kotun muslimci aka ce an samar, to, babban ma'aunin na auna wannan hukuma ko kotu shine abinda ke iko a samanta . Idan har muslimci ne ke iko a kanta sai muce lalle ta muslimci ce. Amma in har ya zama kafirci ne mai iko da ita, to, sunan wannan abinda aka samar shine zalunci.


Sheikh Abdul-Jabbar bai ci mutuncin Annabi (S. A. W. W) ba, sai dai bada kariya wajen tsare mutuncinsa da martabarsa (S. A. W. W), domin yana yaqi ne da munanan aqidu da aka cusa cikin littafin muslimci don biyan buqatu da kare munanan ayyukan wasu da suka yi cikin muslimci. Su kuma masu cewa Sheikh ya aikata wannan abinda suke fada sunyi hakan ne  don kare matsayinsu da qoqarin boye gaskiya. 


Da ace domin Allah suke yin wannan aiki nasu haqiqa da anga/ji abinda su kayi game da maganar da Dr. Gumi ya siffanta Annabin rahma (S. A. W. W) a matsayin ambulan (envelope) in an cire saqon dake cikinsa. Duk wanda ya siffanta Annabi (S. A. W. W) da wannan siffa shi ya kamata a hukunta shi a matsayin wanda yayi cin zarafi matuqar dai ana yi ne don Allah. 


      AIKIN YAHUDAWA NE 


Yahudawa sun saba yin amfani da miyagun malamai wajen cimma manufofinta don daqilar da abinda ba sa so na muslimci, za mu iya fahintar haka yayin data samar da miyagun maluma tayi amfani dasu wajen baqanta da'awar Sayyid Zakzaky (H) da shi kansa, wanda hakan ke bada dama na rashin ganin tausayi game da dukkan abinda zasu aikata kan ita da'awar da jagoran nata. Hakan kuwa yayi tasiri sosai, domin sunyi aiki kuma an biya su, sai dai kuma a qarshe ba suyi nasara ba tunda abinda suke son gani bai samu ba. 


DALILIN MALAMAN NA 'DAUKAR WANNAN MATAKI 


Wasu dalilai ne wadanda ba za su wuce uku (3) ba,  duk abinda zai biyo baya abu ne wanda bai kaisu ba. Wadannan dalilai kuwa sune :


(1)- GUDUN QASQANCIN DUNIYA :- Su wadannan sun zama wadanda ke cin abincinsu da wannan addini, sun sami mabiya suna karantar dasu qarerayin da magabansu suka qirqira suka cika littafan muslimci dasu, sai kuma aka sami wanda yake warware dukkan wannan qulli ta hanyar ilimi ba jahilci ba, kuma yake yaye duhun da aka dilmiyar da mutane cikinsa ba tare da sun fahinci hakan ba. Shine suke gani in har suka bari aka gano su, to,  za a guje su, kuma matsayinsu zai ruguje. Saboda haka sai suka dau wannan mataki na qazafi ga Sheikh don kare matsayinsu. 


(2)- KARE QARERAYIN MALAMANSU :- Tabbas malamansu sun cika littafan muslimci da qarerayi kuma suka yiwa littafan katanga da cewa dukkan abinda ke cikinsu gaskiya ne , alhali qarerayi ne. Sai suka ga cewa lalle idan suka bar aikinsa ya cigaba, da sannu kowa zai gano ashe maluman nasu Fanko ne, su kansu basu fahimci gaskiya ba ballantana su dora mutane kanta. Saboda haka su kaga gara suyi sauri su kawo qarshen wannan haske dake bayyana tun kafin ya haskaka dukkan duniya, sai dai abinda basu sani ba shine, ai hasken ya riga ya mamaye sararin samaniya yadda ke haskaka dukkan abinda ke qarqashinsa, saboda haka sunyi aikin banza da kuma daukar zunubi wanda ba za a kankare musu shi ba.


(3)- KARE MUNANAN AYYUKAN SAHABBAI :- Sun fahinci cewa idan bincike yayi zurfi har aka samu cewa abinda malaman nasu suka rubuta cikin littafai ya tabbata cewa maganganun daga Sahabbai ya fito, to, zai zama babban abinda za a duba shine yaya wadannan maganganu nasu suke in an gwama su da shaidar da Allah ya yiwa Annabi (S. A. W. W) cikin Al-Qur'ani ? Idan aka sami cin karo da ayoyin Al-Qur'ani haqiqa zai zama wadannan Sahabbai sun yiwa Annabi (S. A. W. W) qarya, kuma sun ci zarafinsa. Saboda haka a qarshe za a hukunta su a matsayin wadanda suka sabawa Allah ta hanyar cin zarafin AnnabinSa (S. A. W. W). 


A irin nasu matsayi da tasu fahinta shine, a maimakon ace su Sahabban sunyi kuskure gara a tabbatarwa Annabi (S. A. W. W) daukar dukkan munanan abubuwan da aka alaqanta shi dasu, domin matsayinsu a gunsu ya fi matsayin Annabi (S. A. W. W) wanda yazo da shiriya ya kuma fitar dasu daga duhu, duk da cewa daga baya sun koma cikinsa. 


Wannan ba shine makircin farko a tarihin muslimci ba, domin an yiwa Manzanni (A. S) yadda takai aka kashe wasunsu kamar yadda Qur'ani ya kawo mana, wasu kuma aka cutar dasu ta hanyar qazafofi da shafar mutuncinsu (A. S). Kenan duk abinda muka gani daga wadannan miyagun malamai ba zai taba zama abin mamaki ba, sai dai tuno mana abinda ya faru cikin tarihin muslimci. 


HUKUNCIN DA AKA YANKEWA ANNABI IBRAHIM (A. S) BAI TABBATU BA 


A daidai lokacin da kafirai su kaga Annabi Ibrahim (A. S) ya qasqantar dasu da ababen da suke bautawa koma-bayan Allah sai suka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefa shi cikin wuta don halakar da shi. Sun himmatu kuma sun aikata, sai Allah mai ikon kashewa da rayawa ya nuna musu cewa ai ba su  ke da wannan iko ba. Saboda haka sai Ya nuna musu gazawarsu ta hanyar ikonSa (S. W. A).


Hakan ma ta faru kan Sayyid Zakzaky (H) daga ranar 12-14 na watan Satumba, 2015 a garin Zaria, sai dai Allah ya tseratar dashi daga wannan wuta da aka kunnata a kansa cikin gidansa kamar yadda aka tseratar da Annabi Ibrahim (A. S). 


SHAHADA 'DAUKAKA CE DAGA ALLAH 


Idan kuma Allah yayi nufin daukaka darajar Sheikh Abdul-Jabbar zuwa daraja madaukakiya sai ya karbi ransa ta wannan hanya wacce azzalumai suka hukunta. Idan kuwa hakan ta faru ya zama abin alfahari gare shi a lahira, kuma abin alfahari ga mabiyansa anan duniya, domin daukaka darajarsa da Allah yayi ta hanyar da ya daukaka wasu daga cikin bayinSa Manzanni (A. S). 


            JARUNTAKARSA 


Tun farkon fara wannan da'awa tasa ya shelanta cewa babu gudu babu ja da baya kan wannan hanya, sai dai irin abinda ya sami magabansa ya same shi, domin neman yardar Allah yake yi ba neman yardar wani ba. Sannan kuma shi kadai zai tsaya gaban Allah yayin hukunta shi, saboda haka dole ya bayyana haqiqanin abinda ya sani na gaskiya.


Har zuwa wannan rana 15th December, 2022/  21st Jimada-Ulah, 1444 bayan zartar da wannan hukunci kansa bai yi saranda ba, kuma bai zargi Allah ko yin da-na-sani kan abinda yake yi ba. 


Sayyid Zakzaky (H) ya bayyanawa azzalumar hukuma cewa yana shirye na karbar duk hukuncin da za su zartar a kansa, amma dai ba zai juya daga haqiqanin abinda yake kansa ba. 


Kamar hakane, Sheikh Abdul-Jabbar ya nuna cewa ya karbi wannan hukuncin da suka zartar a kansa, amma ya jaddada musu cewa shi baiyi laifin komai ba bisa zargin da suke masa. Wanda hakan ke nuna zai karbi hukuncin ne a matsayin wanda aka zalunta (MAZLUMI). 


YAA ALLAH KAI KAKE BADA KARIYARKA GA BAYINKA SAHIHAI, KA BADA KARIYA GA SHEIKH ABDUL-JABBAR KAMAR YADDA KA BADA KARIYA GA SAYYID ZAKZAKY (H). 


KA KUNYATA WADANNAN QANANAN AZZALUMAI KAMAR YADDA KA KUNYATA BABBAR AZZALUMA GWAMNATIN BUHARI  


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


16th December, 2022/  22nd Jimada-Ulah, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post