ZAINABUL-KHUBRAH BNT IMAM ALI (A. S) !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


HAIHUWARTA DA MATSAYINTA (S. A) 


Matsayin Sayyidah Zainab (S. A) matsayi wanda baki ba zai iya bayyana shi ba, haka alqalami ba zai iya rubuta shi ba. Dalilin wannan magana kuwa shine kasancewarta daga tsatso mafi inganci cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W). 


An haife ta ne a wannan wata na Jimada-Ulah cikin shekara ta biyar bayan Hijrar Manzon Allah (S. A. W. W).


Mahaifinta shine Imam Ali Bn Abu Dhabi (A.S), mahaifiyarta kuwa ita ce Sayyidah Fatimatuz-Zahra (S. A) Bnt Rasulul-Lahi Muhammad Bn Abdullah (S. A. W. W). 'Yar'uwa ce shaqiqiya wajen Imam Hassan da Hussaini (A. S) wacce ta kasance 'ya ta uku wajen Fatimatu Bnt Muhammad (S. A). 


Ta taso qarqashin kulawa da tarbiyyar mahaifanta (A. S) har zuwa aurenta. Saboda haka duk wata fasahar magana irin ta mahaifiyarta da kuma jaruntaka na mahaifinta ta dauka. Shi yasa idan ta bude baki tana magana tamkar daga bakin Imam Ali (A. S) take fitowa. 



Tana daga cikin Ahlul-Bait (A. S) wacce dukkan wani matsayi wanda iyalan Annabi (S. A. W. W) suke dashi ita ma tana dashi. 


Ya zo cikin riwaya inda Annabi (S. A. W. W) ya tabbatar da wannan matsayi kamar yadda za mu gani cikin wadannan riwayoyi dake tafe. 


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽



كِتَابُ الدَّلَائِلِ، لِمُحَمَّدِ بْنِ جَرِيرٍ الطَّبَرِيِّ عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ أَحْمَدَ الطَّبَرِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ أَحْمَدَ الْقَاضِي التَّنُوخِيِّ عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ عَبْدِ السَّلَامِ عَنْ عُثْمَانَ بْنِ أَبِي شَيْبَةَ عَنْ جَرِيرٍ عَنْ شَيْبَةَ بْنِ نَعَامَةَ عَنْ فَاطِمَةَ الصُّغْرَى عَنْ فَاطِمَةَ الْكُبْرَى قَالَتْ قَالَ النَّبِيُّ ص‏ لِكُلِّ نَبِيٍّ عَصَبَةٌ يَنْتَمُونَ إِلَيْهِ وَ إِنَّ فَاطِمَةَ عَصَبَتِيَ الَّتِي تَنْتَمِي إِلَيَ‏[4].


Ya zo cikin Kitabul-Dala'ilu na Muhammad Bn Jareer Ad-Dabariy, daga Ibrahim Bn Ahmad Ad-Dabariy, daga Muhammad Bn Ahmad Al-Qadhiy At-Tanuukheeyi, daga Ibrahim Bn Abdus-Salam, daga Usmana Bn Abiy Shaibata, daga Jareer daga Shaibata Bn Na'aamata, daga Fadimatus-Sugrah, daga Fadimatul-Kubrah tace : Annabi (S. A. W. W) yace :


" KOWANNE ANNABI YANA DA NASABA WACCE AKE JINGINA SHI GARE TA, KUMA LALLE FADIMATU SHUGABAR NASABATA CE WACCE AKE JINGINATA ZUWA GARE NI. "


A wata riwaya kuma yake cewa :


قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏" كُلُّ بَنِي أُمٍّ يَنْتَمُونَ إِلَى عَصَبَتِهِمْ إِلَّا وُلْدَ 

فَاطِمَةَ فَإِنِّي أَنَا أَبُوهُمْ وَ عَصَبَتُهُمْ."


" KOWANNE 'YAYAN UWA  ANA JINGINASU SHI ZUWA GA NASABARSU (ta wajen Uba), SAI DAI 'YA'YAN FADIMATU, DOMIN NI NINE UBANSU KUMA NASABARSU. "


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 229


Wadannan riwayoyi suna suna mana matsayin Sayyidah Zainab (S. A) ne, domin kuwa kai-tsaye za a jingina ne zuwa ga Manzon Allah (S. A. W. W). 


Ta auri dan Baffanta Abdullahi Bn Ja'afarud-'Dayyar Bn Abu Dhabi ma'abocin fuffuke biyu, kuma ta haifa masa 'ya'yayen kamar haka :


(1)- Aliyu, 


(2)- Aunan (wanda ake kiransa Akbar), 


(3)- Abbas, 


(4)- Muhammad, da kuma 


(5)- Ummu-Kulthum. 


Ta kasance tare da Imam Hussaini (A. S) a daidai lokacin da rundunar Yazeed (L. A) ta tsare shi kuma tayi masa kisan gilla a wani guri da ake kira KARBALA .


Sayyid Zainab (S. A) ta kasance Uwa da Uba a daidai wannan lokaci, domin an karkashe dukkan mazan dake tare da Imam Hussain (A. S) in ka cire Imam Aliyu Zainul-Abideen (A. S) wanda ya kasance marar lafiya wanda ba ya iya yin komai a lokacin don taimakon mahaifinsa Imam Hussain (A. S), sai dai kaifin harshe wanda ya riqa amfani dashi wajen bayyanar da zaluncin daya faru a wannan rana. 


Sayyidah (S. A) ta kasance ita wacce ke rarrashin qananan yara don qarfafarsu tare da nuna tausayi gare su cikin yanayin da suka sami kansu ciki na wannan zalunci. 


Haqiqa da ba don Sayyidah Zainab (S. A) ba tabbas da ba a sami haqiqanin tarihin abinda ya faru a wannan waqi'a ba, domin ta taimaka sosai wajen bayyanar da wannan zalunci da aka yiwa iyalan Manzon Allah (S. A. W. W) da kuma bayyanar da haqiqanin matsayinsu sabanin yadda maqiya suka riqa shelantawa wai su Bayi ne ribatattun yaqi. 


AMINCI YA TABBATA A GARE KI A RANAR HAIHUWARKI DA RANAR DA KIKA MUTU DA KUMA RANAR DA ZA A TASHE KI KINA RAYAYYIYA. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


         (08137925034)


29th November, 2022/  5th Jimada-Ulah, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post