Za a bude wasannin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya (wold Cup) da karatun Qur'ani Mai Girma ,

 


Bin Muhammad 

2022-11-20 KD


Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya labarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Qaira 24 cewa, a yau Lahadi 20 ga watan Nuwamban shekarar 2022 da za'a fara gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022, idanun duniya sun karkata kan Doha babban birnin kasar Qatar; Inda za a bude gasar kwallon kafa mafi shahara a duniya.


Za a fara bikin bude gasar cin kofin duniya da karatun ayoyin kur’ani mai tsarki daga bakin Ghanem al-Muftah, wani makarancin Qatar wanda Qatar ta gabatar a matsayin jakadan gasar cin kofin duniya ta 2022.


Kazalika Qatar ta bude gasar cin kofin kasashen Larabawa da ta karbi bakunci a bara, da ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda hakan ke nuni da riko da wannan kasa ta addinin Musulunci da kuma gudanar da bukukuwan ibadar Musulunci Musamman miliyoyin mutane daga ko'ina cikin duniya ne ke kallon wasannin gasar cin kofin duniya.


Filin wasa na Elbit zai karbi bakuncin tawagar kasar Qatar da Ecuador a bude gasar cin kofin duniya ta 2022 a yammacin yau 20 ga watan Nuwamba.


Masu amfani da shafukan sada zumunta a wannan kasa sun yi maraba da bude gasar cin kofin duniya da kamshin karatun ayoyin kur’ani mai tsarki na Ghanem al-Muftah, wadanda suka bayyana hakan a matsayin abin alfahari ga kasarsu.


Ghanem al-Muftah na daya daga cikin abin koyi ga dimbin matasan larabawa, domin duk da ciwon da ke dauke da cutar ta caudal regression syndrome, tana son aiki da rayuwa kuma tana rayuwa da rabin jikinta ba tare da kasawa ba, ita “Jakadiya ce ,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post