Sabuwar hanyar da barayin internet suka bullo da ita don cutar mutane

 

Hukumar Efcc

EFCC HELP DESK: Hukumar EFCC tana ankarar da al’umma game da wata sabuwar hanya da ‘yan damfara suke bi wajen satar bayanai da kuma kudadan mutane a cikin satin nan.


Abu ne na gaggawa idan ka karanta ka turawa sauran ‘yan’uwa link din domin su ma su karanta su ankare da wuri please its urgent.


Wandannan masu damfara suna yi wa mutane flashing ( ba kira suke ba ) flashing za su ma, kuma ba ya wuce 1 ring. Idan ka sake ka bi flashing din nasu cikin sakan 3 za yi copy na duk contacts dinka, idan da bayanan kadinka na banki ko wasu muhimman lambobi na bankinka sai su datsi account din naka su yashe ma kudi. Allah Ya kiyaye.


Ga lambobin kamar haka, idan suka ma flashing kar ka bi:


Tel: +37127913091


Tel: +37178565072


Tel: +56322553736


Tel: +37052529259


Tel: +375602605281


Tel: +255901130460


Ba wai su kadai ba ne, ka da su sake ku bi flashing na duk wata lamba da ta fara da:


+371


+375


+381


Bayan Hukumar ta EFCC HELP DESK ya bibiyi lambobin ta gano code din kasashen wadanda su ne kamar haka:


+375 Code din Kasar Belarus.


+371 Code din Kasar Lativa.


+381 Code din Kasar Serbia.


+563 Code din Kasar Valparaiso.


+370 Code din Kasar Vilnius.


+255 Codin Kasar Tanzania.


+385 Code din Kasar Croatia


Saboda haka kada mutum ya sake ya daga kira ko kuma ya bi flashing idan har na wadannan codes da muka zayyano a sama ne.


Allah Ya kiyaye.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/


DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post