Shin kunsan Salati ga Manzon Allah(S) Umarni ne na Allah ga dukkan Mai Imani ?


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE. 

Wanda yayiwa Manzon Allah (SAWW) Salati ya Cika Umarnin Allah ne, da Yin koyi Cikin Abinda Allah da Mala'ikunsa sukeyi ga Manzon Allah(S). Kuma yayi koyi ga Muminai masu imani. 

- Manzon Allah (S) Yace; duk inda kuka sami kanku kuyi salati a gare ni, domin salatin ku yana zuwa gare ni, salatin ku a gareni gaskene a gare ku a kan siradi. 

__FALALAR SALATIN ANNABI ARANAR JUMA'A__

   "Manzon rahama (s) yace wanda yayi salati agareni aranar juma'a guda dari to Allah zai biya masa bukatunsa guda sittin (60), talatin na duniya talatin na lahira". [ sawabull a'amal 188]. 

- Daga imam baqir (as) yace idan zakai sallar la'asar a ranar juma'a kuce ya ubangiji kayi salati ga annabi da alayensa, wasiyan yardaddu da mafificin salati ka yi Albarka a gare su da amincewa a garesu da rayukansu da jikkunansu, 

Wanda duk yayi wan nan salatin bayan sallar la'asar ubangiji zai rubuta masa kyawawa dubu 1000 za'a biya masa bukatarsa kuma za'a daukaka darajarsa sau dubu dari. 

-Manzon Allah (S) ya ce; "Ranar Alƙiyama zan tsaya a wurin Mizani, duk mutumin da munanan ayyukan suka nauyaya akan kyawawa,sai in rika kawo salatin da ya yi mun (ina ɗorawa, akan Mizaninsa) har sai kyawawan aikinsa sun yi rinjaye" (thawabul A'amal. 187)...

-Manzon Allah (S) ya ce; "Ku ɗaga sautin muryoyinku wajan yin salati a gareni, domin yana tafiyar da munafinci daga zuciya". (Wasa'ilus-shi'a)...

- Manzon Allah (S) yace duk wanda ya rubuta salati na arubu ce, to Mala'iku bazasu gushe ba suna roka masa gafara, indai sunana bai goge ba a cikin salatin.

- Antambayi Imam Bakir(AS) cewa, wacce Sallah ce aka wajabta ko ba Alwala?. Imam Bakir (AS) yace Itace salatin Annabi (S A W W). (AL-MUNAKIB J-1, SH-244.

- A wani Hadisi Abu Ja'afar (a.s) ya fadi cewa; "Da bawa zai shiga wuta ya zauna tsawon shekaru Dubu saba'in sau saba'in! Inya roqi Allah cewa " Don darajar Annabi Muhammad Da Iyalansa kayi min rahama" to da nan take wutar zatai sanyi gareshi, Kuma Allah zai turo Mala'ika Jibreelu ya fissheshi Daga cikinta. Allah yace; "Na Daukawa kaina cewa, bawa ba zai roqeni don darajar (Annabi) Muhammad Da Iyalan Gidansa ba, face na gafarta masa abinda ke tsakanina dashi". (Thawabul a'amal. 187). 

                  اللهم صل علي محمدوال محمد

__Juma'at Mubak.🌹

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post