MATSAYIN AURE DA CIN ABINCIN AHLUL-KITAB !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


HUKUNCIN AYAR DA MA'ANARTA 


Qur'ani ya zo da magana game da halascin auren Ahlul-Kitaab da cin abincinsu, wanda hakan ya kawo sabanin fahimta  tsakanin malamai ko kuma makarantu na musulmi. 


A yau za muyi magana ne ta hanyar dogaro da nassosi wadanda suka nuna mana haqiqanin fassara ko ma'anar wanda aya da tazo da wannan halasci. 


Ba tare da tsawaitawa ba za mu shiga cikin riwayoyin kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


                      (1)


الباقر (عليه السلام)- عَنْ أَبِي‌الْجَارُودِ قَال سَأَلْتُ أَبَاجَعْفَرٍ (عليه السلام) عَنْ قَوْلِ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ: وَ طَعامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتابَ حِلٌّ لَكُمْ وَ طَعامُكُمْ حِلٌّ لَهُمْ فَقَالَ (عليه السلام) الْحُبُوبُ وَ الْبُقُولُ.


Daga Imam Baqir (A. S), daga baban Jaruudi yace : Na tambayi baban Ja'afar (A. S) game da fadin Allah mai girma da daukaka :


" KUMA ABINCIN WADANDA AKA BAWA LITTAFI HALAS NE GARE KU KUMA ABINCINKU HALAS NE GARE SU. "


Sai (A. S) yace : " Ai (ana nufin) qwayar (abinci ne) da abubuwan da suka mabunqasa qasa. "


(Wato irin su tsabar wake, gyada, alkama, rogo, dankali, doya da sauransu). 


المصدر : 

 الكافي، ج6، ص264/ وسائل الشيعةًْ، ج24، ص204/ بحارالأنوار، ج63، ص24/ 

بحارالأنوار، ج77، ص45/ المحاسن، ج2، ص454/ المحاسن، ج2، ص584/ نورالثقلين/

 البرهان - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص624


                          (2)


علي بن ابراهيم القمي (رحمه الله)- قَوْلُهُ: وَ طَعامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتابَ حِلٌّ لَكُمْ قَالَ: يَعْنِي الصَّادِقَ (عليه السلام) عَنَي بِطَعَامِهِمْ هَاهُنَا الْحُبُوبَ وَ الْفَاكِهَةَ غَيْرَ الذَّبَائِحِ الَّتِي يَذْبَحُونَهَا فَإِنَّهُمْ لَا يَذْكُرُونَ اسْمَ اللَّهِ خَالِصاً عَلَى ذَبَائِحِهِمْ ثُمَّ قَالَ وَ اللَّهِ مَا اسْتَحَلُّوا ذَبَائِحَكُمْ فَكَيْفَ تَسْتَحِلُّونَ ذَبَائِحَهُمْ.


Daga Aliyu Bn Ibrahim Al-Qummy (Allah yayi masa rahma) - Fadinsa :


" KUMA ABINCIN WADANDA AKA BAWA LITTAFI HALAS NE GARE KU. " Yace :


Abin nufi Sadiq (A. S) yace :


" Abincinsu anan ana nufin qwayoyi (tsaba)  da ababen marmari (irin su mangoro, lemo, ayaba, da makamantansu) banda yankansu wadanda suke yankawa, domin su ba sa ambaton sunan Allah kadai akan ababen yankan nasu. "


Sa'annan yace :


" Wallahi basu halasta yankanku, to, ta yaya za ku halasta yankansu? "


المصدر :  عوالي اللآلي، ج2، ص17/ نورالثقلين - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص626


                     (3)


الرضا (عليه السلام)- عَنِ الْحَسَنِ‌بْنِ‌جَهْمٍ قَالَ: قَالَ لِي أَبُوالْحَسَنِ‌الرِّضَا (عليه السلام) يَا أَبَامُحَمَّدٍ مَا تَقُولُ فِي رَجُلٍ يَتَزَوَّجُ نَصْرَانِيَّةً عَلَى مُسْلِمَةٍ قُلْتُ جُعِلْتُ فِدَاكَ وَ مَا قَوْلِي بَيْنَ يَدَيْكَ قَالَ لَتَقُولَنَّ فَإِنَّ ذَلِكَ يُعْلَمُ بِهِ قَوْلِي قُلْتُ لَا يَجُوزُ تَزْوِيجُ النَّصْرَانِيَّةِ عَلَى مُسْلِمَةٍ وَ لَا غَيْرِ مُسْلِمَةٍ قَالَ وَ لِمَ قُلْتُ لِقَوْلِ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ: وَ لا تَنْكِحُوا الْمُشْرِكاتِ حَتَّي يُؤْمِنَّ قَالَ فَمَا تَقُولُ فِي هَذِهِ الْآيَةِ: وَ الْمُحْصَناتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتابَ مِنْ قَبْلِكُمْ قُلْتُ فَقَوْلُهُ وَ لا تَنْكِحُوا الْمُشْرِكاتِ نَسَخَتْ هَذِهِ الْآيَةَ فَتَبَسَّمَ ثُمَّ سَكَتَ.


Daga Ridha (A. S), Daga Hassan Bn Jahmi yace :


Baban Hassan Ridha (A. S) yace min : " Yaa baban Muhammad, me kuke cewa game da mutumin da ya aurar da Banasariya ga musulmi ?"  


Sai nace : Na sanya ka fansa . Ina ni da magana a gabanka?  Yace :


" Kuna cewa lalle haka ana iya saninsa daga maganata. "


Nace : Ba ya inganta auren Banasariya ga musulmi, ko kuma wacce ba musulma ba. Yace :


" (To) Don menene kuka fada saboda fadin Allah mai girma da daukaka : KUMA KADA KU AURI MUSHRIKA HAR SAI TAYI IMANI. " Yace :


" Kuma me kuke fada game da wannan aya : " DA KUMA KATANGAGGIYA DAGA WADANDA AKA BAWA LITTAFI DAGA GABANINKU. "


Nace : Shine fadinsa : " KUMA KADA KU AURI MUSHRIKA... " Ta soke wannan aya.  Sai yayi murmushi sa'an nan yayi shiru. 


المصدر : 

 الكافي، ج5، ص357/ تهذيب الأحكام، ج7، ص297/ الإستبصار، ج3، ص178/ وسايل 

الشيعة، ج20، ص534/ بحارالأنوار، ج2، ص278/ نورالثقلين/ البرهان - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص626


                         (4)


أمير المؤمنين (عليه السلام)- عَنْ أَمِيرِالْمُؤْمِنِينَ (عليه السلام) فِي قَوْلِهِ تَعَالَى: وَ لا تَنْكِحُوا الْمُشْرِكاتِ حَتَّي يُؤْمِنَّ وَ لَأَمَةٌ مُؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكَةٍ وَ لَوْ أَعْجَبَتْكُمْ وَ لا تُنْكِحُوا الْمُشْرِكِينَ حَتَّي يُؤْمِنُوا وَ لَعَبْدٌ مُؤْمِنٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكٍ وَ لَوْ أَعْجَبَكُمْ وَ ذَلِكَ أَنَّ الْمُسْلِمِينَ كَانُوا يَنْكِحُونَ فِي أَهْلِ الْكِتَابِ مِنَ الْيَهُودِ وَ النَّصَارَي وَ يُنْكِحُونَهُمْ حَتَّي نَزَلَتِ الْآيَةُ نَهَي أَنْ يَنْكِحَ الْمُسْلِمُ مِنَ الْمُشْرِكِ أَوْ يُنْكِحُونَهُ ثُمَّ قَالَ تَعَالَى فِي سُورَةِ الْمَائِدَةِ مَا نَسَخَ هَذِهِ الْآيَةَ فَقَالَ: وَ طَعامُ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتابَ حِلٌّ لَكُمْ وَ طَعامُكُمْ حِلٌّ لَهُمْ وَ الْمُحْصَناتُ مِنَ الْمُؤْمِناتِ وَ الْمُحْصَناتُ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتابَ مِنْ قَبْلِكُمْ فَأَطْلَقَ عَزَّ وَجَلَّ مُنَاكَحَتَهُنَّ بَعْدَ أَنْ كَانَ نَهَي وَ تَرَكَ قَوْلَهُ: وَ لا تُنْكِحُوا الْمُشْرِكِينَ حَتَّي يُؤْمِنُوا عَلَى حَالَةٍ لَمْ يَنْسَخْهُ.


Daga Imam Ali (A. S) game da fadinSa madaukaki :


" KUMA KADA KU AURI MUSHRIKA HAR SAI TA YI IMANI, BAIWA MUMINA TA FI ALKHAIRI DAGA MUSHRIKA KO DA KUWA TA BA KU SHA'AWA. KUMA KADA KU AURI MUSHRIKI HAR SAI YAYI IMANI, BAWA MUMINI YA FI ALKHAIRI DAGA MUSHRIKI KO DA KUWA YA BA KU SHA'AWA. " To, kamar hakane lalle musulmai sun kasance suna yin aure cikin Ahlul-Kitaab daga Yahudawa da Nasara, kuma su ma suna aurensu har sai da aya ta sauko wacce ke hani game da musulmi ya auri mushriki, ko ya aurar masa. Sa'an nan Allah (T) ya fada cikin Suratul-Ma'idah wacce ta soke wannan aya, Yace :


" KUMA ABINCIN WADANDA AKA BAWA LITTAFI HALAS NE GARE KU, KUMA ABINCINKU HALAS NE GARE SU.  DA KUMA KATANGAGGIYA DAGA MUMINA , DA KUMA KATANGAGGIYA DAGA WADANDA AKA BAWA LITTAFI DAGA GABANINKU."


Sai Allah mai girma da daukaka ya halatta auratayyarsu bayan yayi hani (da farko),  kuma yabar fadinSa :


" KUMA KADA KU AURI MUSHRIKI HAR SAI YAYI IMANI. " Akan wannan hali bai soke shi ba. "


المصدر :  بحارالأنوار، ج100، ص379/ بحارالأنوار، ج90، ص27/ وسائل الشيعةًْ، ج20، ص538 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص628


Bisa wadannan riwayoyi za mu fahinci cewa abincin da aka halasta mana na Ahlul-Kitaab shine abinda ya shafi kalar da ba a fadawa (cooking) ko kuma nace wadanda basu shafi yanka ba. Idan kuma ya zama an dafa din ma matuqar ba abinda ake yankawa bane babu laifi, halascin na nan. 


Batun auratayya kuma sharadi ne dole ya zama anyi shi tsakanin wadanda ba mushirikai bane, idan aka sami wani bangare ya zama mushriki, to, aure ya haramta a taakaninsu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


23rd November, 2022/  29th Rabi'us-Sani, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post