“Shima Tafin Hannun Ba'ace Kaje Ka Mishi Wani Ado! Ba, Abin Da Ace An Yarda Dashi Shine Kawai Zobe”_Umma Zeenat Ibraheem Zakzaky (h)
~Umma Zeena Ibraheem Zakzaky [H].


“Batun kace ma mak'na,a hijabi yaren wa'yanda basu san ma meye hijabi ne ba. Hijabi ba yana nufin wani ‘style’ ne na musamman za kayi ba. A,a' abin da duk ze rufe adon ka tun daga kai har zuwa tafin ƙafan ka Shine hijabi, ya bar maka tafin hannu kawai da kuma fuska, shima tafin hannun ba'ace ka mishi wani ado! Ba, abin da kawai ace an yarda shine zobe.”


“Kuma in kayi lalli kaje ka zana ‘flowers’ a hannun ka, kayi ta zana ‘flowers’ masu ban sha'awa wanda ko mace ne 'yar uwar ki ta gani ze bata sha'awa to wannan ma kin rusa Hijabin ki. Amma idan ya zama lalle kuma na (Adi), wanda aka saba a zungure hannu gaba ɗaya ya zama yatsa akwai lalle amma ba wanda aka yima ado! A kayi ’Flowers’ ba, wannan an yarda.”


"Dan ance akwai mata da suka zo wajan Manzon Allah (S), za suyi bai'a (Ze karɓi mubaya'ar su), da yake ta labule ne suke yi. Se suka tura hannun su se yace “Wannan hannun na mace ne ko namiji?” Se suka ce “Hannun mace ne.” Se yace “In na mace ne ai da za kiyi ƙunshi akai.” Daga nan ne a fahimci ƙunshi (Adi), wanda ake yi wanda kawai za aga hannun mace gabaɗaya an zungura shi inma ya fara fita zaka gani a yatsa, wannan ba komai.”


Zanci Gaba In Sha Allah


✍️Ibraheem Y. Ibraheem

    —22 November, 2022


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Masha allah muna fatan allah ya ganar da al-umma

    ReplyDelete
  2. Wane ra'ayi za'a bayyana birbishin ra'ayin Shai'ar Musulunci?

    ReplyDelete
Previous Post Next Post