NI BAN YARDA TSARO NE MATSALAR KASAR NAN BA Inji Sheikh Zakzaky [H]



 Ni ban yarda cewa tsaro ne matsalar mu a kasar nan ban Abinda ke damun mu a kasar nan, ainihin rashin asasin da Muka doru a kaine da rashin sanin Ina muka dosa. Shi rashin tsaron nan , su mahukuntan suke haddasawa. Ba wani Wanda ya kawo rashin tsaro a kasar nan, in banda su. Ma'ana wato shi rashin tsaron makamin siyasa ne. Don zamu ga cewa; ainihin ma an zabi a ina ne za'a samar da tsaro din, Ina ne Kuma (su wa za'a tsoratar). Alal misali munga da gangan an zabi cewa da arewacin kasar nan za'a yi , Kuma ma da musulmi. Kuma idan ka duba za ka ga matsaloli suna nan a ko'ina a kasar nan. Amma kuma mun tabbatar da cewa; matsalolin da suke jingina ma arewacin kasar nan, ala'amarin ba haka ba ne. Don mun San Lallai in ana batun tarbiyya ne , mu mun fi su ma tarbiyya, Amma sai su kawo rashin da'a ya fi yawa a wurinmu. Saboda haka , ka ga ya Zama abin, makamin siyasa ne , ya zama wasa ne 'yan siyasa suke yi da rayuka da dukiyoyin mutane. Na ciro wannan jawabin Daga Littafin Zantuka 40 na sheikh Zakzaky (H) Bin Muhammad 2022-11-03 KD

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post