Idan muka ce Jagora, muna nufin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

 


Jagora (H


Idan muka ce Jagora, muna nufin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

A wajenmu, shine sanadin shiriyarmu, ba don muna ganin wadanda ba mu ba a matsayin batattu, sai don daga abin da muka fahimta bayan amsa Da'awarsa shine, ba don shi ba, da ba mu riski alkairai masu yawa na duniya da lahira ba.


Sanadinsa muka san Allah da yadda za mu bauta masa, muka san Manzon Allah (S) da irin yadda ake sallama masa, muka san A'immatu Ahlulbaiti (AS) da wajabcin riko da su a bayan Annabi (S).


Jagora na nufin Jagoran Gwagwarmayar yunkurin kawar da tsarin Kafirci wacce Bature ya dankara mana, da dawo da ikon addinin Musulunci a doron kasa ta yadda adalci da walwala zai shimfidu a doron ƙasa.


Malami ne da dukkan ma'anar Malunta. Idan ka dauka Haddar Alkur’ani ne Malunta, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) mahaddacin Alkur’ani ne. Idan sanin Luggar Larabci ko sanin Fiqihu ko Aqida ko Tafsiri duk Shaikh Zakzaky Malami ne a bangarorin. Idan bangaren ilimin da ake cewa Boko ko na zamani ne, nan ma masani ne a bangaren.


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi karatun littafan addini daban-daban a wajen malamai daban-daban na Shi'a da Sunnah sama da 20 a ƙasar nan da wajenta tun shekarun yarinta har zuwa tsufa. Wanda InshaAllah zan kawo sunayensu wani lokaci.


Shaikh Zakzaky (H) masoyin Manzon Allah (S) ne, don haka ma a rayuwarsa tabbataccen abu ne ya je Makkah da Madina ya ziyarci Makwancin Manzon Allah (S) sau 20. Cikinsu Shaikh Zakzaky ya je aikin Hajji sau 8, ya yi Umra sau 4 (a wasu watanni), sannan ya yi kwanaki 30 din Ramadan din shekaru 8 a tsakanin Haramin Allah Ta'ala da na Annabi (S).


Ya ziyarci duk A'immatu Ahlulbaiti (AS) a makwantansu a Madina, Iraq da Iran, ba sau daya ko biyu ba, yana mai sanin hakkinsu, da sallamawa shugabancinsu.


Shaikh Zakzaky daga abin da muka iya tabbatarwa shine kusan fiye da rabin ranekun shekararsa yana azumtarsu ne. Domin tun yana matashi har tsufansa, har yanzu haka ya kan azumci watanni Rajab, Sha'aban da Ramadan a jere, sannan yana azumtar Litini da Alhamis duk mako, sannan duk wata rana mai falala ko da aka ruwaito ana azumta wanda suna nan da yawa in har Shaikh Zakzaky na halin lafiya yana azumta.


Sallah? Wallahi ban taba ganin wanda ya iya Sallah kamar Sayyid Zakzaky (H) ba. Idan yana janka Sallah, albakarcinsa sai ka rika jin wani kushu'i na musamman, tun ba in aka yi Sujada ba. Alhamdulillahi, na yi Salla a bayansa Farillai 6 bayan fitowarsa daga kurkukun nan, a tsawon lokacin nan ba a samu wani abu da ya faranta zuciyata sama da wannan ba, saboda daɗin da na ji a cikin hakan.


Kuma duk wanda ya san Shaikh Zakzaky, a makaranta ne tun ana Jami'a, ko a waje ne, ko a gida, ko a hanyar tafiya-tafiye, yana ba da shaidar cewa Shaikh Zakzaky mai tsai da Sallah ne, mai kiyaye sallolin dare da rana na nafilfilu ne. Har ya zama ya sha fadan cewa bai san abin da ya kai Sallah dadi a rayuwa ba.


Jagoranmu mai kyauta ne, duk danginsa sun masa shaidar sa da zumunci da kyauta. Haka makwafta da al'umma, bare kuma 'yan uwa almajiransa wadanda za su baka labarin yana wahala su gana shi bai musu wata kyauta ba, musamman ga masu tafiya ziyara, karatu ko yan uwa mata da kullum yake karfafa su a kan tsayuwa da sana'a da dogaro da kai.


Dogaronsa ga Allah a zahiri yake, kullum Allah ne a bakinsa da zuciyarsa da aikinsa. Yana da tsananin Yakini da Allah a kan duk al'amarinsa, wannan yasa Allah Ta'ala bai taba kyale shi da kansa ba a kowane hali. Shi kuma Shaikh Zakzaky bai taba fariya da jin kansa a matsayin wani abu ba, illa bawan Allah, ya kan ga duk wata baiwa ko nasara da ke tare da shi a matsayin yin Allah ne. Wannan shine tushen nasararsa a ko yaushe.


Na godewa Allah da Ya sa mutum mai irin wannan nagartan ne Jagora na, a irin wannan duniyar da ke cike da rikici da rikitattu, mutane mafi yawa suka zama yan ɓaganniya ba su san makama ba bare tabbas.


Madalla da Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).🥰🌹


Kuma Jagora addu'a ❤️


— Saifullahi M Kabir

21/09/2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post