KOMI GIRMAN AYATOLLAH BAI ISA YA BADA IZININ AI JIHADI (ZUBDA JINI) BA — sheikh ibraheem zakzaky (H)

 


Daga ibraheem S.F. Yankara

" ....To izinin ai jihadi fa ? A daga makami ai yaki fa ?  Wa zai bada wannan izinin ? To ko ayatollah bai isaba, ko ayatullahi UZUMAH komin girman ayatullahi bai isa ya bada izinin ai jihadiba ,  Duk duniyar nan ba wanda ya isa ya bada izinin ai jihadi"

Sheikh zakzaky yaci gaba da cewa : "mutum daya 1 rak!! Yake iya bada izinin ai jihadi, shine IMAM MAHADEY (A.T.F) kuma bazai yiwu wani yace mana yaga mahadi da kansa yace mana ai jihadi, bazai yuwuba, sai in yazo da kansa (imam) , sabo da haka izinin yaki, IFTIDA'AN sai imam mahadi inyabayyana,  wannan maganar da nake fadi , ba sabanin ra'ayi tsakanin wani ayatullah da wani ayatullah duk duniyar shi'ah,  ba sabanin ra'ayi, "

" amma yaki da unwanin kare kai wannan lazim ne,  kamar wani ya kawo maku hari ku kare kanku, koba'a luraba?, kare kai wajibine to amma idan kai-kai! Musamman kashirya ka tafi jihadi sai da izinin imam mahadi kuma sai inya bayyana ,  to amma wannan koyarwar ahlul baiti ce , "

Shehin malamin yaci gaba dacewa "Amma koyarwar ama,  su sai wani ya bushi iska kawai yabada izini,  ya halasta zubda jini , kawai mutum yabushi iska yace ai jininsa ya halasta, tamaman kamar yadda yan kora wiwi suke halasta jini,   banga banbancin mai cewa jinin wani ya halasta da dan wiwi ba, tunda yadda dan wiwi zai kora wiwinsa ya fadi wata magana ba hankali haka shima ya fada,  dun ba a addini ya ganiba ba'a addini ya samuba, ara'ayin kashin kasane "

" Na'am! Yana iya daukar usuwa daga batattun malamansu na da , wanda suma suke halasta jini ,  sukai hari su samu kudi , su karkashe mutane, suce sun dibi ganima , amma bada koyar war annabi ba , bada koyarwar kuma magadan annabi ba, wanda kebin mazahabar magajin annabi to lallai bazai taba halasta akai hari akan wabiba da sunan ana jihadi".

Shehin malamin ya bayyana hakan ne a yayin karatun littafin nahajul Balaga zama na 0096. Ibraheem sani fudiyyah yankara Ya Rubuto maku daga Audio din jawabin.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post