Zalincin Da Aka Yiwa Sheikh Zakzaky Yasa Na Fahimci Da'awarsa.– Sheikh Iliyasu Isah Bouza.

 


Daga, Bilal Nasir Umar Sakkwato.


Wani Malamin darika ya karbi kiran Sheikh Zakzaky a Jamhuriyar Nijar, Malamin mai suna Iliyasu Isah Bouza Hayi, ya mika mubayi'arsa ga jagoran harkar musulunci a wannan nahiya Allama Sheikh Ibrahim Yaqoub Alzakzaky, a gurin taron makon hadinkai wanda almajiran Sheikh Zakzaky suka shirya a bara1443.


A lokacin da yake gabatar da jawabi kan makasudin abinda ya janyo ra'ayinsa har ya fahimci wannan kira, Malam Iliyasu ya bayyana irin zalincin da ake yiwa Sheikh Zakzaky ne ya sanya shi tsunduma a cikin bincike, da kuma irin wannan taron da aka yi bara har aka gayyacesu.


Haka kuma Malamin ya bayyana irin kalubalen da suka fara fuskanta daga gurin 'yan uwansa Malamai tun bayan da aka sami labarin ya halarci taron makon hadinkai na yan Shi'a a bara.


Da yake bayani dangane da fahimtarsa ga Sheikh Zakzaky Malam Iliyasu ya bayyana cewa, “Ni a tawa fahimta wanan bawan Allah Sheikh Zakzaky sirri ne na Allah T, domin ba wani dan'adam da za'a harbawa bullets a cikin kwakwalwa kuma ya rayu, wannan bawan Allah sirri ne na Allah wanda ya adana a jikinsa.”


A karshe kuma Malamin ya yi kira ga saura al'ummar musulmi da su zo suma su marawa wannan tafiya ta Sheikh Zakzaky baya a kokarinsa na ganin ya kawar da zalinci tare da tabbatar da adalci a wannan nahiya tamu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post