In Don Allahu Ta'ala Mukeyi Mu Tsayu Ƙyam. Akwai Gwagwgwa Ɓan Sakamako Ranar Gobe Ƙiyama




Ako wani irin aiki kake yi akwai na sama dakai, kuma akwai na ƙasa dakai, shima na sama daikai ɗin akwai na sama dashi, shima na ƙasa dakai ɗin akwai na ƙasa dashi. Kuma duka zaka ga an haɗu ne akan wani hadafi kwara ɗaya tak. Ma'aikata ne "Its mean Company" Makaran tune, Banki ne, wajan kasuwanci ne, wajan sana,o'i ne, Asibiti ne. Dadai sauransu, dukkan su suna aiwatar da aiki ne domin manufa kwara ɗaya rak. (Manufar) kuwa itace wannan wajan da suke gudanar da ayyukan su yaci gaba fiye da tunanin mutane. Mu ɗauki makaranta. Shine mataki na farko da mutum zai shiga domin gina rayuwar sa, kona ƴaƴan sa akan cimma wani hadafi na rayuwa.


Domin zuwa makaranta ne ɗan adam yake zama cikakken mutun mai hankali da tunani. Hakan bawai zai samu bane kwai, dole sai malaman da suke wannan Makaran sun koyar dakai Sannan a fara tunani zaka iya zama kamilin mutum mai hankali domin (Hankali) shine mutum. In muyu duba da haka zamuga cewa a rayuwa malami ba ƙaramin abin girmamawa bane domin ko wani mutum da yayi wani "Achiever" na rayuwar sa, hakan ya samu ne saboda malami ya koyar dashi koda kuwa ya samu dacen gidan ƙarshe gidan da kowa yake fatan samun sa Aljanna dole da gudummuwar malami a ciki.


Malami yana fuskantar wani ƙalu bale da ba ko wani ma'aikaci ne yake fuskarta ta, musamman a lokacin da yake tsakanin buƙata ko ya dogara ne da koyarwar bisa sadakan da ake bashi wato "Salary". Ako wace "School" Islamiyya ne, ko boko ne, bance da matakin gaba da "Secondary" ba. Mallakin wata haƙida ne, ko wani mutum daban. Akan assasa masu lura da shige da ficen Makaran tar wato "management" ta hanyar sune sadakan da ake biyan malamai ze fito. Da duk wani "Promotion" da  "School" Take samu. Abin bacin ran wani malamin saiya koyar kusan "Six months or three months without Salary's, The most happen this in islam School". Ba'a sauke haƙƙin malaman islamiyya kamar yadda ake sauke haƙƙin malaman da suke koyarwa a makarantu boko. 


Anfi ba karatun boko muhimmanci fiye da wuce ƙima amma duk wanda a bashi Hankali an gama masa komai, Allah yana da hujja akan mu. Abin da nakeson na ƙarƙare dashi idan kana koyarwa a Islamiyya koda kuwa turanci da lissafi da hausa kake koyar dasu, kayi tsakanin ka da Allah. Daga cikin ayyukan da basa gushewa bayan mutuwa akwai koyar da ilimi wanda ze amfanar da al'umma. Ka zama mai amfanar al'umma musamman yara masu tasowa, hakan zai zamto ado! a gareka har gobe ƙiyama, kaidai kawai kayi don Allah komai yana da lokaci. Na sama da ƙasa masu aiki a ɓangarorin ma'aikatu Allah yaba kowa ikon sauƙe haƙin daya rataya wuyansa. Allah ya ƙara ƙimsa basira cikin zuƙatan malaman mu na islamiyya.


#AyiKomaiDonAllah

© Ibraheem Y. Ibraheem

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post