Buri da Fatan Mlm Zakzaky (h) Shi ne Kowa Ya Tsira a Duniya Da Lahira...!!!... Umar Hassan Gololo... 

Ka koma can baya ka nemi jawaban Malam Zakzaky(H) na cassettes din Tape recorder, ka nemi jawabansa wadanda ALMIZAN take rubutawa a shafinta na Tunatarwa, ka nemi jawabansa wadanda suke taskace a CD, DVD da memory hade da wadanda suke cikin tsaffin mujallun Mujahida, Gwagwarmaya, The Struggle da litattafan da cibiyar wallafa take taskacewa. 

Ka yi kokarin samun tafsirai, Nahjul-Balagha da jawabansa na wasu programs ka samu wuri ka rinka sauraro daya bayan daya kana karantawa. 

Idan suka zama abokan hirarka anan zaka sani tare da fahimtar hakikanin abinda Malam Zakzaky(H) yake kira akai, shin Duniya ne ko Lahira? 

Kana tsammanin Malam Zakzaky(H) zai sadaukar da lokacinsa, karatunsa, jininsa, jinin 'ya'yansa da Almajiransa domin ya samu shiga da karbuwa a wurin azzalumai?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post