Wasu falaloli da tagomashi ga ma'abicin yin Istigfari !


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MAI YAWAITA YIN ISTIGFARI BA ZAI HADU DA ALLAH CIKIN ZUNUBI BA

Yin istigfari ba wai dole sai mutum ya san ya aikata zunubi ne zai yi shi ba, domin zai iya aikatawa ba tare da ma ya sani ba. Annabi (S.A.W.W) bai taba aikata zunubi ba amma ya kasance yana yawaita yin istigfari kuma yana umartarmu da mu riqa yi.

Ko da ba zunubi ka nemi gafarar Ubangiji girmamawa ce gare shi, kamar ace ka sami mahaifiyarka kace ta riqa haquri dakai komai kyautatawarka gare ta.

Ayoyi da yawa sunyi magana game da yin istigfari kamar yadda za mu bada misali anan qasa kamar haka

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

الآيات النساء- " وَ لَوْ أَنَّهُمْ إِذْ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ جاؤُكَ فَاسْتَغْفَرُوا اللَّهَ وَ اسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللَّهَ تَوَّاباً رَحِيماً "[1] و قال

" DA DAI ACE SU YAYIN DA SUKA ZALUNCI KANSU SUNZO MAKA SON NEMI GAFARAR ALLAH KUMA MANZO YA NEMA MUSU GAFARA, TO, DA SUN SAMI ALLAH MAI KARBAR TUBA MAI JIN QAI."

النساء - " وَ اسْتَغْفِرِ اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ كانَ غَفُوراً رَحِيماً "[2] و قال

" KU NEMI GAFARAR ALLAH, LALLE ALLAH YA KASANCE MAI GAFARA MAI JIN QAI."

 النساء - " وَ مَنْ يَعْمَلْ سُوءاً أَوْ يَظْلِمْ نَفْسَهُ ثُمَّ يَسْتَغْفِرِ اللَّهَ يَجِدِ اللَّهَ غَفُوراً رَحِيماً " [3] 

" DUK WANDA YA AIKATA MUMMUNA KO KUMA YA ZALUNCI KANSA SANNAN YA NEMI GAFARAR ALLAH, TO, ZAI SAMI ALLAH MAI GAFARA MAI JIN QAI ."

الأنفال‏ - " وَ ما كانَ اللَّهُ مُعَذِّبَهُمْ وَ هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ‏ "[4]


" ALLAH BAI KASANCE MAI YI MUSU AZABA BA MATUQAR SUNA ISTIGFARI."

هود - " وَ أَنِ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ يُمَتِّعْكُمْ مَتاعاً حَسَناً إِلى‏ أَجَلٍ مُسَمًّى وَ يُؤْتِ كُلَّ ذِي فَضْلٍ فَضْلَهُ‏ " [5] 

" KUMA KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU SANNAN KU TUBA GARE SHI, ZAI JIYAR DAKU DADI DA ABUBUWA KYAWAWA ZUWA WANI LOKACI AMBATACCE, KUMA YA BAIWA KOWANNE ABOCIN FALALA FALALARSA."

و قال تعالى حاكيا عن هود - " وَ يا قَوْمِ اسْتَغْفِرُوا رَبَّكُمْ ثُمَّ 

تُوبُوا إِلَيْهِ يُرْسِلِ السَّماءَ عَلَيْكُمْ مِدْراراً وَ يَزِدْكُمْ قُوَّةً إِلى‏ قُوَّتِكُمْ وَ لا تَتَوَلَّوْا مُجْرِمِينَ‏ "[6] 

Allah na yin hikaya game da Hud (A.S)

" KUMA YAA KU MUTANENE ! KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU SA'AN NAN KU TUBA GARE SHI, ZAI SAUKAR DA RUWA DAGA SAMA, KUMA YA QARA MUKU WANI QARFI ZUWA QARFINKU, KUMA KADA KU JUYA KUNA MASU KANGAREWA."

و قال تعالى حاكيا عن صالح‏ فَاسْتَغْفِرُوهُ ثُمَّ تُوبُوا إِلَيْهِ 

إِنَّ رَبِّي قَرِيبٌ‏ مُجِيبٌ‏."

Hikaya ga Salihu (A.S)

" KU NEMI GAFARARSA SA'AN NAN KU TUBA GARE SHI, LALLE UBANGIJINA MAKUSANCI NE MAI AMSA ADDU'AH."

(1) النساء: 64.

(2) النساء 106.

(3) النساء: 110.

(4) الأنفال: 33.

(5) هود: 3.

(6) هود: 52.

Duk wannan umarni na Allah (T) wanda sakamakon abin zai dawo zuwa gare mu ne, amma kuma muna qin bin wannan umarni.

Kamar mutum ne yace kazo ka karbi kudi a gunsa amma kaqi zuwa. Ko da shike in kudi aka ce kazo ka karba za ta tattara komai naka a gefe kaje don amsar wannan kudi, amma neman gafarar Ubangiji ce abin gujewa.

A kawo wasu riwayoyi cikin hadisai kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

الخصال عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ ع قَالَ: مَنْ قَالَ أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ وَ أَتُوبُ إِلَيْهِ فَلَيْسَ بِمُسْتَكْبِرٍ وَ لَا جَبَّارٍ إِنَّ الْمُسْتَكْبِرَ مَنْ يُصِرُّ عَلَى الذَّنْبِ الَّذِي قَدْ غَلَبَهُ هَوَاهُ فِيهِ وَ آثَرَ دُنْيَاهُ عَلَى آخِرَتِهِ‏ ."

Ya zo cikin Kisal daga Aliyu Bn Hussaini (A.S) yace: " DUK WANDA YACE; ASTAGFIRULLAHA WA A TUUBU ILAIHI ." TO, BAI KASANCE MAI GIRMAN KAI BA, KUMA BA MAI TSAURIN KAI BANE. LALLE SHI MAI GIRMAN KAI SHINE WANDA KE CIGABA AKAN (aikata) ZUNUBI WANDA ZUCIYARSA TA RINJAYE SHI CIKINSA, KUMA YA FIFITA DUNIYARSA AKAN LAHIRARSA."

الخصال ج 1 ص 143

Riwaya ta gaba kuma wacce tazo cikin SAWABUL-A'AMAAL tana cewa;

ثواب الأعمال أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ الْحَسَنِ بْنِ عَلِيٍّ عَنْ عُبَيْسِ بْنِ هِشَامٍ عَنْ سَلَّامٍ الْخَيَّاطِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: مَنْ قَالَ أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ مِائَةَ مَرَّةٍ حِينَ يَنَامُ بَاتَ وَ قَدْ تَحَاتَّ الذُّنُوبُ كُلُّهَا عَنْهُ كَمَا تَتَحَاتُّ الْوَرَقُ مِنَ الشَّجَرِ وَ يُصْبِحُ وَ لَيْسَ عَلَيْهِ ذَنْبٌ‏."

Daga Sa'idu daga Hassan Bn Aliyu , daga Ubaisi Bn Hishaam, daga Sallaamil-Khayyadi, daga Abu Abdullah (A.S) yace:

" Duk wanda yace; " ASTAGFIRULLAHA." Sau dari yayin da ya kwanta bacci (da daddare) zai wayi gari zunubansa sun karkade dukka kamar yadda ganyaye (leaves) ke zubewa daga kan bishiya, kuma zai wayi gari babu zunubi a kansa ."

ثواب الأعمال: ص 149.

Cikin hadisi na farko ana nuna mana ne fa cewa, girman kai da tsaurin kai shi ke hana mutum ya tuba ga Allah ko ga wanda yasan ya bata masa.

Cikin riwaya ta biyu kuma yana karantar damu ne cewa shi yawan aikata tuba (ISTIGFAARI) na kakkabe zunuban da mutum ya aikata ne kamar yadda ganyayyaki daga kanta ke zuba.

YAA ALLAH KA SANYA MU CIKIN MASU YAWAN TUBA ZUWA GARE KA

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda

15th December, 2021/ 10th Jimada-Ulah, 1443.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post