Dalilan da yasa Abu Huraira yafi kowa yawan hadisai 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YA KAWO HUJJOJI MASU CIN KARO DA JUNA

Cikin wani rubutuna na baya na karo hujjar da tasa Abu Huraira yafi kowa yawan hadisai kamar yadda ya fada da bakinsa, sai dai kuma daga baya naci karo da wata maganar tasa wacce bayaninsa ya qaryata kansa da kansa.

'Daya riwayar ya fadi dalilansa ne na yawan hadisansa saboda har ma mutane na zargin cewa shi yafi kowa yawan hadisai cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W.W). Sai kuma ya kawo wata maganar dake nuna cewa akwai wanda ya fi shi yawan hadisai.

Ga riwayoyin nan kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(7354)- حدثنا علي: حدثنا سفيان: حدثني الزُهري: أنه سمعه من الأعرج يقول: أخبرني أبو هريرة قال: إنكم تزعمون أن أبا هريرة يكثر الحديث على رسول الله صلى الله عليه وسلم، والله الموعد، إني كنت امرأ مسكيناً، ألزم رسول الله صلى الله عليه وسلم على ملء بطني، وكان المهاجرون يشغلهم الصفق بالأسواق، وكانت الأنصار يشغلهم القيام على أموالهم، فشهدت من رسول الله صلى الله عليه وسلم ذات يوم، وقال: (من يبسط رداءه حتى أقضي مقالتي، ثم يقبضه، فلن ينسى شيئاً سمعه مني? )

Bukhari yace: Aliyu ya bamu labari, Sufyan ya bamu labari, Zuhriy ya bani labari cewa yaji daga A'araaj yana cewa: Abu Huraira ya bani labari yace:

" Lalle ku kuna riyawa cewa Abu Huraira yafi kowa riwaito hadisai daga Manzon Allah (S.A.W.W), to, Allah shaida ne. Ni dai na kasance mutum ne miskini, kuma ina lazimtar Manzon Allah (S.A.W.W) cikina babu komai (ko abinci ban ci ba), su kuma Muhajirai sammakonsu zuwa kasuwa na shagaltar dasu, su kuwa Ansar tsayuwa kan dukiyarsu ne ke shagaltar dasu.

Sai wata rana naje wajen Manzon Allah (S.A.W.W), sai yace:

" WANENE ZAI SHIMFIDA MAYAFINSA HAR NA QARE MAGANATA SANNAN YA NADE SHI, BA ZAI TABA MANTA ABINDA YAJI DAGA GARE NI BA?"

 Sai na shimfida rigar dake jikina. Na rantse da wanda aka aiko da gaskiya, ban mance wani abu da naji daga gare shi ba."

(Sahihul-Bukhari, Littafin yin riqo da littafi da sunnah, hadisi mai lamba 7354)

Abinda Abu Huraira ke tabbatarwa anan shine, da gaske yafi kowa yawan hadisai saboda shi yafi kowa kasancewa tare da Annabi (S.A.W.W), kuma ya sami albarkarsa domin ya shimfida rigarsa ya tattara maganar Annabi (S.A.W.W), kuma ya sami alqawarinsa cewa ba zai taba mance abinda yaji daga gare shi ba.

Sai dai kuma cikin wata riwaya ya nuna cewa akwai wanda ya fi shi yawan hadisai saboda wani dalili. Ga riwayar kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(113)- حدثنا علي بن عبد الله قال: حدثنا سفيان قال: حدثنا عمرو قال: أخبرني وهب بن منبه، عن أخيه قال: سمعت أبا هريرة يقول: ما من أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم أحد أكثر حديثا عنه مني، إلا ما كان من عبد الله بن عمرو، فإنه كان يكتب ولا أكتب تابعه معمر، عن همام، عن أبي هريرة."

Aliyu Bn Abdullahi ya bamu labari yace: Sufyan ya bamu labari yace: Wahbu Bn Munbihi ya bani labari daga dan'uwansa yace: Naji Abu Hurairata yana cewa:

" Babu wani daga cikin Sahabban Annabi (S.A.W.W) wanda ya fini yawan hadisai sai dai abinda ke wajen Abdullahi Bn Amruu, domin shi ya kasance yana rubuta (abinda yaji) ni kuma bana rubutawa."

(Sahihul-Bukhari, Kitabul-ilmi, babin rubuta ilmi, hadisi mai lamba 113)

                NAZARI

Cikin wannan riwaya ta biyu Abu Huraira ya kawo cewa Abdullahi Bn Amruu ya fi shi yawan hadisai saboda shi yana rubuta abinda yaji daga Annabi (S.A.W.W), shi kuma ba ya rubuta abinda yaji.

Wannan maganar tasa kuwa tana nuni ne kan cewa matuqar mutum zai riqa rubuta abinda yaji, to, zai fi kiyaye magana fiye da wanda ji kawai yake yi ba ya rubutawa.

Idan kuwa hakane, to, menene matsayin maganarsa ta cewa wai Annabi yace duk wanda ya shimfida mayafinsa har ya qare maganar da yake yi ba zai mance abinda yaji daga gare shi ba?

Sai kuma shi yace Abdullahi ya fi shi yawan hadisai ne saboda shi yana rubuta abinda yaji.

To, wannene gaskiya cikin wadannan riwayoyi biyu wadanda suka zo cikin Bukhari daga bakin Abu Hurairata ?

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        (08137925034)

14th December, 2021/ 9th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post