Hukuncin Shan Giya A Muslunci


 @ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BAYAN HADDIN FARKO HUKUNCIN KISA KAN HAU KAN MASHAYIN GIYA

Ita Giya haramun ne shanta, kuma ita ce uwar dukkan wani aiki na laifi, domin in an sha ta za ta iya haifar da aikata kowanne irin aiki na sabo. Saboda haka ake yin bulala ga wanda yasha, idan ya maimaita kuma a kashe shi don gudun yawaita fasadi a doron qasa.

Sai dai kuma dole ayi karatu don gudun haduwa da masu kawo shubuha don hana zartar da hukuncin kamar yadda ya faru a tarihin magabata.

Bari muyi amfani da riwayoyi uku kan wannan mas'ala don sanin haqiqanin hukuncin shanta da kuma shubuhar da za a iya kawowa.

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

(1)- الأمالي للشيخ الطوسي عَنِ ابْنِ مَخْلَدٍ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ نُصَيْرٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ إِبْرَاهِيمَ بْنِ زِيَادٍ عَنْ سَهْلِ بْنِ زَنْجَلَةَ عَنِ الصَّبَّاحِ بْنِ مُحَارِبٍ عَنْ دَاوُدَ الْأَوْدِيِّ عَنْ سِمَاكٍ عَنْ خَالِدِ بْنِ جَرِيرٍ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ إِذَا شَرِبَ الْخَمْرَ فَاجْلِدُوهُ وَ إِنْ عَادَ فَاقْتُلُوهُ‏.

Ya zo cikin Amali na Sheikh 'Dusi daga Ibn Mukhladi, daga Ja'afar Bn Muhammad Bn Nadjrin, daga Muhammad Bn Ibrahim Bn Ziyaadin, daga Sahl Bn Zanjalata, daga Sabbaahi Bn Muhaaribi, daga Dawuda Al-Audiyyi, daga Simaak daga Khaalid Bn Jareer yace: Manzon Allah (S.A.W.W) yace;

" IDAN (mutum) YA SHA GIYA KUYI MASA BULALA, IDAN KUMA YA MAIMAITA KU KASHE SHI !"

أمالي الطوسيّ ج 2 ص 8.

(2)- الإرشاد جَاءَ مِنْ طَرِيقِ الْعَامَّةِ وَ الْخَاصَّةِ أَنَّ قُدَامَةَ بْنَ مَظْعُونٍ شَرِبَ الْخَمْرَ فَأَرَادَ عُمَرُ أَنْ يَحُدَّهُ فَقَالَ لَهُ قُدَامَةُ لَا يَجِبُ عَلَيَّ الْحَدُّ لِأَنَّ اللَّهَ تَعَالَى يَقُولُ‏ لَيْسَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَ عَمِلُوا الصَّالِحاتِ جُناحٌ فِيما طَعِمُوا إِذا مَا اتَّقَوْا وَ آمَنُوا وَ عَمِلُوا الصَّالِحاتِ‏[25] فَدَرَأَ عُمَرُ عَنْهُ الْحَدَّ فَبَلَغَ ذَلِكَ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ ع فَمَشَى إِلَى عُمَرَ فَقَالَ لَهُ لِمَ تَرَكْتَ إِقَامَةَ الْحَدِّ عَلَى قُدَامَةَ فِي شُرْبِ الْخَمْرِ فَقَالَ إِنَّهُ تَلَا عَلَيَّ الْآيَةَ وَ تَلَاهَا عُمَرُ فَقَالَ لَهُ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع لَيْسَ قُدَامَةُ مِنْ أَهْلِ هَذِهِ الْآيَةِ وَ لَا مَنْ سَلَكَ سَبِيلَهُ فِي ارْتِكَابِ مَ حَرَّمَ اللَّهُ إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَ عَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَا يَسْتَحِلُّونَ حَرَاماً فَارْدُدْ قُدَامَةَ وَ اسْتَتِبْهُ مِمَّا قَالَ فَإِنْ تَابَ فَأَقِمْ عَلَيْهِ الْحَدَّ وَ إِنْ لَمْ يَتُبْ فَاقْتُلْهُ فَقَدْ خَرَجَ عَنِ الْمِلَّةِ فَاسْتَيْقَظَ عُمَرُ لِذَلِكَ وَ عَرَّفَ قُدَامَةَ الْخَبَرَ فَأَظْهَرَ التَّوْبَةَ وَ الْإِقْلَاعَ فَأَدْرَأَ عُمَرُ عَنْهُ الْقَتْلَ وَ لَمْ يَدْرِ كَيْفَ يَحُدُّهُ فَقَالَ لِأَمِيرِ الْمُؤْمِنِينَ ع أَشِرْ عَلَيَّ فِي حَدِّهِ فَقَالَ حَدُّهُ ثَمَانُونَ إِنَّ شَارِبَ الْخَمْرِ إِذَا شَرِبَهَا سَكِرَ وَ إِذَا سَكِرَ هَذَى وَ إِذَا هَذَى افْتَرَى فَجَلَدَهُ عُمَرُ ثَمَانِينَ وَ صَارَ إِلَى قَوْلِهِ ع فِي ذَلِكَ‏."

Cikin Irshaad, yazo ta hanyoyin jama'a da kuma kebe cewa; Lalle Qudaamata Bn Maz'uun ya sha Giya, sai Umar yayi nufin yi masa bulala, sai Qudaamata yace masa:

" Ai haddi bai hau kaina ba, domin kuwa Allah madaukaki na cewa: " BABU LAIFI AKAN WADANDA SU KAYI IMANI KUMA AUKA AIKATA KYAKKYAWA CIKIN ABINDA SUKA CI MATUQAR DAI SUNYI TAQAWA KUMA SU KAYI IMANI KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA."

Sai Umar ya tunkude yi masa haddi, sai labari ya riski shugaban muminai Ali (A.S), sai ya tafi zuwa ga Umar yace masa:

" ME YASA KABAR YIN HADDI AKAN QUDAAMATA GAME DA SHAN GIYA ? Sai yace:

" Ai ya karanta min aya ce. " Sai Umar din ya karantota. Sai shugaban muminai Ali (A.S) yace:

"AI QUDAAMATA BA YA DAGA CIKIN AHLIN WANNAN AYA, KUMA BA WANDA YA RIQI TAFARKINSA CIKIN ABINDA ALLAH YA HARAMTA. LALLE WADANDA SU KAYI IMANI KUMA SU KAYI KYAKKYAWAN AIKI BA SA HALATTA HARAM. KA DAWO DA QUDAAMATA KACE YA TUBA DAGA ABINDA YA FADA. IDAN YA TUBA SAI KA ZARTAR MASA DA HADDI, IDAN KUMA BAI TUBA BA, TO, KA KASHE SHI DOMIN YA FICE DAGA TAFARKI."

Sai Umar ya farka saboda haka, ya sanarwa Qudaamata labarin, sai ya bayyanar da tubansa da kuma nadamarsa. Sai Umar yabar yi masa hukuncin kisa, amma kuma bai san yadda zai yi masa haddi (na bulalar ba), sai ya cewa shugaban muminai (A.S)!

 " Ka nuna min yadda zanyi masa haddin." Sai yace:

" HADDINSA SHINE BULALA 80, DOMIN SHI MASHAYIN GIYA IDAN YA SHA TA YA KANYI MAYE, KUMA IDAN YAYI MAYE YAKAN FADI MAGANA CIKIN RASHIN HAYYACINSA (he will be out of sense), KUMA IDAN YA FITA DAGA HAYYACINSA YAKAN QIRQIRI (kowanne irin abu)."

Sai Umar yayi masa bulala 80, kuma ya cigaba da wannan magana ta shugaban muminai."

إرشاد المفيد ص 95.

(3)- المناقب لابن شهرآشوب رَوَتِ الْخَاصَّةُ وَ الْعَامَّةُ أَنَّ أَبَا بَكْرٍ 

أَرَادَ أَنْ يُقِيمَ الْحَدَّ عَلَى رَجُلٍ شَرِبَ الْخَمْرَ فَقَالَ الرَّجُلُ إِنِّي شَرِبْتُهَا وَ لَا عِلْمَ لِي بِتَحْرِيمِهَا فَأُرْتِجَ عَلَيْهِ فَأَرْسَلَ إِلَى عَلِيٍّ ع يَسْأَلُهُ عَنْ ذَلِكَ فَقَالَ مُرْ نَقِيبَيْنِ مِنْ رِجَالِ الْمُسْلِمِينَ يَطُوفَانِ بِهِ عَلَى مَجَالِسِ الْمُهَاجِرِينَ وَ الْأَنْصَارِ وَ يَنْشُدَانِهِمْ هَلْ فِيهِمْ أَحَدٌ تَلَا عَلَيْهِ آيَةَ التَّحْرِيمِ أَوْ أَخْبَرَهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ ص فَإِنْ شَهِدَ بِذَلِكَ رَجُلَانِ مِنْهُمْ فَأَقِمِ الْحَدَّ عَلَيْهِ وَ إِنْ لَمْ يَشْهَدْ بِذَلِكَ فَاسْتَتِبْهُ وَ خَلِّ سَبِيلَهُ فَكَانَ الرَّجُلُ صَادِقاً فِي مَقَالِهِ فَخَلَّى سَبِيلَهُ‏[38].

Ya zo cikin Manaqib na Ibn Shahr Ashub daga mutane kadan da ma masu yawa cewa; 

Lalle Abubakar yayi nufin zartar da haddi kan wani mutum wanda yasha Giya, sai mutumin yace:

" Lalle ni na sha ta amma bani da wani ilimi kan hanin da akayi a kanta. Sai abin ya sarqaqe masa (wato Abubakar ya kasa sanin hukuncin zartarwa), sai ya aika zuwa ga Aliyu (A.S) yana tambayarsa game da haka. Sai yace:

" KA UMARCI WASU DANGI GUDA BIYU DAGA CIKIN MUTANE MUSULMAI SU KEWAYA DASHI AKAN GURAREN ZAMAN MUHAJIRAI DA ANSAR SUNA HADA SU DA ALLAH. SHIN CIKINSU AKWAI WANDA YA TABA KARANTA MASA AYAR HARAMCIN (shan giya) KO KUMA WANDA YA BA SHI LABARI DAGA MANZON ALLAH (S.A.W.W)? IDAN KUWA BA A SANAR DANI HAKAN BA, TO, A KARBI TUBANSA KUMA YA KAMA HANYARSA, YA KASANCE MUTUM MAI GASKIYA CIKIN MAGANAR TASA, SAI YA KAMA GABANSA."

(1) التهذيب ج 10 ص 90. و مثله في الكافي ج 7 ص 215 و 214

Wannan shine hukuncin wanda yasha giya, sai dai ba wai kawai ana zartar masa da hukunci bane don an sami shaidun da suka shaida cewa ya sha giya, a'a, dole sai an tuhume shi game da sanin wannan hukunci na haramci.

Yanzu da za a sami wanda ba musulmi ba ya muslimta sai kuma yasha gida daga baya, to, ko da shari'ar muslimci ake yi a qasar ba za a zartar masa da hukunci ba, dole sai an tabbatar da cewa ya san shan giya haramun ne.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

29th December, 2021/ 24th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post