Hukuncin mai gusar da sha'awarsa ta hanyar wasa da wani bangaren jikinsa

Abbakarkoso

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

JINSIN MUTANE UKU DA BA ZA SU SHIGA ALJANNAH BA

Allah (T) ne ya halicce mu kuma ya zama mai iko akan dukkan bangarorin jikinmu, gangar jikinmu tamu ce amma ba mu da ikon sarrafata ta hanyar da mu kaga dama, dole ya zama munyi amfani dasu ta hanyar da wanda ya halitta mana su ke so.

Akwai wasu abubuwa da mutane ke yi bisa son zuciyarsu wanda zai iya kaisu wuta ba tare da sun sani ba, domin wasu suna yi ne bisa rashin sanin hukuncin hakan.

Mace ko namiji kanyi amfani da wani bangaren jikinsu (their private part) don gamsar da kawukansu ko gusar da sha'awarsu irin ta jinsi, yin hakan kuwa haramun ne wanda zai iya kaisu ga shiga wuta.

Ya zo cikin riwaya kamar haka;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

الخصال : عَنْ سَعْدٍ عَنِ الطَّيَالِسِيِّ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ عَوْفٍ عَنِ ابْنِ أَبِي نَجْرَانَ التَّمِيمِيِّ عَنِ ابْنِ حُمَيْدٍ عَنْ أَبِي بَصِيرٍ قَالَ سَمِعْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع يَقُولُ‏ ثَلَاثَةٌ لا يُكَلِّمُهُمُ اللَّهُ يَوْمَ الْقِيامَةِ وَ لا يَنْظُرُ إِلَيْهِمْ‏ ... وَ لا يُزَكِّيهِمْ وَ لَهُمْ عَذابٌ أَلِيمٌ‏ النَّاتِفُ شَيْبَهُ وَ النَّاكِحُ نَفْسَهُ وَ الْمَنْكُوحُ فِي دُبُرِهِ‏.

Ya zo cikin Al-Kisaal, daga Sa'ad, daga 'Dayyaliaiy, daga Abdurrahman Bn Awfin, daga Ibn Abiy Najraana Al-Tamimiyyi, daga Ibn Humaid daga Abu Baseer yace: Naji Abu Abdullah (A.S) yana cewa:

" MUTANE UKU ALLAH BA ZAIYI MAGANA DASU RANAR ALQIYAMA BA, KUMA BA ZAI YI DUBI ZUWA GARE SU BA....KUMA BA ZAI TSARKAKE SU BA, KUMA GARE SU AKWAI AZABA MAI RADADI.

(1)- MAI CIRE FURFURARSA:- Wannan farin gashi dake fitowa mutum a kayinsa musamman in ya soma girma, wasu kuma tun a halin quruciya ma yakan fito musu. To, cire wannan farin gashin haramun ne.

(2)- DA MAI AUREN KANSA:- Auren kai shine mutum ya riqa wasa da al'aurarsa don gusar da sha'awa. Mata kanyi amfani da dan yatsansu (finger) su sanya shi cikin farji suna wasa dashi cikinsa har su gamsu. Maza kuma kanyi amfani da Azzakarinsu ta hanyar murzawa har buqatarsu ta biya. Kuma mace na zuwa ga 'yar'uwarta mace don gamsar da junansu, to, yin hakan haramun ne.

(3)- DA WANDA KE ZUWA GA MACE KO NAMIJI TA DUBURA:- Haramun ne mutum ya jewa mace ta dubura ko da kuwa matarsa ce, kuma haramun ne namiji ya jewa dan'uwan namiji ."

الخصال ج 1 ص 52

Saboda haka sai kiyaye ko da an kasance ana aikatawa a baya.

" DUK WANDA WA'AZI YAZO MASA YA HANU, TO, YANA DA ABINDA YA GABATA AL'AMARINSA NA WAJEN ALLAH......"

Wato abinda ya aikata a baya ya wuce matuqar ya bari kuma ya tuba.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      (08137925034)

29th December, 2021/ 24th Jimada-Ulah, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post