Shin, gaske ne matan Annabi (S.A.W.W) na daga cikin Ahlul-bayt ?


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

AMSA DAGA BAKIN UMMUL-MUMININA UMMUS-SALAMATA (R.A)

Babban abinda ya kamata a sani shine, Allah (T) ba ya yin magana sannan yazo ya warwareta daga baya, in da ya kasance haka to da kuwa bai kasance Allah abin bauta ba.

Aikata sabo ko kuskure na daga cikin gazawa ta 'Dan Adam ko kuma nace wanda ba Annabi bane kuma ba wanda Allah ya katange shi ba . Duk wanda zai iya aikata sabo ko kuma aikata kuskure cikin ayyukansa ba zai taba zama jagora wanda zai gaji Annabi (S.A.W.W) wajen isar da saqonsa ba.

Yana daga cikin abinda har gobe wasu na cikin duhu na rashin saninsa shine su wanene Ahlul-Bait na Manzon Allah (S.A.W.W) wadanda Allah ya tsarkake su.

An kasu kashi uku ne game da sanin su wanenene. Wasu sun tafi ne kan cewa matan Annabi (S.A.W.W) ne kadai Ahlul-Baitinsa, wai domin ayar da tayi magana kansu ta zo ne cikin ayoyin da ake magana kan matan nasa.

Wasu kuma suka ce a'a, abin ya wuce nan don bai taqaita a kansu kadai ba, har da wasu daga cikin 'ya'yansa da kuma danginsa. Wasu kuma suka ce a'a, iyalan nasa (S.A.W.W) sune wadanda aka tsarkake kuma aka haramta musu cin sadaqa.

Ayar da tayi magana dai kan su wanene Ahlul-Bait (A.S) ita ayar nan ta cikin suratul-Ahzab wacce za muyi nuni kanta insha Allahu. Gata kamar haka:

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾 

"......إِنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيُذۡهِبَ عَنكُمُ ٱلرِّجۡسَ أَهۡلَ ٱلۡبَيۡتِ وَيُطَهِّرَكُمۡ تَطۡهِيرٗا ."( ٣٣)

" ABIN SANI KAWAI ALLAH NA NUFIN YA TAFIYAR DA QAZANTA CE DAGA GARE KU YAA KU IYALAN GIDA, KUMA YA TSARKAKE KU TSARKAKEWA ."

(AHZAB, AYA TA 33)

To, anan za muyi amfani da wata riwaya wacce tazo daga cikin dayan ingantattun littafan Sunnah daga bakin daya daga cikin matan fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S.A.W.W) wato Ummus-Salamata (R.A).

Riwayar tana cewa;

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

«4245» حدثنا محمود بن غيلان حدثنا أبو أحمد الزبيري حدثنا سفيان عن زبيد عن شهر بن حوشب عن أم سلمة أن النبي صلى الله عليه وسلم جلل على الحسن والحسين وعلي وفاطمة كساء ثم قال: ((اللهم هؤلاء أهل بيتي وخاصتي أذهب عنهم الرجس وطهرهم تطهيرا)). فقالت أم سلمة وأنا معهم يا رسول الله قال: ((إنك إلى خير)). قال: هذا حديث حسن صحيح وهو أحسن شيء روي في هذا الباب.

وفي الباب عن عمر بن أبي سلمة وأنس بن مالك وأبي الحمراء ومعقل بن يسار وعائشة.

Muhammad Bn Ghailana ya bamu labari, Abu Ahmad Al-Zubairiy ya bamu labari, Sufyan ya bamu labari daga Zubair, daga Shahru Bn Haushabi, daga Ummus-Salamata cewa; " Lalle Annabi (S.A.W.W) ya dora mayafinsa akan Hassan da Hussaini da Aliyu da kuma Fadimatu, sa'an nan yace;

" YAA UBANGIJI WADANNAN SUNE IYALAN GIDANA KUMA KEBANTATTUNA, KA TAFIYAR DA QAZANTA DAGA GARE SU KUMA KA TSARKAKE SU TSARKAKEWA."

Sai Ummus-Salamata tace; " Har nima ina tare dasu yaa Ma'aikin Allah ?" Yace:

" KE DAI KINA KAN ALKHAIRI (amma ba wannan matsayin ba) ."

Tirmidhi yace: " Wannan hadisi mai kyau ne kuma ingantacce, kuma shine ma abu mafi kyau wanda aka riwaito cikin wannan babi. Kuma cikin babin akwai (wani hadisin da aka riwaito irin wannan) daga Amru Bn Abiy Salamata, da Anas Bn Malik da Abu Himraa'a, da Ma'aqalu Bn Yasaari da kuma A'isha.

(SUNAN-TIRMIDHI, HADISI MAI LAMBA 4245)

To, ina ga kamar dukkan soyayya da mutum zai nunawa wani ba za ta kai son da shi wanin ke yiwa kansa ba. Ga abinda ya fito daga bakunan matan Annabi (S.A.W.W) cewa su basu cikin wannan aji inji mijin nasu, amma duk da haka sai ga shi wasu na musanta su cewa qarya suke yi don kuwa har da su cikin wannan matsayi.

Yanzu ya rage ga mai hankali yayi nazari, shin, abinda wadannan malamai suka kawo suka ingantasu qarya suka yiwa matan Annabi (S.A.W.W) ko kuma matan nasa ne suka yi qarya da suka bada wannan labari ?

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

    (08137925034)

16th September, 2021/ 10th Safar, 1443.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Gaskiyane matan annabi basa cikin Ahlulbayt. Allah ya saka da alkhairi da irin wannan karatu. Muna godiya sosai.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post