Ci gaba 3: Rabon gado a Muslunci

Sheikh Adamu Ahmad Tsoho

RABON GADO A MUSLIMCI (INHERITANCE) !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BA A TAUYE WANI ABU DAGA CIKIN KASON MIJI KO 'DAN'UWA LI'UMMICikin wannan rubutu namu mun dauko mas'alar rabon gado ne wanda ya hada Miji, 'Yan'uwa Li'ummai da kuma 'Yan'uwa Li'abai, wato 'yan'uwan da mamaci ya hada dangantaka dasu ta bangaren Uwa dana bangaren Uba.


Ga yadda kason zai kasance da iznin Allah.


๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ


ุชูุณูŠุฑ ุงู„ุนูŠุงุดูŠ ุนَู†ْ ู…ُุญَู…َّุฏِ ุจْู†ِ ู…ُุณْู„ِู…ٍ ุนَู†ْ ุฃَุจِูŠ ุฌَุนْูَุฑٍ ุน ู‚َุงู„َ: ู‚ُู„ْุชُ ู„َู‡ُ ู…َุง ุชَู‚ُูˆู„ُ ูِูŠ ุงู…ْุฑَุฃَุฉٍ ู…َุงุชَุชْ ูˆَ ุชَุฑَูƒَุชْ ุฒَูˆْุฌَู‡َุง ูˆَ ุฅِุฎْูˆَุชَู‡َุง ู„ِุฃُู…ِّู‡َุง ูˆَ ุฅِุฎْูˆَุฉً ูˆَ ุฃَุฎَูˆَุงุชٍ ู„ِุฃَุจِูŠู‡َุง ู‚َุงู„َ 

ู„ِู„ุฒَّูˆْุฌِ ุงู„ู†ِّุตْูُ ุซَู„َุงุซَุฉُ ุฃَุณْู‡ُู…ٍ ูˆَ ู„ِุฅِุฎْูˆَุชِู‡َุง ู…ِู†َ ุงู„ْุฃُู…ِّ ุงู„ุซُّู„ُุซُ ุณَู‡ْู…َุงู†ِ ุงู„ุฐَّูƒَุฑُ ูِูŠู‡ِ ูˆَ ุงู„ْุฃُู†ْุซَู‰ ุณَูˆَุงุกٌ ูˆَ ุจَู‚ِูŠَ ุณَู‡ْู…ٌ ู„ِู„ْุฅِุฎْูˆَุฉِ ูˆَ ุงู„ْุฃَุฎَูˆَุงุชِ ู…ِู†َ ุงู„ْุฃَุจِ- ู„ِู„ุฐَّูƒَุฑِ ู…ِุซْู„ُ ุญَุธِّ ุงู„ْุฃُู†ْุซَูŠَูŠْู†ِ‏ ู„ِุฃَู†َّ ุงู„ุณِّู‡َุงู…َ ู„َุง ุชَุนُูˆู„ُ ูˆَ ู„ِุฃَู†َّ ุงู„ุฒَّูˆْุฌَ ู„َุง ูŠَู†ْู‚ُุตُ ู…ِู†َ ุงู„ู†ِّุตْูِ ูˆَ ู„َุง ุงู„ْุฅِุฎْูˆَุฉُ ู…ِู†َ ุงู„ْุฃُู…ِّ ู…ِู†ْ ุซُู„ُุซِู‡ِู…ْ‏ ูَุฅِู†ْ ูƒุงู†ُูˆุง ุฃَูƒْุซَุฑَ ู…ِู†ْ ุฐู„ِูƒَ ูَู‡ُู…ْ ุดُุฑَูƒุงุกُ ูِูŠ ุงู„ุซُّู„ُุซِ‏ ูˆَ ุฅِู†ْ ูƒَุงู†َ ูˆَุงุญِุฏุงً ูَู„َู‡ُ ุงู„ุณُّุฏُุณُ ูˆَ ุฃَู…َّุง ุงู„َّุฐِูŠ ุนَู†َู‰ ุงู„ู„َّู‡ُ ูِูŠ ู‚َูˆْู„ِู‡ِ- ูˆَ ุฅِู†ْ ูƒุงู†َ ุฑَุฌُู„ٌ ูŠُูˆุฑَุซُ ูƒَู„ุงู„َุฉً ุฃَูˆِ ุงู…ْุฑَุฃَุฉٌ ูˆَ ู„َู‡ُ ุฃَุฎٌ ุฃَูˆْ ุฃُุฎْุชٌ ูَู„ِูƒُู„ِّ ูˆุงุญِุฏٍ ู…ِู†ْู‡ُู…َุง ุงู„ุณُّุฏُุณُ ูَุฅِู†ْ ูƒุงู†ُูˆุง ุฃَูƒْุซَุฑَ ู…ِู†ْ ุฐู„ِูƒَ ูَู‡ُู…ْ ุดُุฑَูƒุงุกُ ูِูŠ ุงู„ุซُّู„ُุซِ‏ ุฅِู†َّู…َุง ุนَู†َู‰ ุจِุฐَู„ِูƒَ ุงู„ْุฅِุฎْูˆَุฉَ ูˆَ ุงู„ْุฃَุฎَูˆَุงุชِ ู…ِู†َ 

ุงู„ْุฃُู…ِّ ุฎَุงุตَّุฉً.


Ya zo cikin Tafsir na Ayyashi, daga Muhammad Bn Muslim, daga Abu Ja'afar (A.S) yace: Nace masa, " Me za ka fada game da matar data rasu ta bar Mijinta da 'yan'uwanta na bangaren Uwa da kuma 'yan'uwa maza da mata ta gangaren Ubanta ? Yace;


" MIJI YANA DA RABI 1/2 , SAI AYI KASO UKU, 'YAN'UWANTA NA BANGAREN UWA SUNA DA 'DAYA BISA UKU 1/3, SAURA KASO BIYU, DUKKA MAZA DA MATAN DAIDAI SUKE (wajen samun kaso ta yadda babu wanda zai fi wani). SAURAN KASON NA 'YAN'UWA MAZA DA 'YAN'UWA MATA NE NA BANGAREN UBA, NAMIJI NA DA KASO BIYU NA MACE. DOMIN SHI KASON BA A YI MASA AULU (wato ba zai kasance ta yadda wani daga cikin miji ko 'yan'uwa Li'ummai su rasa wani abu cikin kason da Allah yace a basu ba), DOMIN SHI MIJI BA ZA A TAUYE SHI DAGA RABI 1/2 BA, HAKAMA 'YAN'UWA TA BANGAREN UWA BA ZA SU RASA WANI ABU DAGA CIKIN 'DAYA BISA UKUNSU 1/3 BA.


" IDAN KUMA (su 'yan'uwa Li'ummai) SUKA KASANCE SUNFI HAKA, TO, SAI SUYI TARAYYA CIKIN 'DAYA BISA UKU 1/3, IDAN KUMA (dan'uwan) SHI KADAI NE, TO, YANA DA 'DAYA BISA SHIDA 1/6."


TO, AMMA WANNAN WANDA ALLAH YAYI MAGANARSA CIKIN FADINSA (S.W.A) ;


" IDAN MUTUM YA KASANCE AN GAJE SHI BISA KALALA KO KUMA MACE , KUMA YANA DA 'DAN'UWA KO 'YAR'UWA, KOWANNE DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BIDA SHIDA 1/6, IDAN KUMA SUNFI HAKA, TO, SAI SUYI TARAYYA CIKIN 'DAYA BISA UKU 1/3."


TO, WANNAN (magana) TANA KAN 'YAN'UWA NE WADANDA AKA HADU DASU TA BANGAREN UWA KADAI ."


ุชูุณูŠุฑ ุงู„ุนูŠّุงุดูŠّ ุฌ 1 ุต 226.                       MISALI

              ________________


Mata ce ta rasu tabar mijinta da 'yan'uwa maza da mata ta bangaren Uba, da kuma 'yan'uwa maza da mata ta bangaren Uwa, tare da dukiya #1,000,000


YADDA KASON ZAI KASANCE

_____________________________To, anan shi miji yana da rabin abinda matar tasa ta bari ne tunda bashi da 'ya'ya kuma bashi da mahaifa, 'yan'uwansa ta bangaren Uwa kuma suna da kaso daya (1) ne cikin kashi uku na dukiyar. Su kuma 'yan'uwa wadanda suka hadu ta bangaren Uba za su sami saura ne bayan an cirewa kowa kasonsa kamar yadda Qur'ani ya fada.


Saboda haka sai kason ya zama kamar haka;


๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ


MIJI LI'UMMAI LI'ABAI     


   1 1 ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ

____ __________ _______

   2 3 saura

   3 + 2 ๐Ÿ‘‡๐Ÿพ

________________________

               6


          KASON MIJI


  3 1,000,000

__ * ________= #500,000

  6 1

      KASON LI'UMMAI

  2 1,000,000

___ * _________=#333,333

  6 1

Cikin wannan kaso za muga Miji ya sami rabin abinda matarsa ta bari, shine #500,000 daga cikin #1,000,000, su kuma 'yan'uwa wadanda suka hadu ta bangaren Uwa sun sami kashi daya (1) daga cikin kashi uku na dukiyar, shine #333,333 daga cikin #1,000,000. Saboda haka zasu raba shi ne daidai-wa-daida tsakaninsu, babu fifiko tsakanin namiji da mace.

Idan muka hada kason miji dana 'yan'uwa ta bangaren Uwa za mu sami kamar haka;

    #500,000

+ #333,333

    __________

     #833,333

    ___________

Abinda ya rage daga cikin #1,000,000 bayan an cire #833,333 shine #166,6667, to, wannan sauran shine kason 'yan'uwa wadanda suka hadu ta bangaren Uba, sai namiji ya dau kaso biyu na kason mace, domin su hukuncinsu iri daya ne da hukuncin 'ya'ya idan babu 'ya'yan kuma babu 'yan'uwan mamaci wadanda suka hadu kan Uwa da Uba.

ALLAH YASA MU DACE

๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ™๐Ÿป


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da Ado Isah Guda.


      (08137925034)

10th September, 2021/ 4th Safar, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post