Ci gaba 2: Rabon gado a Muslunci


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES @

HAR CIKIN SAHABBAI SUNA DA RASHIN ILIMIN SANIN MA'ANAR KALALA

Sau da yawa mutane na fitar da hukunci ne bisa jahilinci da sunan Ijtihadi, shi kuwa Ijtihadi ana yinsa ne idan ya zamana babu hukunci qarara da yazo cikin Qur'ani ko kuma cikin Hadisan Annabi (S.A.W.W) ko na A'imma (A.S).

Rashin saninka ga abu bai zama babu hukuncinsa ba, saboda haka ko tambaya akayi maka sai ya zama baka sani ba, to, maimakon ka fitar da wata fatawa ta qashin kanka ka miqa abin zuwa ga ma'abotansa don kaucewa fadawa cikin halaka bisa rashin sani.

TAMBAYAR DA AKA YIWA ABUBAKAR

👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

 الإرشاد سُئِلَ أَبُو بَكْرٍ عَنِ الْكَلَالَةِ فَقَالَ أَقُولُ فِيهَا بِرَأْيِي فَإِنْ أَصَبْتُ فَمِنَ اللَّهِ وَ إِنْ أَخْطَأْتُ فَمِنْ نَفْسِي وَ مِنَ الشَّيْطَانِ فَبَلَغَ ذَلِكَ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ ع فَقَالَ مَا أَغْنَاهُ عَنِ الرَّأْيِ فِي هَذَا الْمَكَانِ أَ مَا عَلِمَ أَنَّ الْكَلَالَةَ هُمُ الْإِخْوَةُ وَ الْأَخَوَاتُ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ وَ الْأُمِّ وَ مِنْ قِبَلِ الْأَبِ عَلَى الِانْفِرَادِ وَ مِنْ قِبَلِ الْأُمِّ أَيْضاً عَلَى حِدَتِهَا قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ‏ يَسْتَفْتُونَكَ قُلِ اللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِي الْكَلالَةِ إِنِ امْرُؤٌ هَلَكَ لَيْسَ لَهُ وَلَدٌ وَ لَهُ أُخْتٌ فَلَها نِصْفُ ما تَرَكَ‏ وَ قَالَ عَزَّ قَائِلًا وَ إِنْ كانَ رَجُلٌ يُورَثُ كَلالَةً أَوِ امْرَأَةٌ وَ لَهُ أَخٌ أَوْ أُخْتٌ فَلِكُلِّ واحِدٍ مِنْهُمَا السُّدُسُ فَإِنْ كانُوا أَكْثَرَ مِنْ ذلِكَ فَهُمْ شُرَكاءُ فِي الثُّلُثِ‏.

Ya zo cikin Irshad cewa an tambayi Abubakar game da KALALA, sai yace: " Zan fada a kanta bisa ra'ayina, idan nayi daidai daga Allah ne, idan kuma nayi kuskure to, daga gare ni ne kuma daga Shaidan."

Sai labarin ya iso ga Amirul-Muminina Ali (A.S), sai yace: " Ai ra'ayi ba zai wadatar dashi ba a wannan guri. Shi bai san cewa KALALA sune 'yan'uwa maza ko 'yan'uwa mata na bangaren Uwa da Uba ba? Da kuma bangaren Uba bisa kadaita, da kuma bangaren Uwa bisa kadaituwarta ? Allah (T) na cewa;

" SUNAYI MAKA FATAWA, KACE ALLAH NAYI MUKU FATAWA CIKIN KALALA. IDAN MUTUM YA HALAKA BA SHI DA 'DA AMMA YANA DA 'YAR'UWA, TO, TANA DA RABIN ABINDA YA BARI."

Kuma Allah mai girma da daukaka yace;

" IDAN YA KASANCE MUTUM AN GAJE SHI BISA KALALA KO KUMA MACE, KUMA YANA DA 'DAN'UWA KO 'YAR'UWA, TO, KOWANNE DAGA CIKINSU YANA DA 'DAYA BIDA SHIDA 1/6 , IDAN KUMA YA KASANCE SUNFI HAKA, TO, SAI SUYI TARAYYA CIKIN 'DAYA BISA UKU 1/3 ."

إرشاد المفيد ص 107 طبع النجف.

NB:- Idan muka kalli wannan hukunci da yazo cikin ayoyin za muga hukunci kala biyu ne, wato 'yan'uwa na bangaren Uwa da Uba ko bangaren Uba wadanda hukuncinsu iri daya ne ida babu mafi kusanci ga mamaci.

Abu na biyu kuma shine hukuncin 'yan'uwa wadanda Uwa ce ta hada su da mamaci, to, su hukuncinsu iri daya ne, idan sun kadaita kowa zai sami daya bisa shida ne 1/6, idan kuma sun hadu da yawa sai a kasa dukiyar kashi uku a basu daya daga ciki su raba daidai-wa-daida babu fifiko tsakanin namiji da mace.

To, irin wannan rashin fahintar hukunci da aka samota tun a farko yayi naso har zuwa wannan zamani ana yi hukunci ba bisa ilimi ba da sunan Ijtihadi, alhali hukunci nanan cikin littattafai wajen ma'abota sani da aka kauce musu.

YA ALLAH KA SANAR DAMU ILIMI NA HAQIQA.

🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       (08137925034)

10th September, 2021/ 4th Safar, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post