Zalunci da Danniya Basa Hana Gaskiya Wanzuwa (2)




Kamar yadda na faɗa Hadisai da dama sun yi magana akan zalunci amma bari na tsakuro kaɗan daga ciki:


A wasu sanannun hadisai an ruwaito: 


1.Manzon Allah[S] ya ce, “Kuji tsoron yin zalunci domin zalunci duhu ne ranar kiyama.” Wato zai kasance ma mutum musiba ranar lahira.


2-Manzon Allah[S] ya ce, “Za a zo da mutum ranar lahira tare da lada mai tarin yawa, sai wani mutum ya zo ya ce, ya ubangiji ya zalunce ni, sai a kwashi ladarsa abayar da ita ga wanda ya zalunta, can wani shima ya zo cikin waɗanda ya zalunta a sake ɗibar ladarsa a bashi, haka-da-haka dai har ta kai ga ba yada wata sauran lada,idan wani wanda ya zalunta ya zo to sai a kwashi zunubinsa a zuba masa har ta kai daga ƙarshe akai wannan azzalumi zuwa ga wuta.”


3-Imam Ali[AS] ya ce, “Duk wanda ya ci dukiyar ɗan uwansa a bisa zalunci to zai ci wani yanki na wuta ranar ƙiyama.”


4- Imam Sadiƙ ya ce, “Duk wanda ya yi zalunci to sai Allah ya sallaɗa masa wani da zai zalunce shi.


5-Imam Ali ya ce, “Duk wanda ya yi zalunci to Allah zai gaggatar da halakarsa, a wata ruwaya ya ce, “Duk wanda ya yi zalunci to zai gajarta rayuwarsa.”wato rayuwarsa ba zata yi tsawo ba.


6-Imam Baƙir ya ce, “Kaji tsoron zaluntar wanda bai da wani mai taimako akan ka in ba Allah ba.”


7-Imam Ali ya ce, “Ranar hukunci akan azzalumi tafi tsanani akan ranar zalunci kan wanda aka zalunta.” Wato ranar da Allah zai kama azzalumi tafi tsanani gareshi kan ranar da ya zalunci wanda ya zalunta.


8-Imam Baƙir ya ce, “Abinda wanda aka zalunta yake samu daga azzalumi to yafi akan abinda azzalumi yake samu kan wanda ya zalunta.” Wato shi azzalumi ya cutar da wanda ya zalunta a duniyan ne, shi kuma wanda aka zalunta ya yi masa illa a addinan ce kamar misalin wancan Hadisin na sama cewa za a kwashi ladar azzalumi in yana da ita a bama wanda ya zalunta in kuma bai da ita akwashi zunubin wanda aka zalunta a zuba masa,shi yasa a wani Hadisi Manzon Allah yana cewa, “Zalunci nadama ne.”  Wato ƙarshen azzalumi nadama a duniya da lahira, maikaratu ka dubi yadda ƙarshen azzalumai yake kasancewa tun a wannan gida na duniya ballantana kuma a lahira.



Bari na ɗan bamu misali: Idan ana batun zalunci dole sai an faɗi ɗaya daga cikin waɗannan mutanen, wato Lamarudu da Fir'auna, sanin kowa ne waɗannan mutane ba ƙananun azzalumai bane kamar yadda yazo a tarihi, annabawan da suka yi rayuwa tare da waɗannan azzalumai sun azabtu kuma sun wahaltu matuƙa a gurin wannan azzalumai.



Annabi Ibrahim (AS) babu irin cutawar da ba'a yi masa ba har wuta sai da aka haɗa aka jefa shi a ciki amma da yake shi yake tare da gaskiya sai da yakai ga gaci saboda daman shi Allah (T) yana tare da maigaskiya ne a koda-yaushe, Allah baya goyon-bayan azzalumi kawai dai yana ara masa lokaci ne yayi iya abin da zai iya kafin ya damƙeshi, sannan kuma duk wata cutarwa ko azabtarwa ga mumini to jarabawa ce kuma da mutum yayi ƙoƙarin dakewa da jurewa ƙarshe nasara ce zata biyo baya.


Lamarudu har wutarsa da aljannarsa sai da ya ƙirƙira saboda tsabar zalunci domin ya samu ƙarfin Mulkin da babu wani mai iya ja dashi a lokacinsa amma daga ƙarshe dai yanzu ya zama tarihi.


Mu leƙa rayuwar Fir'auna: zamu ga babu irin nau'ikan zalunci da danniyar da bai yi ba a lokacinsa domin dai kada karshensa yazo saboda bokayensa sun faɗa masa cewa za'a haifi wanda zai kawo karshen mulkinsa na danniya da zalunci, sai Fir'auna ya riƙa kashe jarirai (sabuwar haihuwa) maza, daga yaji an haihu sai ya tura a kashe masa abin da aka haifa idan namiji ne, abin har sai da yakai ga kamo duk wata mace da take da ciki (juna-biyu) ya aje su a gidansa duk wacce ta haifi ɗa namiji sai a kashe shi, amma duk da wannan dubarar tasa hakan bai hana a haifi Annabi Musa (AS) Wanda ya taso a gidansa cikin hikima irinta Allah (T) kuma yazo ya kawo ƙarshhensa.


Annabi Musa (AS) ya wahaltu matuƙa kusan sai ace shi abin biyu ya zame masa shi da ɗan uwansa Annabi Haruna (AS), ga fama da suke da Fir'auna sannan ga wasu irin mabiya da suke warware duk wani kyakkyawan tsari da yayi, duk da haka da cutawar sai ya dake kuma Allah (T) ya taimakesa yaci nasara akan Fir'auna da mutanensa.


Idan kuma dukiya kake alfahari da ita kake zaluntar al'umma da danne musu haƙƙi, yau ina ɗan ƙaruna yake? Shima tashi ta daɗe da ƙarewa, to saboda haka kowane azzalumi, ɗan kama-karya da mai danne haƙƙin Al'umma ya kwana da sanin cewa shima tana nan tafe kansa, ina yi masa albishir da cewa ƙarshensa zai zo ko kusa ko nesa domin zalunci baya ɗorawa.


Annabawan Allah (AS) dukkansu sun sha wahalhalu da tsangwama a gurin azzaluman lokacinsu, Annabi Nuhu (AS) sai da ya shafe shekaru daruruwa yana da'awa, babu kalar cutawar da ba'a masa ba, an sha kashe shi a jefar dashi a bayan gari amma Allah (T) ya tashi abinsa, hakan bai sa ya karaya ba ƙarshe Allah (T) ya kawo masa ɗauki yayi nasara akan azzalumai.


Annabin Yusuf (AS) shi a cikin cutarwa da aka yi masa har gidan yari (kurkuku) aka saka shi, yasha wahaloli iri-iri amma daga karshe yayi nasara akan azzalumai.


Annabawa sun jarabtu sosai matuƙa ga cutarwa da azabobi daga azzaluman lokacinsu amma sai suka jure daga ƙarshe nasara ce ta biyo bayan duk wahalhalun da suka sha.



Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAWA) shima ma an sha ƙalla masa tuggu, ƙulle-ƙulle da makirce-makirce kala-kala daga azzaluman lokacinsa, babu nau'in cutawar da basu yi masa ba har hana shi fita sai da suka yi, an hana a siya ko a sai da masa shi da sauran Muminan da suke tare da shi bisa tsantsar zalunci, amma daga baya yayi nasara akan azzalumai.


Duk waɗancan wahalhalun da cutarwa da yasha gagarumar nasara ce ta biyo bayansu tun daga fatahu Makkah da kyakkyawar nasarar da aka samu zuwa yanzu kusan shekaru sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu musulunci sai daɗa bunƙasa  yake, zalunci da danniyar azzalumai bai hana wanzuwar sa ba.


Zan cigaba.


©A A Wisdom Daura

04/08/2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post