'Yan Uwa Soyayya Da Aure Ba'abun Wasa Bane A Social media, Yakamata Mu kiyaye !!!Babu wurin da aka mayar da so kamar sanya riga da cire shi irin social media. Abun da mamaki, Daga ganin hoton mutum, baka san ɗan gidan waye ko a ina ya tashi ba. Mutunci ko rashin mutuncin gidansu, addini ko rashinsa ba kawai dai tunda macece kai kana so ko kuma tun da namiji ne tana so. Har akan samu wasu da suke da kamar tabun hankali su zauna suna shirya maganar aure a social media ba tare da an haɗu ba. So da aure ba abun wasa bane jama’a, shiyasa yaudara ya yi yawa a wurin maza da mata. Domin bai zama dole don kun yi shekaru a wani website ya zama idan kun haɗu ku yi aure ba.


Na ga wacce ta yi shekara wurin biyu da wani bawan Allah suna soyayya sosai amma shi yana karatu ne a wata ƙasa kuma matarsa ɗaya. Ya ga hotonta ita ma ta ga nashi, yayi mata alƙawarin aure in ya dawo Nigeria. Yana dawowa kawai sai ya dai na kulata gashi ba ta da number sa na Nigeria. Ta kasa jurewa ta nemi wani abokinsa ya bata number shi ta kira amma tun da ya ji ita ce ya daina ɗauka. A ƙarshe dai ya dawo bai yi cikakken wata biyar ba yayi aure. Yarinyar ta shiga halin damuwa da baƙin ciki sanadiyyar wannan tana faɗa mun tana kuka. Ban da wannan ban san iya adadin mata da maza da aka musu irin wannan yaudarar a social website daban-daban ba.


Muyi Karatun ta natsu 'Yan Uwa, Mubar Cutar da Junan mu.....


Akula sosai Kafin Muhadu a Rubutu na Gaba..


@Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149993999


Barka Da Shan Ruwa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post