Wafatin Ummul-Muminina Nana Khadijah (S.A) !



 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MATAR DA ANNABI (S. A. W. W) BAI QARA SAMUN IRINTA BA HAR YABAR DUNIYA


Tarihin muslimci na haqiqa bai taba kawo tarihin wata mace cikin matan Annabawa (A. S) wacce ta kyautata zama da abokin zamanta (mijinta) kamar zaman da Ummul-muminina Khadijah (S. A) tayi tare da Manzon Allah (S. A. W. W) ba. 


Qur'ani ya kawo tarihin wasu daga cikin matan Annabawa (A. S) wadanda zamansu tare da Annabawan bai amfanar dasu da komai ba sai hasara a rayuwarsu ta duniya da lahira.


Hatta a wannan zamani na al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) Qur'ani ya zo da tarihin yadda matan Annabi (S. A. W. W) suka riqa aikata wasu dabi'u gare shi (S. A. W. W) na zargi har takai Allah (T) ya riqa qarqadinsu kan aikata irin wadannan halayya da cewa matuqar ba za su daina ba zai canza masa wasu matan da suka fi alkhairi (wanda hakan ke nuna cewa ashe dai akwai wadanda suka fi su). 


Darasi anan shine, kamar yadda Allah (T) bai kawo labarin matan Annabawa (A. S) na kirki cikin Alqur'ani ba haka ma ya zauna shiru (silent) kan Sayyidah Khadijah (S. A) cikin Qur'ani. 


Sayyidah Khadijah (S. A) ta rasu ne a irin wannan rana ta 10 ga watan Ramadana shekara ta 10 bayan aiko Ma'aiki (S. A. W. W), wato shekara ta 3 kenan kafin Hijrarsa zuwa Madinah. 


Kafin rasuwarta (S. A) ta bada gudumawa wajen taimakon addinin Allah da qarfinta, lokacinta da kuma mafi komai shine dukiyarta. Muslimci bai taba amfanuwa da dukiyar wata halitta kamarta (S. A) ba, dalilin haka tasa Annabi (S. A. W. W) ke cewa; 


" DA BA DON DUKIYAR KHADIJAH DA TAKOBIN IMAM ALI (A. S) BA DA ADDINI BAI ZAUNA DA QAFAFUNSA BA ."


Tun kafin muslimci ta kasance mace mai kyawawan dabi'u da mutuntaka cikin matan Quraishawa, har suna kiranta da suna Al-Tahira (tsarkakakkiya), sannan ana karanta shugabar matan Quraishawa. 


Wannan dalili yasa manyan Quraishawa irin su Utba Bn Abiy Mu'it , Abu Sufyan, Abu Jahal da dai sauransu suka nuna kudi don su aureta amma taqi amsa musu. 


Auren tsarkakekkiya sai tsarkakakke, ashe ta nata bangaren tana ta nazarin yadda za tayi ta auri Manzon Allah (S. A. W. W) bisa ji da ganin kyawawan dabi'unsa wadanda suka sa ake kiransa amintacce (Al-Ameen). Saboda haka sai ta nuna sha'awarta ga aurensa (S. A. W. W), shi kuma ya amsa mata saboda sanin kyawawan dabi'unta. 


Bayan anbi dukkan wasu qa'idoji na aure akayi aure tsakaninsu sunyi zaman lafiya wanda tarihi bai taba kawo tarihin ma'aurata masu kyakkyawan zama irin nasu ba, sai dai wadanda suka biye musu sune Imam Ali (A. S) da Sayyidah Fatimah (S. A). 


Kyakkyawan zaman da suka yi yasa Manzon Allah (S. A. W. W) bai manta da ita ba har bayan ranta, domin shi mumini tasirinsa ba ya taba fita cikin zukatan muminai.


Ranar rasuwarta ta zama rana mafi girma ta baqin ciki ga Manzon Allah (S. A. W. W), saboda haka ma yake kiran shekarar rasuwarta da shekarar baqin ciki (AMUL-HUZNI).


Tun kafin rasuwarta akayi mata bushara da gidan Aljannah, kuma Annabi (S. A. W. W) ya riqa ambatonta cikin matansa da kuma kyautatawa qawayenta wanda hakan yayi sanadiyyar Ummul-muminina A'isha ta furta kishinta a fili ga Manzon Allah (S. A. W. W). Shi kuma ya nuna mata cewa ita fa Sayyidah Khadijah (S. A) ba irinsu bace, domin 'yar Aljannah ce kuma dukkan 'ya'yanta daga gareta suke. 


Ta rasu tana 'yar shekara 65 a duniya kuma ta bar 'ya'ya biyu (2), sune Sayyidah Fatimah da Zainaba (S. A).


AMINCI YA TABBATA A GAREKI RANAR DA AKA HAIFE KI DA RANAR DA KIKA YI WAFATI DA KUMA RANAR DA KIKE TASHI RAYAYYIYA! 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


      22ND APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post