Wanne dalili yasa Sahabin Manzo (S) Usman fadawa cikin gidan mutane, har suka yi nufin kashe Shi ?



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


AI 'DABI'AR UMAR CE MA SHIGA GIDAN MUTANE BA TARE DA IZNI BA


A ko da yaushe muslimci na koyar damu tarbiyya ce tare da sanin dokoki wadanda suka zama wajibi mu kiyaye su. Wannan dalili yasa Annabi (S. A. W. W) bai bar duniya ba har sai da ya sanar damu hukuncin komai har yadda ake shiga cikin gidajen mutane a muslimci.


Allah (S. W. A) na cewa; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


" يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَدۡخُلُواْ بُيُوتًا غَيۡرَ بُيُوتِكُمۡ حَتَّىٰ تَسۡتَأۡنِسُواْ وَتُسَلِّمُواْ عَلَىٰٓ أَهۡلِهَاۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ." ( ٧٢)


" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! KADA KU SHIGA GIDAJE WADANDA BA NAKU BA HAR SAI KUN NEMI IZNI KUMA KUNYI SALLAMA GA MASU SHI, HAKAN SHINE MAFI ALKHAIRI GARE KU ZAMMANINKU ZA KU TUNA ."


(SURATUL-NUR:27)


To, amma sai muka ji malamai na kawowa cikin Bukhari wai wata rana Umar Bn Khaddab ya ji mata suna kida a cikin wani gida, sai ya zaga ta bayan gidan ya kama Katanga ya tsallaka cikin gidan ba tare da izni ko sanin mai gidan ba. Kuma sun kawo hakan ne wai don nuna tsananinsa na tsare dokokin Allah. 


NI kuma nake cewa, 


" UHMM 🤔🤔🤔, TSARE DOKAR ALLAH TA HANYAR KETA DOKAR ALLAH ?"


Sai kuma ga shi mun qara cin karo da wani hadisi wanda ya kawo cewa Usman Bn Affan ma ya taba shiga gidan mutane har suka yi nufin kashe shi. Ga riwayar kamar haka; 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 حدثنا حماد بن زيد عن يحيى بن سعيد عن أبي أمامة بن سهل بن حنيف أن عثمان بن عفان أشرف يوم الدار فقال أنشدكم الله أتعلمون أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال لا يحل دم امرئ مسلم إلا بإحدى ثلاث زنا بعد إحصان أو ارتداد بعد إسلام أو قتل نفسا بغير حق فقتل به فوالله ما زنيت في جاهلية ولا في إسلام ولا ارتددت منذ بايعت رسول الله صلى الله عليه وسلم ولا قتلت النفس التي حرم الله فبم تقتلونني قال أبو عيسى وفي الباب عن بن مسعود وعائشة وابن عباس وهذا حديث حسن ورواه حماد بن سلمة عن يحيى بن سعيد فرفعه وروى يحيى بن سعيد القطان وغير واحد عن يحيى بن سعيد هذا الحديث فأوقفوه ولم يرفعوه وقد روي هذا الحديث من غير وجه عن عثمان عن النبي صلى الله عليه وسلم مرفوعا


Hammad Bn Zaid ya bamu labari daga Yahya Bn Sa'eed, daga baban Umamata Bn Sahal Bn Haneef cewa; 


" Wata rana Usmana Bn Affan ya bayyana cikin wani gida (har mutanen gidan suka yi nufin kashe shi), sai yace; 


" Ina hada ku da Allah (T) ! Ashe baku san cewa Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" JININ MUTUM MUSULMI BA YA HALATTA HAR SAI DA 'DAYAN ABUBUWA UKU BA ? AIKATA ZINA BAYAN MUTUM YA ZAMA MUHSINI, KO KUMA YIN RIDDAH BAYAN MUSLIMCI, KO KUMA YA KASHE RAI BA TARE DA HAQQI BA SAI A KASHE SHI ."


" To, wallahi ni ban taba yin zina a jahiliyya ba haka ma a muslimci, kuma banyi Riddah ba tun daga lokacin dana yiwa Manzon Allah mubaya'a, sannan kuma ban kashe rai wacce Allah ya haramta kashe ta ba. To, bisa wacce hujja ce ku kashe ni ?"


Abu Isah (Tirmidhi) yace, a cikin babin daga Ibn Mas'ud da A'isha da Ibn Abbas cewa wannan hadisin mai kyau ne. 


Kuma Hammad Bin Salamata ya riwaito shi daga Yahya Bn Sa'eed, sai ya daukaka shi........ 


(JAMI'US-SAHIH LI TIRMIDHI, KITABUL-FITANI, BABUN MAA JAA'A LAA YAQTALUN-NAFSAN.....)


To, yanzu dan Allah masu irin wadannan dabi'u ne ake cewa wai Annabi (S. A. W. W) yace mu bi sunnarsa da tasu? 


Ni kuma ina ga kamar Annabi (S. A. W. W) ba zai taba yin umarni da abin abinda basu karya dokar Allah ke yi ba. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


30th April, 2021/ 18th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post