Muna zargin miyagun malamai a hana saka tafsiri din Malam Zakzaky a tashar — Yan uwa na Garin Yola


Daga Wakilinmu

Mabiya Harkar Musulunci da aka fi sani da 'Yan shi'a na garin Yola a jihar Adamawa sun fitar da takardar sanarwa inda suka yi zargin cewa an dakatar da sanya Tafsirin Alkur'ani mai girma na Malaminsu, Shaikh Ibraheem Zakzaky a gidan Rediyon Gotel dake garin Yola. 


Takardar wacce suka aikowa da Jaridar MADOGARA ta labarta cewa; "cikin alhini muke sanar da al'umma cewa sakamakon kai komon wasu miyagun mutane zuwa ofishin DSS, ya tilastawa hukumomin gidan rediyon GOTEL dakatar da sanya wannan tafsiri mai albarka, wanda aka kwashe shekaru goma sha takwas ana sanyawa", suka tabbatar.  


Sanarwar ta kara da cewa; "muna sanarwa al'umma cewa ana ci gaba da sanya tafsirin a kafar sada zumunta ta Facebook, YouTube da kuma WhatsApp (Video da Audio) a shafukan mu na Lajnar Tabligh Yola (Facebook), Tabligh TV Yola (YouTube) da kuma 08034848143 (WhatsApp)", suka lurantar.  


Shi dai Shaikh Ibraheem Zakzaky har yanzu gwamnatin Nijeriya na ci gaba da tsare shi har kusan shekaru shida tun bayan kashe mabiyansa sama da 300 da hukumomin Nijeriyar suka yi a watan Disambar 2015. 


A cikin watan Disambar 2016, wata babban kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umurnin a sake shi tare da biyansa diyyar take hakkinsa da aka yi da matarsa naira miliyan 50 da kuma gina masa gida a arewacin Nijeriya, sai dai har ya zuwa yau hukumomin kasar ba su bi umurnin ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post