Wafatinki bai hana Manzon Allah ambatonki ba Yaa Sayyidah Khadijah (S.A)

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MALA'IKA JIBRIL (A. S) AKA AIKO DON RARRASHIN SAYYIDAH FATIMAH (S. A)


Dukkan masoyi na kirki ba zai taba gushewa cikin zuciyar wanda suka yi zaman alziqi da mutunta juna ba, ballantana kuma zama na bautar Allah Mahaliccinsu.


Har na tuno da wani mutum wanda suka yi zama da matarsa cikin jahiliyya da aikata aikin jahilci da kafirci, amma rasuwarta yasa wannan mijin nata fito da wani iliminsa wanda ba a san shi dashi ba, domin a wannan lokacin aka san ashe ya iya qirge (counting). 


An ji shi yayin data mutu yana cewa; 


" 1, 2 , 3, 4, 5, 6, 7, 8, 9, 10 !"


Sai yace; 


" YAU GOMA TA CIKA ! "


Wannan lissafi ne wanda aka san ya iya shi sanadin mutuwar matarsa wacce suka yi zama na jahilci da danne haqqoqin juna, to, ina kuma wadanda suka yi zaman na bauta da tsarkake Allah ?


Ga wasu riwayoyi guda biyu da za mu kawo wadanda ke tabbatar mana da cewa Annabi (S. A. W. W) bai sami mace kamar Sayyidah Khadijah (S. A) ba, kuma tunawa da ambatonta bai gushe daga kan harshensa mai albarka ba har ya kuma ya hadu da ita (S. A). 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 الخصال ابْنُ الْوَلِيدِ عَنِ الصَّفَّارِ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ أَبِي عَلِيٍّ الْوَاسِطِيِّ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عِصْمَةَ عَنْ يَحْيَى بْنِ عَبْدِ اللَّهِ عَنْ عَمْرِو بْنِ أَبِي الْمِقْدَامِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: دَخَلَ رَسُولُ اللَّهِ ص مَنْزِلَهُ فَإِذَا عَائِشَةُ مُقْبِلَةٌ عَلَى فَاطِمَةَ- تُصَايِحُهَا وَ هِيَ تَقُولُ وَ اللَّهِ يَا بِنْتَ خَدِيجَةَ مَا تَرَيْنَ إِلَّا أَنَّ لِأُمِّكِ عَلَيْنَا فَضْلًا وَ أَيُّ فَضْلٍ كَانَ لَهَا عَلَيْنَا مَا هِيَ إِلَّا كَبَعْضِنَا فَسَمِعَ مَقَالَتَهَا لِفَاطِمَةَ فَلَمَّا رَأَتْ فَاطِمَةُ رَسُولَ اللَّهِ ص بَكَتْ فَقَالَ مَا يُبْكِيكِ يَا بِنْتَ مُحَمَّدٍ قَالَتْ ذَكَرَتْ أُمِّي فَتَنَقَّصَتْهَا فَبَكَيْتُ فَغَضِبَ رَسُولُ اللَّهِ ص ثُمَّ قَالَ مَهْ يَا حُمَيْرَاءُ فَإِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى بَارَكَ فِي الْوَدُودِ الْوَلُودِ وَ إِنَّ خَدِيجَةَ رَحِمَهَا اللَّهُ وَلَدَتْ مِنِّي طَاهِراً وَ هُوَ عَبْدُ اللَّهِ وَ هُوَ الْمُطَهَّرُ وَ وَلَدَتْ مِنِّي الْقَاسِمَ وَ فَاطِمَةَ وَ رُقَيَّةَ وَ أُمَّ كُلْثُومٍ وَ زَيْنَبَ وَ أَنْتِ مِمَّنْ أَعْقَمَ اللَّهُ رحمه [رَحِمَهَا] فَلَمْ تَلِدِي شَيْئاً.


المصدر 2: 37 و 38.


Ya zo cikin AL-KISAL na Ibn Walid, daga Saffaaru, daga Barqeey, daga baban Aliyu Al-Wasidiy, daga Abdullahi Bn Ismata, daga Yahya Bn Abdullahi, daga Amruu Bn Abiy Miqdaam, daga babansa daga Abu Abdullahi (A. S) yace; 


" Manzon Allah (S. A. W. W) ya shiga gidansa sai ga A'ishatu ta fuskanci Fadimatu (S. A) tana yi mata rashin mutunci tana tana ce mata;  


" Wallahi yaa ke 'yar Khadijah ! Babu abinda muke gani face akwai wani fifikon mahaifiyar (wajen Annabi) a kanmu, kuma ma wanne fifiko ne take dashi a kanmu alhali ita ma kamarmu take !"


Sai (Annabi) ya ji maganar da take fadawa Fatimah. To, yayin da Fadimatu taga Manzon Allah (S. A. W. W) sai ta fashe da kuka (she burst into tears) . Sai (Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" KUKAN ME KIKE YI YAA 'YAR MUHAMMAD ?" Tace; 


" Ta ambaci mahaifiyata ce kuma tana ta qasqantar da ita, shine nake kuka. "


Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya fusata, sa'an nan yace; 


" KUL KIKA QARA IRIN WANNAN YAA KE HUMAIRA ! DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YAYI ALBARKA CIKIN MATA NE MASU HAIHUWA ! KUMA LALLE KHADIJAH ALLAH YAYI MATA RAHMA TA HAIFA MIN MAI TSARKI SHINE ABDULLAHI (mai sunan mahaifina) KUMA SHINE MAI TSARKAKEWA, KUMA TA HAIFA MIN QASIM DA FADIMATU DA RUQAYYATU DA UMMU-KULTHUM DA ZAINAB . KE KUWA KINA DAGA CIKIN WADANDA ALLAH YA YANKE RAHMARSA (marar haihuwa), BA KI HAIFI KOMAI BA !"



الأمالي للشيخ الطوسي الْمُفِيدُ عَنِ ابْنِ قُولَوَيْهِ عَنْ أَبِيهِ عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ عِيسَى عَنِ الْعَبَّاسِ بْنِ عَامِرٍ عَنْ أَبَانٍ عَنْ بُرَيْدٍ عَنِ الصَّادِقِ ع قَالَ: لَمَّا تُوُفِّيَتْ خَدِيجَةُ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا جَعَلَتْ فَاطِمَةُ ع تَلُوذُ بِرَسُولِ اللَّهِ ص وَ تَدُورُ حَوْلَهُ وَ تَقُولُ أَبَتِ‏ أَيْنَ أُمِّي قَالَ فَنَزَلَ جَبْرَئِيلُ ع فَقَالَ لَهُ رَبُّكَ يَأْمُرُكَ أَنْ تُقْرِئَ فَاطِمَةَ السَّلَامَ وَ تَقُولَ لَهَا إِنَّ أُمَّكِ فِي بَيْتٍ مِنْ قَصَبٍ‏ كِعَابُهُ مِنْ ذَهَبٍ وَ عُمُدُهُ يَاقُوتٌ أَالمجالسحْمَرُ بَيْنَ آسِيَةَ وَ مَرْيَمَ بِنْتِ عِمْرَانَ فَقَالَتْ فَاطِمَةُ ع إِنَّ اللَّهَ هُوَ السَّلَامُ وَ مِنْهُ السَّلَامُ وَ إِلَيْهِ السَّلَامُ‏.


المجالس: 110.



Sannan ya zo cikin AL-AMALI na Sheikh 'Dusi Al-Mufidu, daga Ibn Quulawaihi, daga babansa daga Sa'ad, daga Ibn Isah, daga Al-Abbas Bn Amir, daga Abaan, daga Buraidin, daga Sadiq (A. S) yace; 


" Yayin da Khadijah (R. A) ta rasu sai Fadimatu (S. A) ta rabi (came close) Manzon Allah (S. A. W. W) tana ta kewayawa a gefensa tana cewa;  


" Babana ina mahaifiyata ?" Yace; 


Sai Jibrilu (A. S) ya sauko yace masa; 


" UBANGIJINKA YANA UMARTARKA DA KA ISAR DA GAISUWA ZUWA GA FADIMATU, KUMA KACE MATA, " LALLE MAHAIFIYARKI TANA CIKIN WANI GIDA NA BENI (upstairs), RUFINSA NA ZINARI NE KUMA AMUDANSA (pillars) NA JAJAYEN YAQUTU NE TSAKANIN ASIYA DA MARYAM 'YAR IMRANA. "


Sai Fadimatu (A. S) tace; 


" Lalle Allah shine aminci, kuma daga gare shi aminci yake, shi ma (Jibrilu) aminci ya tabbata a gare shi !"


(AL-MAJAALIS:110)


Wannan fa ita ce Khadijah (S. A). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


       (08137925034)


     24TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post