Nassosi daga ayoyin Al'qur'ani: Ɗabi'un Manzon Allah (S.A.W.W) (1)

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


NASSOSI DAGA AYOYIN ALQUR'ANI 


Manzon Allah (S. A. W. W) ya kasance mafi kyawun halaye da dabi'u ababan koyi ga dukkan muminai. Duk wata dabi'a ta kamala an samo ta ne daga wajen fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W). Saboda haka sai dai kowa yayi koyi dashi ba shi yayi koyi da wani ba. 


Kadan daga cikin irin wadannan kyawawan halaye sune :-


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇




MAI TAUSHIN ZUCIYA DA SAUQIN KAI NE 


" فَبِما رَحْمَةٍ مِنَ اللَّهِ لِنْتَ لَهُمْ وَ لَوْ كُنْتَ فَظًّا غَلِيظَ الْقَلْبِ لَانْفَضُّوا مِنْ حَوْلِكَ فَاعْفُ عَنْهُمْ وَ اسْتَغْفِرْ لَهُمْ وَ شاوِرْهُمْ فِي الْأَمْرِ فَإِذا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُتَوَكِّلِينَ‏."


(الآيات آل عمران‏)


" SABODA RAHMA DAGA ALLAH KAYI SAUQIN KAI GARE SU, DA ACE KA KASANCE MAI SAURIN FUSHI MAI KAUSHIN ZUCIYA DA SUN WATSE DAGA GEFANKA. (Saboda haka) KA YAFE MUSU (daga rashin mutuncin da suke yi maka) KUMA KA GAFARTA MUSU (kan cutarwar da suke yi maka), KUMA KAYI SHAWARI DASU CIKIN AL'AMARI (don jawo su a jika). AMMA YAYIN DA KAYI AZAMAR (yanke hukunci) KA DOGARA GA ALLAH (don za su riqa zarginka da zundenka), LALLE ALLAH NA SON MASU DOGARO (gare Shi). "



BA YA QARYA DON NEMAN SAMUN MABIYA 


 " لا أَقُولُ لَكُمْ عِنْدِي خَزائِنُ اللَّهِ وَ لا أَعْلَمُ الْغَيْبَ وَ لا أَقُولُ لَكُمْ إِنِّي مَلَكٌ إِنْ أَتَّبِعُ إِلَّا ما يُوحى‏ إِلَيَ‏..."


 (الأنعام‏ قُلْ)


"NI DAI BA NA CE MUKU TARE DANI AKWAI TASKAR ALLAH (na arziqin da zan riqa raba muku), KUMA BAN SAN GHAIBU BA (face abinda Allah ke sanar dani wanda ku baku sani ba), KUMA NI BA ZAN CE MUKU NI MALA'IKA (ne cikinku ba) ,BA KOMAI NAKE BI BA FACE ABINDA AKA YI MIN WAHAYINSA. "


(Saboda haka in za ku bi ni kan haka shike nan) 


MAI YAFIYA DA KAU DA KAI NE 

 


" خُذِ الْعَفْوَ وَ أْمُرْ بِالْعُرْفِ وَ أَعْرِضْ عَنِ الْجاهِلِينَ‏."


(الأعراف‏)


" KA RIQI YIN YAFIYA (ga wadanda suka munana maka don hassada da qiyayya) KUMA KAYI UMARNI DA KYAKKYAWA, KUMA KA KAWAR DA KAI DAGA JAHILAI (masu cewa kai Boka ne mawaqi) 

 

ALLAH NE MAI MAYAR DA RADDI GA MASU AIBANTA SHI 


" وَ مِنْهُمُ الَّذِينَ يُؤْذُونَ النَّبِيَّ وَ يَقُولُونَ هُوَ أُذُنٌ قُلْ أُذُنُ خَيْرٍ لَكُمْ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَ يُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِينَ وَ رَحْمَةٌ لِلَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ‏."


(التوبة)



" KUMA DAGA CIKINSU AKWAI MASU CUTAR DA ANNABI SUNA CEWA WAI SHI KUNNE NE. TO, KACE MUSU; " WANNAN KUNNEN YA FI KU ALKHAIRI (domin) YANA YIN IMANI DA ALLAH KUMA YANA YIN IMANI DOMIN MUMINAI, KUMA RAHMA CE GA WADANDA SUKA YI IMANI DAGA CIKINKU. "


(Shi ya kasance rahma ga masu imani) 

 

WANDA ALLAH KE RARRASHINSA 



" وَ اصْبِرْ وَ ما صَبْرُكَ إِلَّا بِاللَّهِ وَ لا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَ لا تَكُ فِي ضَيْقٍ مِمَّا يَمْكُرُونَ‏."


( النحل‏)


" KUMA KAYI HAQURI, KUMA HAQURIN NAKA BAI KASANCE BA FACE DOMIN ALLAH (kake yinsa), SANNAN KUMA KADA KAYI BAQI CIKI A KANSU (don kaga sun qi shiryuwa), KUMA KADA KA KASANCE CIKIN QUNCI NA DAGA ABINDA (suke qulla maka) NA MAKIRCI .


(wannan kuwa na nuna mana ne cewa komai nasa don Allah yake yi) 



MAI TSANANIN DAMUWA NE DA HALIN AL'UMMARSA 



" فَلَعَلَّكَ باخِعٌ نَفْسَكَ عَلى‏ آثارِهِمْ إِنْ لَمْ يُؤْمِنُوا بِهذَا الْحَدِيثِ أَسَفاً .


" HAR KAYI KUSA KA HALAKAR DA KANKA (don damuwa) AKAN GURABANSU (kawai don) BA SUYI IMANI DA WANNAN LABARI (Qur'ani) BA SABODA BAQIN CIKI. "



و قال تعالى الكهف‏ فَلا تُمارِ فِيهِمْ إِلَّا مِراءً ظاهِراً وَ لا تَسْتَفْتِ فِيهِمْ مِنْهُمْ أَحَداً وَ لا تَقُولَنَّ لِشَيْ‏ءٍ إِنِّي فاعِلٌ ذلِكَ غَداً إِلَّا أَنْ يَشاءَ اللَّهُ وَ اذْكُرْ رَبَّكَ إِذا نَسِيتَ وَ قُلْ عَسى‏ أَنْ يَهْدِيَنِ رَبِّي لِأَقْرَبَ مِنْ هذا رَشَداً."


( الكهف‏)



" KUMA KADA KAYI JAYAYYA CIKINSU SAI DAI DA BAYYANANNEN AL'AMARI, KUMA KADA KAYI FATAWA GA KOWA DAGA CIKINSU. 


KUMA LALLE KADA KACE GA WANI ABU, " LALLE NI MAI AIKATAWA NE A GOBE .


SAI DAI (kace) IN ALLAH YA SO. SANNAN KUMA KA AMBACI UBANGIJINKA (cikin kowanne irin aiki naka) KO DA KA MANTA. KUMA KACE, " AKWAI TSAMMANIN UBANGIJINA YA SHIRYAR DANI DAGA ABINDA YAFI KUSA GA WANNAN NA SHIRIYA. "


(An koyar damu cewa duk abinda za muyi mu ambaci sunan Allah ko da kuwa a tsakiyarsa ne ko qarshensa matuqar mun manta da farko) 



DUK WAHALAR DA YASHA DON AL'UMMARSA CE 


" طه ما أَنْزَلْنا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ لِتَشْقى‏ إِلَّا تَذْكِرَةً لِمَنْ يَخْشى‏.'


( طه‏ )


" YAA KAI MUHAMMAD! BAMU SAUKAR DA QUR'ANI A KANKA DON KA WAHALA (Ta hanyar karantar dashi) BA. 


SAI DAI KAWAI DON TUNATARWA GA WANDA KE TSORON ALLAH. 


(Duk wata wahalar da ya sha wallahi da dalilinmu ne amma ba wai don kansa ba) 



SHI MAI YAWAN HAQURI DA TSARKAKE ALLAH NE 


 و قال تعالى 


طه‏ 


فَاصْبِرْ عَلى‏ ما يَقُولُونَ وَ سَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَ قَبْلَ غُرُوبِها وَ مِنْ آناءِ اللَّيْلِ فَسَبِّحْ وَ أَطْرافَ النَّهارِ لَعَلَّكَ تَرْضى‏ وَ لا تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلى‏ ما مَتَّعْنا بِهِ أَزْواجاً مِنْهُمْ زَهْرَةَ الْحَياةِ الدُّنْيا لِنَفْتِنَهُمْ فِيهِ وَ رِزْقُ رَبِّكَ خَيْرٌ وَ أَبْقى‏ وَ أْمُرْ أَهْلَكَ بِالصَّلاةِ وَ اصْطَبِرْ عَلَيْها لا نَسْئَلُكَ رِزْقاً نَحْنُ نَرْزُقُكَ وَ الْعاقِبَةُ لِلتَّقْوى‏


" KAYI HAQURI BISA ABINDA SUKE FADA A KANKA (Na cewa kai masihirci ne mawaqi kuma boka ko mai tabin hankali) KUMA KAYI TASBIHI DON (nuna) GODIYA GA UBANGIJINKA KAFIN RANA TA HUDO DA KUMA GABANIN FADUWARTA. KUMA DAGA CIKIN DARE (ma) KAYI (ta yin) TASBIHI DA KUMA QARSHEN YINI TSAMMANINKA KA (qara) SAMUN YARDA (ta Ubangijinka). 


KUMA KADA KA KARKATAR DA IDANUWANKA (na sha'awa) ZUWA GA ABINDA MUKA JIYAR DASU DADI (na kudi, dukiya, dabbobi ko ababan hawa irin nada dana wannan zamani) DUK QYALQYALI NE NA RAYUWAR DUNIYA DON MU JARRABA SU CIKINTA. ARZIQIN UBANGIJINKA (na imani da ya ba ka) SHINE MAFI ALKHAIRI KUMA MAFI WANZUWA (har tashin alqiyama) .


 KUMA KA UMARCI IYALANKA DA YIN SALLAH SANNAN SUYI HAQURI A KANTA (domin Shaidan ya fi batar da mutane ta hanyar sanya kasala cikinta da yinta don a nunawa mutane). BA MU TAMBAYARKA WANI ARZIQI (ranar alqiyama) DOMIN MU MUKE AZURTA KA, KUMA KYAKKYAWAN QARSHE NA GA MASU TAQAWA."


(Babu ruwan Allah a ranar alqiyama da tambayarka cewa ya kai mai kudi ne kuwa) 


SHI YANA TARE DA MAI IMANI NE KO DA KUWA TALAKA NE 


" وَ أَنْذِرْ عَشِيرَتَكَ الْأَقْرَبِينَ وَ اخْفِضْ جَناحَكَ لِمَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ فَإِنْ عَصَوْكَ فَقُلْ إِنِّي بَرِي‏ءٌ مِمَّا تَعْمَلُونَ وَ تَوَكَّلْ عَلَى الْعَزِيزِ الرَّحِيمِ الَّذِي يَراكَ حِينَ تَقُومُ وَ تَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ‏ 


( الشعراء)


" KUMA KA GARGADI DANGINKA NA KUSA (cewa su dawo zuwa bautar Allah Shi kadai) . KUMA KA SASAAUTAR DA FIFFIKENKA (na tausayi kamar yadda uwa ke yiwa danta) GA DUKKAN WANDA YA BI KA DAGA CIKIN MUMINAI. KUMA IDAN SUKA SABA MAKA (kan wannan kira da kake yi), TO, KACE; " LALLE NI MAI BARRANTA NE DAGA ABINDA KUKE BAUTAWA. SANNAN KUMA KA DOGARA GA MABUWAYI MAI JIN QAI (don komai zai iya samunka kan hakan). SHINE WANDA YAKE GANINKA YAYIN DA KAKE MIQEWA (kana sallah cikin dare), DA KUMA JUJJUYAWARKA CIKIN (tsatson mahaifa) MASU SUJADAH, DOMIN SHI SHINE MAI JI KUMA MASANI. "


(Ashe shi asalin mahaifansa tsarkakakkun tsatso ne wadanda suka fito daga tsatson Annabi Ibrahim (A. S)). 

 


SHI AKAN GASKIYA YAKE A KULLUM 


" وَ لا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَ لا تَكُنْ فِي ضَيْقٍ مِمَّا يَمْكُرُونَ‏ إلى قوله تعالى‏ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ إِنَّكَ عَلَى الْحَقِّ الْمُبِينِ‏ ."


(النمل‏)


" KUMA KADA KAYI BAQIN CIKI A KANSU (don sun cutar da kai ko sun qi yarda da kai), KUMA KADA KA KASANCE CIKIN QUNCI NA DAGA (abinda suke qulla maka) NA MAKIRCI ."



SHI MAI SALLAMA AL'AMARINSA GA ALLAH NE 


و قال تعالى  


" إِنَّما أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ رَبَّ هذِهِ الْبَلْدَةِ الَّذِي حَرَّمَها وَ لَهُ كُلُّ شَيْ‏ءٍ وَ أُمِرْتُ أَنْ أَكُونَ مِنَ الْمُسْلِمِينَ."


(النمل‏)


" (Kace) ABIN SANI NI DAI AN UMARCE NI NE DANA BAUTAWA UBANGIJIN WANNAN GARI (Allah) WANDA AKA HARAMTA SHI (Makkah) , KUMA KOMAI GARE SHI YAKE. SANNAN KUMA AN UMARCE NI DANA KASANCE CIKIN MUSULMAI (masu sallama al'amarinsu gaba daya ga Allah). "


ZA MU CIGABA INSHA ALLAH. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


      24TH APRIL, 2021

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post