TASIRIN HOTO DA KIMIYYAR 'DAUKARSA BISA QA'IDA



MU'UTAMAR NA CIBIYAR WALLAFA DA YADA AYYUKAN SAYYID ZAKZAKY (H) KARO NA 2 A GARIN BAUCHI  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

A rana ta 2 kuma rana ta qarshe ne 4-4-2021 aka saurari jawabi daga bakin shahararre kuma masanin malamin nan Malam Ibrahim Aqeel Zaria .


Malamin yayi jawabi ne kan wannan Maudhu'i da muka ambata a sama, kuma haqiqa ya bawa topic din haqqinsa yadda ya dace, domin shi masani ne ta wannan fanni. 


Cikin jawabin nasa ya kawo misalai da dama wanda turawa suka riqa amfani da hotuna /Vedios don isar da saqonsu zuwa ga wadanda suke son isarwa. Har ya kawo misali da shahararren gurin shirya Finafinai na qasar Amurka mai suna (HOLY WOOD) yadda ya fassara shi da cewa Sanda mai tsarki. 


Yace, daga cikin irin target nasu sun qirqiro wani firm mai suna Umar Mukhtar wanda hadafinsu shine su jefa tsoro cikin zukatan musulmi ta yadda za suga fada (fighting) da Bature ba qaramin aiki bane kuma babu nasara cikinsa, domin ai qarshen cassette din abinda yake karantarwa kenan.


Ya qara da cewa, amma ai sun kasa fitar da cassette na Sheikh Usman Bn Fodiyo , domin idan suka fitar babban darasin da za su karantar shine idan musulmai suka zabura za su kawar da tsarin Bature, domin Sheikh Usman 'Dan Fodiyo ne yayi nasara a yaqin. 


Yace, daga cikin irin wannan hadafi nasu suka yi (Horror firm) don su firgita mutane da nufin cimma wata manufa tasu. 


Malamin yayi bayani sosai yadda hoto mai motsi da marar motsi ke yin tasiri, har ya kawo maganar Imam Sadiq (A. S) inda yake cewa; 


" KU KIRA MUTANE TA HANYAR AIKI...  "


 Malamin yace shi aiki kuwa ganinsa ake yi, shi yasa yafi tasiri fiye da komai .


Dangane da kimiyyar hoto kuwa yace ya kamata mai daukar hoto ya sami (camera 📷 auto) ko kuma ya zamana ya qware kafin ya dau hoto, sannan kuma ya kula wajen daukar sosai wajen daukar nasa a angle, domin yawancin hoton da aka dauke shi a angle yakan fito tamkar zagi (challenge) ne ga wanda aka dauka. Sannan kuma yace (background) na da matuqar muhimmanci. 


A qarshen jawabin nasa yace, idan mutum na son daukar hoton jama'a masu yawa, to, kamata yayi ace ya sami guri mai  tudu (high place) yadda zai iya bashi damar daukar jama'a masu yawa. Kuma yace tarar gaban Muzahara ana daukar hoto bai cika bada natija ba, domin jama'a ce masu yawa amma sai su fito 'yan kadan a idon duniya. 


Mai jawabin rufe taro kuwa shine Sheikh Adamu Ahmad Tsaho Jos, wanda yayi ta'aliqi kan dukkan Maudhu'ai da aka gabatar a halin tsahon wannan taro. 


Shehin malamin ya kawo cewa farkon wanda ya fara rubutu shine Annabi Idris (A. S), kuma shine ya soma dinki (tailoring). Yace, saboda muhimmancin karatu da rubutu abinda aka fara saukarwa Annabi Muhammad (A. A. W. W) shine,  " KAYI KARATU  ."


Malamin ya qara da cewa, da ace na farko ba suyi rubutu sun taskace shi ba, to,  da mu na yanzu bamu sami komai na magabata ba. Kuma yace, haqqi ne a kanmu na al'umma da muke cikinta dama wadanda za suzo daga bayanmu mu sanar damu haqiqanin gaskiya, kuma hakan ba zai yiwu ba har sai muna taskake ayyukanmu. 


Shehin malamin yayi gargadi sosai ga dukkan wanda zaiyi rubutu ya kasance yasan abinda zai rubuta kuma ya nazarci abinda zai biyo baya, domin wakiltar Harka muke yi kuma da ayyukanmu za a fassara Harkar. Har ya kawo hadisi na Imam Ja'afar As-Sadiq (A. S) inda yake cewa; 


" KU KASANCE ADO GARE MU, KUMA KADA KU KASANCE QAZANTA GARE MU  ." Ya kuma qara da cewa ya ce; 


" KU KASANCE MASU KIRA DA HARSUNANKU (masu kyau da dadi da kuma fasaha cikin abinda zai fito daga bakunanmu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)



5th April, 2021/ 23rd Sha'aban, 1442.




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post