-An Ruwaito Hadisi a Cikin Kifayatud-Dalib na al-Kinji ash-Shafi'i 123. Daga Umar Dan Khaddabi Shi kuma Ya daukaka Shi zuwa ga Manzon Allah (S) Yace: "Da ace dukkan tekuna Tawadune, Kuma Dukkan Itace Alkaluma ne, Duk Mutane Marubuta ne, Sannan duk Aljanu masu Kirga ne. Ba zasu iya tattara su rubuta falalolin Ali (as) ba!"


-Allahu Akbar! Manzon Allah (S) Yayi Gaskiya. Hakika falala da Darajojin Imam Ali I(as) Sunyi Yawan da Sai dai Mu daure gigin kwakwalenmu da ambata Mata Maganar Manzon Allah (S) cewa; "Ya Kai Ali! Ba wanda ya San Allah Sai ni da kai! Ba Wanda ya Sanni Sai Allah sai kai! Ba kuma Wanda Ya Sanka Sai Allah sai Ni."


-Yaya Kuwa zaka Sauwala Wannan bawan Allah Karimi, Wanda Mun  San da Hadisin Annabi (S) da Yake Cewa Matsayinka a Waje na Kamar Matsayina a Wajen Ubangiji na ne.


-Amincin Allah Ya tabbata a gareka Ya kai Wanda darajarka da Falalarka Suka gagara rubutuwa da ruwan tekuna da alkaluman dukkan itatuwa, da kuma Hannayen dukkan Mutane da lissafin dukkan AlJannu!


-Za'a Iya samun Wannan ruwayar a: Littafin Yunabi'ul-Muwadda na Qunduzi al-Hanafi 239. Da Al-Manaqib na al Maufiq bin Ahmad al-Hanafi 18. Ko kuma littafin Kifayatud-Dalib na al-Kinji ash-Shafi'i 123.


-Muhammad Jiddah Nguru.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post