Shin yana halatta a hada salloli biyu a halin zaman gida, ba tare da wani uzuri ba??


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


AMSA DAGA AIKIN ANNABI (S. A. W. W) 


Abinda kowa ne ya sani cewa ita sallah wacce aka wajabta mana yinta a kullum guda biyar (5) ce kamar yadda yazo cikin hadisan Manzon Allah (S. A. W. W). Sune :-


(1)- AZAHAR


(2)- LA'ASAR


(3)- MAGRIB 


(4)- ISHA'I da kuma 


(5)- ASUBAHI 


Sai dai kuma dukkansu lokuta uku suke dashi bisa nassin Qur'ani. 


(i) - AZAHAR da LA'ASAR 


(ii) - MAGRIB da ISHA'I 


(iii) - ASUBA.


Lokutan yinsu kuma yazo ne cikin Alqur'ani mai girma wanda qarya ba ta zuwa ta gaba ko ta baya gare shi. Ga nassin nan biye kamar haka; 


" أَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمۡسِ إِلَىٰ غَسَقِ ٱلَّيۡلِ وَقُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِۖ إِنَّ قُرۡءَانَ ٱلۡفَجۡرِ كَانَ مَشۡهُودٗا." ( ٨٧)


" KU TSAIDA SALLAH YAYIN DA RANA TA KARKATA (azahar da la'asar) ZUWA DUHUN DARE (magrib da Isha'i) DA KUMA LOKACIN KARATUN ALFIJR (asuba), LALLE KARATUN ALFIJR (sallar asuba) TA KASANCE WACCE AKE HALARTA ."(SURATUL-ISRA'I, AYA TA 78)


Duk Tafsirin da ka duba ko malamin daka tambaya idan dai wannan ayar za a fassara maka, to, lokuta uku zai kawo maka kamar yadda yazo cikin Qur'ani, sai dai kawai ace maka sallolin biyar ne. 


Na'am, an sami hadisin da aka ce Annabi (S. A. W. W) yayi wadannan salloli biyar cikin lokuta daban-dabam, sai dai kuma babu inda aka ce hada su haramun ne. Sai kuma na karanta wani hadisi wanda aka ce wai Annabi (S. A. W. W) yace duk wanda ya hada salloli biyu ba bisa wani uzuri ba, to, ya jewa wata qofa daga cikin qofofin al-kaba'ir.


Sai dai kuma in aka ce wannan magana ta hana hada salloli biyu ba bisa uzuri ba ya zama laifi, to, sai muce ana samun tufka-da-warwara kenan, domin wannan magana ta saba aikinsa (S. A. W. W). 


Wasu malaman sunyi qoqarin sai sun nuna cewa ba a hada salloli biyu lokaci guda wai in ba bisa lalura ba. Lalurar kuma ita ce :-


- Tafiya 


- Halin tsoro (cikin halin yaqi) 


- Ruwan sama. 


Duk da irin wannan kame-kamen nasu sai kuma ga shi sun kawo cikin daya daga cikin ingantattun littafansu shida cewa Annabi (A. A. W. W) ya hada salloli cikin halin zaman gida ba a halin tafiya ko tsoro ba. ما جاء في الجمع بين الصلاتين في الحضرحدثنا هناد حدثنا أبو معاوية عن الأعمش عن حبيب بن أبي ثابت عن سعيد بن جبير عن بن عباس قال جمع رسول الله صلى الله عليه وسلم بين الظهر والعصر وبين المغرب والعشاء بالمدينة من غير خوف ولا مطر قال فقيل لابن عباس ما أراد بذلك قال أراد أن لا يحرج أمته وفي الباب عن أبي هريرة قال أبو عيسى حديث بن عباس قد روي عنه من غير وجه رواه جابر بن زيد وسعيد بن جبير وعبد الله بن شفيق العقيلي وقد روي عن بن عباس عن النبي صلى الله عليه وسلم غير هذا


Hunaad ya bamu labari, baban Mu'awiyata ya bamu labari daga A'amashu, daga Habeeb Bn Abiy Thaabit, daga Sa'eed Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R. A) yace; 


" Manzon Allah (S. A. W. W) ya hada tsakanin azabar da la'asar, da tsakanin magrib da Isha'i a Madinah ba tare da tsoro ba kuma ba tare da ruwa ba ." 


Mai riwayar yace, sai aka cewa Ibn Abbas (R. A); " Me yake nufi da hakan? " Sai Ibn Abbas (R. A) yace; 


" YAYI NUFIN KADA YA QUNTATAWA AL'UMMARSA CE. "(JAMI'US-SAHIH LI-TIRMIDHI, KITABUS-SALAT, BABUN MAA JAA'A FEE JAM'I BAINA SALATAINIY FEE HADHRI)


Kunga anan batun cewa wai ruwa ne ke sa a hada sallah biyu a halin zaman gida ya tashi daga aiki. Idan kuwa hakane wanne wacce hujja ce tasa ake zargin masu hada salloli a halin zaman gida ?


Sannan kuma Imam Malik ya kawo irin wannan riwaya cikin MUWADDA cewa; 


Malik ya bamu labari daga baban Zubair Al-Makkiy, daga Sa'eed Bn Jubair, daga Abdullahi Bn Abbas yace; 


" MANZON ALLAH (S. A. W. W) YAYI SALLAR AZAHAR DA LA'ASAR A HADE, KUMA MAGRIBA DA ISHA'I A HADE, BA KUMA A HALIN TSORO KO TAFIYA BA. "


(KITABIN TAQAITA SALLAH A HALIN TAFIYA, BABIN HADA TSAKANIN SALLOLI A HALIN ZAMAN GIDA DA TAFIYA, HADISI MAI LAMBA :229)


Sai Imam Malik yace, wataqila ana ruwa ne. Kaga anan shi ma tsammani yake yi cewa ko ruwa ake yi amma babu wanda ya fada masa hakan. Kawai dai ance Annabi (S. A. W. W) ya hada sallolin amma ba a lokacin tsoro bane kuma ba ta halin tafiya bane. 


Amma da aka tambayi Ibn Abbas game da wannan hada sallar da Annabi (S. A. W. W). Sai yace ;


" A'A, ANNABI YAYI HAKAN NE KAWAI DON KADA YA QUNTATAWA AL'UMMARSA . "


Wato abin nufi shine kada mutum yaji cewa yana son hadawa amma wani yace masa babu damar yin hakan.


Wannan shine abinda yazo cikin Qur'ani kamar yadda muka kawo muka ayar, da kuma wannan hadisai da muka kawo muku na cikin TIRMIDHI da kuma MUWADDA MALIK. 


ALLAH YASA MU DACE.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


        (08137925034)


1st May, 2021/ 19th Ramadan, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post